25/01/2026
Wani abin mamaki da al'ajabi game da Babban Masallacin Makka (Masjid al-Haram)
shi ne gini mafi tsada a duniya, an gina shi da kuɗin da ya kai dala biliyan 100 ($100 Billion).
Girma:
• Murabba’in mita 1,000,000
Ƙarfin ɗaukar mutane:
🕋 Zai iya ɗaukar mutane miliyan 2 lokaci guda
🕋 Yana karɓar baƙi miliyan 20 a kowace shekara
🕋 Yana buɗe awanni 24 a rana
🕋 Ba a taɓa rufe shi gaba ɗaya ba tsawon shekaru sama da 1,400
---
Tsabta da Kulawa:
🕋 Ma’aikatan tsabta 1,800
🕋 Motocin tsabta na lantarki 40
🕋 Na’urorin tsabtace fili na lantarki 60
🕋 Kwantena/kwandunan shara 2,000 a ko’ina cikin harami
🕋 An shimfiɗa kafet 40,000
(tsawon su ya fi nisan Jeddah zuwa Makka – km 79)
---
Bandaki da Ruwa:
🕋 Bandaki 13,000, ana wanke su sau 4 a kowane awa 6
🕋 Na’urorin ruwan sha 25,000
(daya daga cikin manyan tsarin rarraba ruwa a duniya)
🕋 Ana duba samfuri 100 na ruwan sha a kowace rana
🕋 Karin ruwan rijiyar Zamzam ana adana shi a tankuna
da ƙarfin kwalaben ruwa miliyan 1.7 (lita 10 kowanne)
---
Karanta Al-Qur’ani & Watsa Shirye-shirye:
🕋 Sabis na Haramain Recitation – karatun Al-Qur’ani awanni 24/7
🕋 Ana karantawa da hanyoyi 10 da aka amince da su
🕋 Fiye da shiri 500,000 aka watsa zuwa ƙasashe 180 cikin shekaru 3
---
Tsaro & Jin Daɗi:
🕋 Akwatunan ajiya fiye da 2,000 don kayan mutane
🕋 Na’urorin sanyaya iska daruruwa a cikin masallaci
🕋 Ƙasan masallaci yana mayar da haske da zafi, yana rage zafin wurin
🕋 Manhajar jagorar yawon buɗe ido (Electronic Tour Guide)
– tana nuna duk wani sashe na masallaci
---
Tsarin Sauti (Audio System):
🕋 Daya daga cikin manyan kuma mafi rikitarwa a duniya
• Kuskuren sauti: 0%
• Makirufo/speakers 6,000
• Tsarin sauti 4 daban-daban
• Ma’aikatan injiniyan sauti 50
---
Harsuna & Fassara:
🕋 Al-Qur’ani an fassara shi zuwa harsuna 65
🕋 Hudubar Juma’a ana fassara ta zuwa harsuna 5
---
Sabis ga masu buƙata ta musamman:
🕋 Keken guragu 10,000 kyauta
🕋 Keken lantarki 400
🕋 Kekunan atomatik (ƙafafu 2 da 3)
---
Sabis na Musamman a Watan Ramadan:
🕋 Abinci kyauta miliyan 4 a kowace rana don buɗa baki
🕋 Dabino miliyan 5 ana rarrabawa kullum
🕋 Bayan buɗa baki, ana share wurin sallar Maghrib cikin minti 2 kacal
---
SUBHANALLAH 🤍🕋
Girman ni’ima, tsari da kula da Masallacin Harami abin mamaki ne.
Kuyi sharing idan abin ya burgeku