14/05/2026
ASIRI YA TONU: An Bankado Hakikanin Shekarun Hon. Abun Al’ajabin Zazzau
Wani fasfo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya bayyana bayanan da ake zargin na Hon. Mahmud Sadis Buba (Abun Al’ajabin Zazzau) ne. Fasfon ya nuna cewa an haife shi ne a shekarar 2010, wanda hakan ke nuna cewa shekarunsa kusan 16 a yanzu.
Sai dai a wata hira da aka yi da shi a baya, Hon. Abun Al’ajabin Zazzau ya bayyana cewa yana da shekaru 30, lamarin da ya sa mutane da dama s**a fara tambayar wanne bayani ne gaskiya.
Yanzu haka jama’a na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu, musamman ganin cewa dokar zaɓe a Nijeriya ta tanadi cewa dole sai mutum ya kai shekaru 25 kafin ya tsaya takarar wasu muk**ai.
Idan har wannan fasfo gaskiya ne, me zai kasance makomar takararsa da kuma fom ɗin da aka ce ya saya?
💬 Kai fa me kake cewa a kan wannan lamari?
hausa news 25
Mai Isar da Gaskiya”