
22/05/2025
Wata bazawara ta kasance tana riƙon wata kyakkyawar budurwa. Duk wanda ya zo neman aurenta sai Bazawarar ta ce, ita ba zata bada aurenta ba sai an biya kuɗin aure da ɗawainiyarsa naira Miliyan 20, babu kuwa ragin ko Sisi. Da yawan samari s**a haƙura da aurenta.
Wani saurayi, ya ga budurwar nan yana sonta, ita kuma ta gaya masa ƙa'idar aurenta. Saurayi ya je gida ya faɗawa Babansa tsarin auren budurwar da yake so. Saurayi ya ce, yana da naira Miliyan 15 ta ribar kamfaninsa da ya samu.
Babansa ya ce, kawo 15m, saurayi ya kawo. Babansa ya ɗauke shi s**a nufi gidan Bazawarar nan.
Babansa ya ce, zan yi magana amma kar ki katse ni sai na je ƙarshe. Bazawara ta ce, toh.
Baban Saurayi ya ce, ga 5m kuɗin auren ƴar da k**e riƙo.... Za ta yi magana ya ce, ta yi shiru... Ga kuma Naira 5m ni mahaifin wannan yaro na ganki ina sonki, zan aureki.
Take Bazawara ta ce, Masha Allah, Alhamdulillah, komai ya yi daidai, Allah ya bamu zaman lafiya. Sai a ɗaura kawai....!!!
Mutane s**a ce, ke da k**e neman 20m ta ya ya kika ƙare a 10m? Sai ta ce Allah sarki, SIYAN JIMLA AI BA DAIDAI YAKE DA SIYAN ƊAIƊAI BA....!!!!
Shi kuma Saurayi ya yiwa Babansa godiya ya ce, har canjin 5m na samu, sai a bani na ƙarasa ɗawainiyar biki... Baban ya ce, Kai baka da hankali ne, baka fahimtar lissafi, wannan 5m ɗin da ta rage BABARKA ZA A BAWA, TA DANNAR ƘIRJI CE.....!!!!!