15/03/2025
Shin dagaske ne lemun kwalba na (Fearless) yanasa ciwon ƙafafu?
Lemun ƙara kuzari kamarsu (Fearless, predator, red-bull, power horse, monster, supa komando, bullet da sauransu) lemu ne wanda ake amfani dasu domin ƙara kuzari acikin jiki wanda suke ɗauke da sinadarai kamarsu;
Caffeine, Taurine, Added sugars , L carnitine, Ginseng extract, Guarana etc
Waɗannan sinadaran, an saka su ne dayawan gaske acikin lemun ƙara kuzari wanda hakan yakan haifarda illoli sosai acikin jikin mutum.
Waɗansu dagacikin illolin shan lemun ƙara kuzari sun haɗa da;
1. Caffeine overdose:
Wannan yana taɓa lafiyar zuciya ta hanyar zuciya ta ɗinga bugawa sosai har mutum yakamu da hawan jini batare da yasani ba.
Idan sinadarin caffeine yayi yawa acikin jikin mutum, zai iya sa mutum shiga fargaba, damuwa da rashin bacci
2. Weight gain:
Yawan shan energy drinks yakansa mutum yayi ƙiba sosai saboda yana ɗauke da calories masu yawa acikinsa wanda zai iya sa mutum yakamu da ciwon siga (Type 2 Diabetes) batare da mutum yasani ba.
3. Dental problems:
Yawan shan energy drinks yakansa mutum yakamu da ciwon haƙori
Haƙorin mutum zai iya yin kogo acikinsa tayanda idan kaci abinci mai sanyi ko zafi, zakaji raɗaɗi sosai.
4. Dehydration:
Yawan shan energy drinks yakan haifarwa mutum da ciwon ƙoda.
5. Joints inflammation and pain:
Ciwon gaɓoɓin jiki saboda yawan adadin sinadarin sikari da caffeine 📌
6. Insomnia:
Yawan shan energy drinks yakan haifarwa mutum da matsalolin bacci, wanda hakan yana taɓa lafiyar ƙwaƙwalwa da ciwon kai mai tsanani da rashin lafiyar ido 👁️
Bayan haka
Idan kasha lemun ƙara kuzari, to kar ka ƙara shan wani har sai bayan kwana biyu (48 hours)
Idan kasha lemun ƙara kuzari, yanada kyau ka motsa jiki kamar (kwallon kafa, jugging, tafiya mai nisan zango a ƙafa) domin inganta lafiyar jikinka da ƙonarda wannan sinadaran dake acikin wannan lemun
Idan kanada hawan jini ko ciwon siga, to yanada kyau ka ƙauracewa lemun ƙara kuzari idan kanason rayuwa acikin iyalinka.
Alhassan Mai Lafia