25/10/2025
Ambasada Halima Shehu ta ce ba za ta iya Auren Bahaushe
Ma'abociyar kafafen sada zumuntar zamani Amb. Halima Shehu, ta janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan ta wallafa rubutu mai ɗauke da kalmomin da s**a tada kura ga hausawa.
A cikin rubutunta na Facebook, ta bayyana cewa:
“Zan iya auren kowace ƙabila amma banda Bahaushe domin kuwa nayi, ban ji daɗi ba.”
Wannan furuci nata ya haifar da muhawara tsakanin masu bibiyar shafinta, inda wasu ke goyon bayanta suna cewa “kowa yafi sanin inda takalmin ya matse masa”, yayin da wasu kuma s**a zarge ta da nuna wariya da raina hausawa.
Wasu na ganin cewa wannan magana za ta iya zama darasi ga matasa musamman a sha’anin zaɓin abokin aure, yayin da wasu s**a ce bai dace mace mai matsayi irin nata ta fadi irin wannan kalma ba.