Hisbah Board KT L.G DIV

  • Home
  • Hisbah Board KT L.G DIV

Hisbah Board KT L.G DIV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hisbah Board KT L.G DIV, .

KTSHB 2025KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA HALARCI SALLAR IDIN BA...
06/06/2025

KTSHB 2025
KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.

SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA HALARCI SALLAR IDIN BABBAR SALLAH SHEKARA TA 1446.

A yau juma'a 6 ga watan juni shekara ta 2025 shugaban hukumar hisbah na karamar hukumar katsina malam shamsu kabir ya halarci sallah idin babbar sallah tare da jami'an hukumar hisbah na karamar hukumar katsina a masallacin Goruba Road Katsina.

A inda Malam Sulaiman Rahama ya gabatar da sallah da kuma hudubah.

Daga karshe muna rokon Allah ya karbi ibadunmu Ameen!.

Reported by:
Abdulrahman Kofa Bello
ICT UNIT KT. LG. HISBAH BOARD

KTSHBKATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA ZIYARCI OFFICE DIN MAI GIRM...
20/05/2025

KTSHB
KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.

SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA ZIYARCI OFFICE DIN MAI GIRMA CHIYAMAN NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA.

A yau Talata 20 ga watan Mayu shekara ta 2025 shugaban hukumar Hisbah na karamar hukumar katsina malam shamsu kabir ya ziyarci ofishin mai girma chiyaman na karamar hukumar katsina Hon. Isah Miqdad AD Saude.

A inda shugaban hukumar Hisbah na karamar hukumar katsina ya mika kudurorin sa tare da jaddada goyon bayan sa ga mai girma chiyaman, san nan daga bisani ya mika takardar dokokin da hukumar Hisbah ta saka a karkashin jagoranci Sheik Dr.Aminu Usman Abu Ammar a fadin jihar Katsina da kuma kananan hukumomin tah.

Daga karshe Mai girma chiyaman na karamar hukumar katsina Hon. Isah Miqdad AD Saude ya ya ba sosai tare da daukar alwashin zaiyi aiki tare da hukumar Hisbah ta karamar hukumar katsina kafada da kafada.

Reported by
Sardauna ICT Unit Hisbah Board KTLG.

KTSHB KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION Lahadi 27/04/2025Dami dumin su: Yanzu Hukumar Hisbah ta karamar hukumar katsina ...
27/04/2025

KTSHB
KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION
Lahadi 27/04/2025
Dami dumin su: Yanzu Hukumar Hisbah ta karamar hukumar katsina a karkashin jagorancin malam shamsu kabir ta kai samame a kasuwar yar kutungu a inda ta iske maza da mata suna ta sharholiya da zina ce zina ce.

A inda aka samu nasarar k**a yan mata guda biyu 2.

Reported by
B.KOFA ICT Unit Hisbah Board KTLG.

KTSHBKATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR KATSINA TA KARBI BAKONCIN KUNGIYAR LAJNATUL HIS...
24/04/2025

KTSHB
KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.

HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR KATSINA TA KARBI BAKONCIN KUNGIYAR LAJNATUL HISBAH ASSOCIATION OF NIGERIA (LAJHAN) TA KARAMAR HUKUMAR KATSINA SANNAN DAGA BISANI HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR KATSINA TA GABATAR DA TA'AZIYYA GIDAN SU DAYA DAGA CIKIN JAMI'AN TA.

A yammacin yau Alhamis 24 ga watan Aprilu shekara ta 2025 hukumar hisbah ta karamar hukumar katsina a karkashin jagorancin malam shamsu kabir sun karbi bakoncin kungiyar Lajnatul Hisbah Association of Nigeria ta karamar hukumar katsina bisa jagorancin shugaban ta Malam Muhammad Kabir Jihadi.

A inda shugaban kungiyar Lajnatul Hisbah na karamar hukumar katsina malam Muhammad kabir Jihadi ya nuna farin cikin shi matuka tare da karfafa gwaiwa ga jami'an hukumar Hisbah tare da bada shawarwari san nan ya nuna goyan bayan akan jagorancin malam shamsu kabir.

San nan daga bisani shugaban hukumar hisbah na karamar hukumar katsina malam shamsu kabir ya nuna jin dadin shi bisa ziyarar da kungiyar ta kawo ma hukumar hisbah a karkashin jagorancin malam Muhammad kabir Jihadi.

Daga karshe hukumar hisbah ta karamar hukumar katsina malam shamsu kabir ya ziyarci gidan daya daga cikin jami'an hisbah na karamar hukumar katsina (Abubakar Mu'azu) domin gabatar da ta'aziyya bisa rasuwar mahaifin sa.

Muna rokon Allah ya gafarta masa ya jikan sa ya sanya Aljanna itace makomar sa.

Reported by
Sardauna ICT Unit Hisbah Board KTLG.

KTSHBKATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YAYI TA'AZIYYA GIDAN BUNIN KAT...
23/04/2025

KTSHB
KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.

SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YAYI TA'AZIYYA GIDAN BUNIN KATSINA MAGAJI MODOJI

A yammacin yau Laraba 23 ga watan Aprilu shekara ta 2025 shugaban hukumar hisbah na karamar hukumar katsina malam shamsu kabir yayi ta'aziyya ga iyalan Marigayi Alhaji Salisu Ado Bunin Katsina Magaji Modoji.

Daga karshe muna Addu'ar Allah ya jikan shi ya gafarta mashi yayi masa rahama yasa Aljanna ta kasance makoma a gare shi.

Reported by
Sardauna ICT Unit Hisbah Board KTLG

Kusani Idan ka taba wanda Allah ke so, toh ka saurari zuwa azaba
23/04/2025

Kusani Idan ka taba wanda Allah ke so, toh ka saurari zuwa azaba

KTSHBKATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA HALARCI JANA'IDAR GIDAN AD ...
21/04/2025

KTSHB
KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.

SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA HALARCI JANA'IDAR GIDAN AD SAUDE.

A yammacin yau Litinin 21 ga watan Aprilu shekara ta 2025 shugaban hukumar hisbah na karamar hukumar katsina malam shamsu kabir ya halarci Jana'idar Alhaji Sanusi AD Saude.

Inda shugaban hukumar hisbah na karamar hukumar katsina yayi ta'aziyya ga dan majalissa karamar hukumar Hon Ali Abu Albaba da kuma Chairman na karamar hukumar katsina Hon Isah Miqdad AD Saude.

Daga bisani Shugaban hukumar Hisbah na karamar hukumar katsina malam shamsu kabir yayi ta'aziyya ga iyalan gidan AD Saude tare da Addu'o'i na musamman.

Daga karshe muna Addu'ar Allah ya jikan shi ya gafarta mashi yayi masa rahama yasa Aljanna ta kasance makoma a gare shi.

Reported by
Sardauna ICT Unit Hisbah Board KTLG

KTSHBKATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA HALARCI TARON KAMMALA KARAT...
20/04/2025

KTSHB
KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.

SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA HALARCI TARON KAMMALA KARATUN DAURA NA KUNGIYAR AL'UMMAH DIRECT RELIEF FOUNDATION.

A yau 20 ga watan Aprilu shekara ta 2025 shugaban hukumar hisbah na karamar hukumar katsina malam shamsu kabir ya halarci taron kammala daura na kungiyar Al'ummah Direct Relief Foundation.

A inda aka gudanar da taron a dakin taro na ofishin karamar hukumar katsina taron ya samu halartar manyan mutane da dama sun hada da Kwamandan Hisbah na Karamar hukumar katsina, Wakilin Chairman, Sheik Imam Aminu Yammawa, Alkali Abdurrahman, da sauran su.

A inda akayi zan hankali akan muhimmancin dogaro da kai, kula da tarbiyya, da kuma shawarwari na musamman.

Reported by
Sardauna ICT Unit Hisbah Board KTLG

KTSHBKATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR KATSINA TA GABATAR DA MOTSA JIKI NA MUSAMMAN GA...
19/04/2025

KTSHB
KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.

HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR KATSINA TA GABATAR DA MOTSA JIKI NA MUSAMMAN GA JAMI'AN HISBAH.

A yau Asabar 19 ga watan Aprilu shekara ta 2025 hukumar hisbah ta karamar hukumar katsina a karkashin jagorancin malam shamsu kabir ta gabatar da Motsa Jiki na Musamman ga jami'an hukumar Hisbah na karamar hukumar katsina.

Reported by
Sardauna ICT Unit Hisbah Board KTLG

KTSHBKATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA GABATAR DA PRE HUDUBAH A GA...
18/04/2025

KTSHB
KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.

SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA GABATAR DA PRE HUDUBAH A GARIN BAKURU TARE DA ZIYARA TA MUSAMMAN.

Shugaban hukumar Hisbah na karamar hukumar katsina malam shamsu kabir ya gabatar da Pre Hudubah akan kula da tarbiyya a cikin unguwanni a masallacin Ahlussunnah na Juma'ah garin bakuru.

A inda daga bisani shugaban hukumar hisbah na karamar hukumar katsina malam shamsu kabir tare da tawagar sa s**a ziyarci gidan mai unguwar bakuru malam Lawal.

Mai Unguwar ya nuna jin dadin sannan daga bisani ya gabatar da fatan alkhairi tare da addu'o'i na musamman ga hukumar hisbah.

Reported by
Sardauna ICT Unit Hisbah Board KTLG

KTSHBKATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISIONMUHIMMIYAR SANARWA!!!Amadadin Shugaban katsina local government division Malam Sha...
18/04/2025

KTSHB
KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION
MUHIMMIYAR SANARWA!!!
Amadadin Shugaban katsina local government division Malam Shamsu kabir yace a fada ma kowa da kowa duka jami'an hisbah na katsina local government Division akwai special Combat training da za'a gabatar a gobe Asabar 19/04/2025 da misalin karfe 8 na Safe a Muhammad Dikko Stadium (Karakanda) Katsina.

Sanarwa Daga Shugaba
Malam Shamsu kabir

DA DUMI DUMINSA: Wani Pastor ya tafi sama zuwa Aljanna domin k**awa jama'ar sa ɗaki, bayan sun bashi guzurin soyayyun ka...
15/10/2023

DA DUMI DUMINSA: Wani Pastor ya tafi sama zuwa Aljanna domin k**awa jama'ar sa ɗaki, bayan sun bashi guzurin soyayyun kaji

Kamar yadda zaku gani ga mabiyansa ne s**a ɗaga shi sama yana ƙoƙarin shiga cikin rufin Silin inda ta nan ne zai fasa rufin kwano ya wuce can sama zuwa Aljanna don ya k**a musu gidaje k**ar yadda yace.

Faston kafin ya tafi saida ya umarce su da su haɗa masa guzurin abincin da zai riƙa ci a kan hanyar zuwa aljannar kafin ya dawo.

Tuni mabiyan sa, s**a siyo gasassun kaji da balangu da tsire mai zafi da ruwan roba da kayan marmari s**a aje masa a cikin rufin Silin ɗin idan ya shiga zai ɗauka ya wuce sama.
Credit: Amintacciya

Ko Dr. Babangida Rumaa yana da abun cewa akan wannan

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hisbah Board KT L.G DIV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share