Bas Enlight Diary

  • Home
  • Bas Enlight Diary

Bas Enlight Diary Muna maraba da duk sakwannin ku kuma mun yi alkawarin kare mutunci da martabar kowa. Kuma ba ma bukatar a kawo m

Ban da faɗa ko zagi sa'annan ba ma bukatar kawo mana abinda bai shafi page ɗin nan ba.

14/01/2024

Admin don Allah ki ɓoye ID na ko zan samu 'yan uwa su bani shawara. Akwai wanda muke mutunci dashi kuma wallahi ina son shi amma shi kuma baya kulani, in akwai addu'ar da 'yan uwa zasu bani domin hankalin shi ya dawo gareni ina so.

Ina comment

Wallahi taɓa ganin masu ƙarfin imani da dogaro ga Allah irin Falasɗinawa ba, har fargabar shiga manhajar Tiktok nake yi ...
30/10/2023

Wallahi taɓa ganin masu ƙarfin imani da dogaro ga Allah irin Falasɗinawa ba, har fargabar shiga manhajar Tiktok nake yi saboda ba na iya yin sakwan talatin ba tare da na zib da hawayen baƙin cikin da 'yan'uwanmu Falasɗinawa ke ciki ba!

An zubar da su, an mance da halin da suke ciki ga wasu daga cikin shuwagabannin ƙasashen duniya har ma da ta addnina mai tsarki!

Falasɗinawa na cikin taashin har ta kai ga an fara yi musu hasashen mutuwar da za ta riske su a gaba zai haura na baya! Wayyo Allahna!!

Ya Hayyu ya Qayyum don tsarkin sunayen da Ka keɓance kanKa da su Ka taimaka wa Falasɗinu da Hamas, Ka karya Yahudawa da Isra'ila da ma duk masu goyon bayan su a faɗin duniya.

Ya Zuljalalu Wal Ikraam ga mu durƙushe a gabanKa cikin ƙasƙanci Ka ɗaukaka Musulunci da Falasɗinawa!

Falasɗinawa na kuka!ani

09/06/2023

Assalamu alaikum.

Duk wanda ya lizimci Salatin Annabi S.A.W, baƙin cikinsa ya gushe, zunubansa sun faku, Addu'o'insa sun karɓu, buƙatunsa sun biya da iznin Allah.

Mu yawaita kada muyi rowa.

Allhumma Salli Wa Sallim Ala Nabiyyina Muhammad.

Barkanmu da Juma'a 'yan Bas Enlight Diary

13/05/2023

Bangarori biyu dake yaki a kasar Sudan sun isa zuwa Kasar Saudiyya don Tattaunawar sulhu a karon farko. Saudiyya da Amrika ne s**a dauki nauyin wannan zaman na sulhu wanda za a gabatar da shi a birnin Saudiyya.

Tun makonnin da s**a gabata ake ta kokarin samun daidaito, yunkurin da aka kasa kai wa ga cimma shi. Duka ɓangarorin sun ce za su amince da tsagaita wuta domin bai wa fararen hula damar ficewa daga yankunan da yaƙin ya fi ƙamari.

A yau Asabar ne Ministan Harkokin wajen Ƙasar Saudiyya Faisal bin Farhan ya tarbi wakilan ɓangarorin biyu yayin da s**a isa ƙasar domin tattaunawar sulhun.

ya bayyana cewa, yana fatan tattaunawar za ta kawo ƙarshen rikicin tare da kawo zaman lafiya da tsaro a ƙasar ta Sudan.
Jagoran dakarun na RSF Janar Mohamed Hamdan Daglo ya bayyana a shafinsa na Tuwita cewa rundunar RSF ta yi maraba da matakin tsagaita wutar domin samun damar kai tallafi cikin ƙasar.Ya kuma kara da bayyana cewa RSF a shirye take domin mayar da mulki hannun farar hula a ƙasar.

04/09/2022

Tsakanin samarin Kano da samarin Kaduna wane ne ya fi iya daukar wanka da iya zance?

Ni dai na ce... Kadayake mu hade a comments box. 😂
Ku bayyana mana ra'ayin ku a comment section.

01/07/2022

Assalamu alaikum mutanen wannan gida namu mai albarka, dafatan mun same ku lafiya.

Wata tambaya ce gare ni...

Shin a matsayinka na namiji zaka iya bawa budurwar ka kidney din ka domin ta rayu?

Haka ma, a matsayin ki na 'ya mace in saurayinki ba shi da lafiya za ki iya ba shi kidney din ki domin ya rayu?

Mu hadu a comment section domin jin ra'ayoyin ku.

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bas Enlight Diary posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share