Four Star Tv

Four Star Tv Labarai Dominku

13/07/2025

S. A. W

GABAS TA TSAKIYA TA SAKE ƊAUKAR ƊUMI. Tuni dai yakin Gabasa tsakiya ta sake ɗaukar ɗumi da ruɗu bayan harin da Iran ta k...
24/06/2025

GABAS TA TSAKIYA TA SAKE ƊAUKAR ƊUMI.

Tuni dai yakin Gabasa tsakiya ta sake ɗaukar ɗumi da ruɗu bayan harin da Iran ta kai sansanonin sojin Amuruka a Iraq da Qatar. Wannan na zuwa ne awanni bayan ganawa da ministan harkokin waje Iran Abbas Araghchi ya yi da shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin a birnin Masko. Sai dai har yanzu ba a san haƙiƙanin abin da s**a yi magana a kai ba.

Idan ba a manta ba, Amurukq tai hari wuraren haɗa makamin Nukiliya mallakin Iran har guda a uku. Sai dai Iran ta yi kakkausan s**a tare da cin alwashin maida martani mai zafi ga Amuruka.

A yammacin wannan rana ne dai Iran ɗin ta kai hari kan sansanonin na Amuruka guda biyu, wanda hakan ya yi matuƙar janhalin duniya. Kuma ya yi matuƙar tashin hankalin ƙasashen Larawaba Musamman waɗanda sansanonin Amiruka ke kewaye da su. Tuni dai ƙasashen suke nuna rashin jin daɗi tare da yin Allah wadai da harin na Iran. Saudiya ta yi Allah wadai tare da nuna rashin jin daɗinta na abin da Iran ɗin ta yi.

A hannu guda kuma, tuni Qatar ta yi Allah wadai da harin; tana mai nuni da cewa harin ya saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa. Hukumomi a ƙasar sun ce, "sun samu nasarar kakkaɓo mak**ai masu linzami da dama waɗanda Iran ɗin ta harbo". Jaridar Doha News ta hasko wasu bidoyi na ɓaraguzan makami mai linzami da ta yi iƙirarin cewa irin waɗanda Qatar ɗin ta kakkaɓoni a harin.

Haka zalika jaridar ta rawaito ministan harkokin cikin gida na Qatar yana cewa "al'amura suna tafiya daidai a ƙasar bayan harin da aka kai a wannan rana ". Kuma Jaridar ta rawaito cewa an dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a faɗin ƙasar zuwa wani lokaci"
Tuni dai Iran ɗin ta bakin majalissar ƙoli ta tsaron ƙasar ta bayyana Qatar a matsayin ƙawa kuma ƴar uwa ga Iran. Suna mai cewa harin nasu ya kaucewa wuraren taruwar jama'a k**ar yadda "Doha News ta rawaito.

Ana zaman ɗar-ɗar a yakin Gabasa ta tsakiya, da rahotanni ke zuwa cewa an kai hari kan sansanin sojin Amuruka a Kuwait. Sai dai hukumomi a ƙasar sun ƙaryata wannan zance auna mai cewa babu wani abu da ya faru; k**ar yadda jaridar Kuwait Times ta rawaito.

ISR@ILA TA NEMI HAƊIN KAN AMURUKA DAN A HALLAKA KUMAINI. Rahotanni na tabbatar da cewa, firaministan Isr*ila Natanyahu y...
16/06/2025

ISR@ILA TA NEMI HAƊIN KAN AMURUKA DAN A HALLAKA KUMAINI.

Rahotanni na tabbatar da cewa, firaministan Isr*ila Natanyahu ya nemi haɗin kan shugaban Amuruka Trum dan a hakka shugaban addini a Ir*n Ayatullahi Ali Kumaini. Jaridar Sky news ta rawaito cewa:

"jaridar Reuters ta rawaito wasu makusantan fadar shugaban ƙasar Amuruka biyu sun tsegunta musu shirin da iran ɗin take yi na ganin an hallaka Kumaini. Sai dai majiyar ta ce tuni Trump ya nuna rashin amincewa da lamari"

A wani labarin kuma, rahonanni na nu ni da cewa tuni shugaba Kumaini ya ya koma maɓoyar ƙarƙashin ƙasa a Levizan a can Arewa maso Gashin Tehran awanni bayan Isr*ila ta ƙaddamar da hare*hare a Tehiran. Wasu majiyoyi biyu sun tseguntawa jaridar "Iran International -English" cewa Kumaini na ɓuye ne a maɓoyar tun a ranar Juma'ar da ta gabata. Tun bayan da Ira*ila ta kai hari kan muhimman wurare a Ir*an rahotanni na tabbatar da zazzafan martanin da Ir*an take kaiwa na ramuwa a kan wurare musamman a birnin Tel-aviv. Sai dai Isra*la tana cewa

"Ir*an ta kai harinta ne kan fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba"

Sai dai kuma gudajen jaridu da masu sharhi na nuni da irin mummunar ɓarnar da harin ya yi a Isr*aila tun bayan ƙaddamar da shi. Tuni dai hukumomi a ƙasar su ka buƙaci mutane da su ƙaurcewa wurare tare da umartarsu da su ɓuya.

Haka zalika, Aljazeera ta rawaito cewa

"An rufe filayen jirage, tare da kwashe jiragen ƙasar ciki harda jirgin gwmanati na Firaminista Natanyahu, an kai su Saifuros"

Jiragen sama sun soke zirga-zirga domin tsoron abinda ka je ya zo.

Bugu da ƙari, daren nan ƙasashen Qatar da Oman sun tuntuɓi Ir*an akan batun tsagaita wuta da Amurka ke neman ayi tsakanin Ir*an da Isr@'ila. Amma ƙasar Iran ta ƙeƙashe ƙasa tace:

"Ko kuwa kusa ko alama domin bata ga dalilin da zata fara tattauna batun tsagaita wuta ba tukuna..."

Reuters ta rawaito Ir*an na cewa:

"Isra'ila ta fara dakatar da hare haren da tun a farko ita ce ta fara sannan ita Iran ta duba yiwuwar tsagaita wuta..."

Allah ka raba mu da yaƙi.........
11/05/2025

Allah ka raba mu da yaƙi.........

07/05/2025

Good night

06/05/2025

Wata matar aure ta gurfana a gaban kotun Musulunci kan zargin auren maza biyu a lokaci guda a Jihar Kano.

23/03/2025

Da dumi'dumi: Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta bayar da sammacin k**a shugaban majalisar dattawan Najeriya bisa zargin yin lalata da Sen Natasha

Rahotanni sun bayyana cewa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta sanya shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, cikin jerin takunkumin da kasashen duniya s**a sanyawa takunkumi, inda ta bayar da umarnin k**a shi ba tare da bata lokaci ba idan aka ganta a wata kasa.

An kuma aika da wata takarda ta musamman ga gwamnatin Najeriya, inda ake kira ga shugaba Bola Tinubu da ya dauki mataki.

Sammacin dai ya biyo bayan zargin da wata ‘yar majalisar dattawan kasar Sen Natasha ta yi masa na zargin Akpabio da lalata da kuma sumbata. Ta yi ikirarin cewa tana da shaidun bidiyo da ke tabbatar da ikirarin nata, wanda kotun ta ICC ta tabbatar da cewa sun yi nazari gaba daya kafin ta ba da umarnin k**a.

Daga Shafin Mikiya

14/03/2025

Allah ya karɓi ibadunmu ya biya buƙatunmu.

Celebrating my 3rd year on Facebook. Thank you for your continuing support. I could never have made it without you. 🙏🤗🎉
26/01/2025

Celebrating my 3rd year on Facebook. Thank you for your continuing support. I could never have made it without you. 🙏🤗🎉

29/12/2024

Saɓani tsakanin Najeriya da Nijar

Saɓani ne da ya samo asali tun shekarar bara, bayan da sojojin ƙasar s**a hanɓare zaɓaɓɓen shugaban farar hula Muhamad Bazoum, bisa zarginsa da laifin cin amanar ƙasa, zargin da har kawo rana irin ta yau gwamnatin sojin Nijar ba ta gabatarwa duniya bayyanannun hujjojin da suke tabbatar da hakan ba, wanda zamu iya gane cewa zargi ne marar tushe b***e mak**a.

Wannan juyin mulki a ƙasar dake cikin gamayyar ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) guda goma sha biyar, ya jawo rabuwar kai a tsakanin ƙasashe membobin ƙungiyar, inda guda goma sha ɗaya a ƙarkashen mulkin farar hula s**a ja tungar goyon bayan dawo da mulkin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da aka hamɓare, guda hudu kuma a ƙarƙashin mulkin soji s**a goyi bayan masu juyin mulkin, sai dai abin sani anan shi ne, goma sha huɗun nan suna da tarihin kin mulkin mallaka da kuma mulkin gwamnatin soji.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu shi ne shugaban wannan gamayyar ƙasashe, wanda sananne ne akansa cewar ya shafe wani kaso mai yawa na rayuwarsa yana gwagwarmayar adawa da tsarin mulkin soja a Najeriya. Wannan abu ne wanda yake sananne ga dukkan wanda ya san tarihin siyasa da gwagwarmayar da Mista Bola Tinubu yayi a baya.

A tsawon tarihi, Najeriya da Nijar zaman ‘yan uwantaka suke yi, in ban da wannan karon da gamayyar ƙasashen ECOWAS s**a ɗauki matakin hukunta gwamnatin sojan Nijar ɗin da s**a yi juyin mulkin, hukuncin da ya ƙunshi dakatarwa da sanya takunkumin tattalin arziƙi, shige da fice, diplomasiyya da sauran danginsu akan waɗancan ƙasashe huɗu, wannan kuma yarjejeniya ce aka cimma ba ra'ayin shugaba Tinubu ba.

Matakan da shugabancin ECOWAS ya ɗauka matakai ne masu kyau da tsayawa a tsaka tsaki, wanda duk mai hankali zai fahimta kuma ya gamsu da su, domin rashin ɗaukar mataki akan wancan juyin mulki, tamkar amincewa ne da mulkin bakin bindiga, mulkin k**a karya, da kuma gayyato sojoji a sauran ƙasashe akan su sake fitowa daga bariki su ƙwaci mulki a kasashensu. A duniyar yau, soji ba shi da gurbi a jagorantar gwamnati. Ra'ayin al'umma mafiya rinjaye shi ne yake jagoranci.

Yasir Ramadan Gwale
29.12.2024

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Four Star Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Four Star Tv:

Share