30/10/2025
Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗaukar sabon bashin waje na dala biliyan 2.35, domin cike gibi a kasafin kuɗin shekara ta 2025.
Shugaban Majalisar, Tajudeen Abbas, ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar a Abuja, inda ya ce kudaden za su taimaka wajen aiwatar da manyan ayyukan ci gaban ƙasa da kuma sake biyan wasu lamunin da s**a kai ƙarshen lokacin biyan su.
A cikin wasiƙar da shugaban ƙasa ya aika, ya bayyana cewa rance zai taimaka wajen fitowa daga kasuwannin Eurobond, bankunan waje, da kuma wasu cibiyoyin bashi na ƙasa da ƙasa.
Jimillar bashin Najeriya ya karu
Rahoton Hukumar Gudanar da Bashi ta Ƙasa (DMO) ya nuna cewa, jimillar bashin Najeriya ya kai naira tiriliyan 152.4 a tsakiyar shekarar 2025, wanda ya haɗa da lamunin cikin gida da na waje.
Wannan sabon rance na dala biliyan 2.35 zai ƙara nauyin bashin ƙasar, wanda a ƙarshen shekarar 2024 ya kai dala biliyan 94.2, kwatankwacin naira tiriliyan 70.3.
Dalilin karɓar sabon bashin
Gwamnati ta ce manufar sabon bashin ita ce cike gibin kasafin kuɗi na 2025, da kuma ƙarfafa fannonin tattalin arziki, tsaro, da aikin raya ƙasa.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce wannan mataki “yana da muhimmanci domin tabbatar da dorewar kasafin kuɗi da tallafa wa shirin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.”
Sai dai wasu masana sun bayyana damuwarsu cewa ƙarin ciyo bashin zai iya ƙara nauyin bashin ƙasar, wanda ke iya shafar kudaden shiga da ake warewa ga ayyukan walwalar jama’a.
Masana sun bukaci gwamnati da ta tabbatar da cewa dukkan kuɗaɗen da aka aro an yi amfani da su ta hanya mai inganci da gaskiya.