Jigawa FM 93.5 Andaza

  • Home
  • Jigawa FM 93.5 Andaza

Jigawa FM 93.5 Andaza Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Jigawa FM 93.5 Andaza, Radio Station, .

03-06-2025               HAJJHukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta kaddamar da rabon manyan jakankuna ga maniyata...
03/06/2025

03-06-2025 HAJJ
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta kaddamar da rabon manyan jakankuna ga maniyata a Birnin makka
Darakta janar na hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce an raba jakankunan ne ga shugabannin shiyya shiyya domin su ne matakin farko
Ya ce shugabannin alhazan na shiyya shiyya zasu aiki tare da jamian alhazai na kananan hukumomi wajen rabon manyan jakankunan
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kara da cewar hukumar ta karbi manyan jakankuna 930 na maniyatan jihar

03/06/2025 RAMMasu sayar da raguna a kasuwar Shuwarin dake yankin karamar hukumar Kiyawa sun koka dangane da karancin ma...
03/06/2025

03/06/2025 RAM
Masu sayar da raguna a kasuwar Shuwarin dake yankin karamar hukumar Kiyawa sun koka dangane da karancin masu sayen ragunan yayin da babbar Sallah ke kara gabatowa.
Rahotanni sunce masu sai da ragunan sun danganta karancin masu sayen ga hauhawar farashi sak**akon dakatar da shigo da raguna daga jamhuriyar Nijer.
Matakan da hukumomin gwamnatin mulkin soji s**a dauka na takaita mu`amula a tsakanin iyakar Najeriya da Nijer, ya haddasa karancin shigo da dabbobi lamarin da ya haifar da karuwar farashin ragunan a kasuwanni.
Wakilinmu yace ana sayar da manyan raguna daga naira dubu dari da tamanin zuwa naira dubu dari tara da tamanin, yayin da ake sayar matsakaicin rago akan naira dubu dari da sittin.
Haka kuma farashin rakumi ya k**a daga naira dubu dari bakwai da tamanin zuwa fiye da naira miliyan daya.
Tuni dai magidanta s**a koka dangane da tashin gwauron zabbin farashin raguna da sauran dabbobi, yayin da dama s**a ce bazasu sami damar yin layya ba a wannan shekarar.

11-05-2025                  GWAMNA/GARKIGwamna Umar Namadi ya bayyana farin cikinsa da addu’o’i da goyon bayan da ake ba...
11/05/2025

11-05-2025 GWAMNA/GARKI
Gwamna Umar Namadi ya bayyana farin cikinsa da addu’o’i da goyon bayan da ake bai wa wannan gwamnati domin samun nasara.
Ya bayyana hakan ne a taron gwamnati da jama-a na karamar hukumar Garki.
Malam Umar Namadi ya bayyana cewa hakan ya kara masa kwarin gwiwa wajen ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su rage rashin aikin yi, bunkasa tattalin arziki da kuma inganta ci gaban ababen more rayuwa a fannoni daban-daban.
Ya bayyana farin cikinsa bisa kyaututtuka na musamman da kungiyoyin manoma, makiyaya, matasa da ‘yan siyasa na karamar hukumar Garki s**a mika masa.
Gwamnan ya kuma yaba da goyon bayan dattawan jam’iyyar APC na jihar tare da sha alwashin ci gaba da aiki tare wajen aiwatar da tsarin maki goma sha biyu domin ciyar da Jihar Jigawa gaba.
Malam Umar Namadi ya kuma mika irin wannan godiya ga shugabannin addini, na gargajiya da na al’umma a fadin jihar.

Gwamnonin Arewa tare da sarakunan gargajiya sun tattauna kan batutuwan da s**a shafi yankin, ciki har da batun matsalar ...
10/05/2025

Gwamnonin Arewa tare da sarakunan gargajiya sun tattauna kan batutuwan da s**a shafi yankin, ciki har da batun matsalar rashin tsaro da sauran batutuwan dake damun al'ummar yankin, a fadar gwamnatin jihar Kaduna ranar Asabar.

A lokacin taron, gwamnonin sun jaddada goyon bayansu kan batun ƙirƙiro da ƴan sandan jihohi.

09-05-2025                           GOV/WIFEMai dakin Gwamnan jihar Jigawa, Hajiya Amina Umar Namadi ta kaddamar da rab...
09/05/2025

09-05-2025 GOV/WIFE
Mai dakin Gwamnan jihar Jigawa, Hajiya Amina Umar Namadi ta kaddamar da rabon kayan sawa na makaranta da kayayyakin karatu ga Dalibai marayu da masu rangwamen gata su 500 a masarautun Kazaure da Ringim.
Da take jawabi yayin kaddamar da rabon kayayyakin, Hajiya Amina Umar Namadi ta ce tallafawa marasa karfi da marayu tare da basu ilimi mai nagarta zai taimaka su rayu cikin aminci
A nata jawabin mai baiwa Gwamna shawara a bangaren ilimi matakin farko, Dakta Hauwa Mustapha Babura, ta ce bunkasa ilimi a jihar Jigawa na daya daga cikin manufofin Gwamna, Malam Umar Namadi goma sha biyu..
Shima a nasa jawabin shugaban karamar hukumar Kazaure, Alhaji Mansur Usman Dabuwa ya bayyana farin cikin sa, tare da godewa mai dakin gwamnan bisa wannan abin alheri da ta kai masarautar Kazaure, inda ya ce samar da kayayyakin zai karfafa gwiwar wadanda abin ya shafa su nemi ilimi.

16-04-2025                     BUJIWasu magoya bayan jamiyar PDP a mazabar Chirbun Dake Karamar Hukumar Buji sun sauya s...
16/04/2025

16-04-2025 BUJI
Wasu magoya bayan jamiyar PDP a mazabar Chirbun Dake Karamar Hukumar Buji sun sauya sheka zuwa jamiyar APC, bisa aiyukan raya kasa da shugaban KH ya yi musu na mayar da Injin bada ruwan sha na garin zuwa mai amfani da hasken rana da kuma gyaran wutar lantarki da aka musu
Sabbin yan jamiyyar ta APC da s**a sami jagorancin Kamsilan mazabar Chirbun Sunusi Barau sunce rabonsu da zuwa sakatariyar KH Buji shekaru goma kenan.
Da yake jawabi , Mai Kura Unguwar Maina yace ko a zaben kananan hukumomi da ya gabata ba sa jamiyyar APC amma a yanzu sun ga irin aiyukan da shugaban KH Najib Falalu Tukur ya tabbatar da inganta rayuwar alummar garin.
Tun da farko a jawabin sa na godiya Dagachin Garin Unguwar Maina Alhaji Bala Ubah ya ce limamai da masu unguwanni da matasan garuruwa sun ziyarci shugaban KH kuma basu da wata kalma dazasu fada masa illah adduar Allah ya Kara masa kwari Gwiwa wajan samun nasarar cigaba da aikata aiyukan Alkhairi. Da yake maida jawabi shugaban KH NAJIB FALALU TUKUR ya yiwa sabbi Yan jamiyar APC maraba tare da basu tabbacin yin tafiya tare dasu
Ya kuma bukaci alummar yankin dasu cigaba da yiwa Gwamna Umar Namadi adduar samun nasara aiwatar da manufofin sa goma Sha biyu.

16-04-2025                   COUNCILGwamnatin Jihar Jigawa ta umurci kamfanonin tsaro masu zaman kansu guda uku da ke ai...
16/04/2025

16-04-2025 COUNCIL
Gwamnatin Jihar Jigawa ta umurci kamfanonin tsaro masu zaman kansu guda uku da ke aiki a jihar nan da su baiwa mata ma’aikatansu damar saka hijabi yayin da suke bakin aiki.
Kwamishinan Yaɗa Labarai , Alhaji Sagir Musa Ahmad, ne ya bayyana hakan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jiha.
Ya ce wannan umarni na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin samar da yanayi na haɗin kai da fahimta ga kowa da kowa musamman mata.
Kwamishinan ya ƙara da cewa an yanke shawarar ne bayan rahoton da kwamitin majalisar kan tsaron makarantu da asibitoci da kotuna ya gabatar.
Ya ce akwai bukatar kamfanonin su bai wa matan da ke aiki da su damar saka hijabi yayin aiki daga cikin waɗanda aka ɗauka aikin tsaro su 9,969 a matsayin girmamawa ga addini da al’adun al’umma.
Hakazalika, ya bayyana cewa majalisar ta amince da fitar da kudi naira miliyan 516 domin sayen tikitin jirgi na dawowar dalibai 184 da tikitin tafiya guda 185 ga ɗaliban Jihar Jigawa da ke karatu a fannoni na likitanci da kimiyyar lafiya a Jami’ar Near East da ke ƙasar Cyprus.
Haka kuma, kwamishinan ya sanar da amincewar majalisar wajen kaddamar da makon ƙirƙira da ƙere-ƙere na Jihar Jigawa daga shekarar 2025.

16-04-2025                       HANDSShirin kula da lafiyar Ido na Hands tare da tallafin shirin CMB dake samun tallafi...
16/04/2025

16-04-2025 HANDS
Shirin kula da lafiyar Ido na Hands tare da tallafin shirin CMB dake samun tallafin gwamnatin kasar Jamus sun bada gudunmawar kayayyakin kula da lafiyar ido ga asibitin koyarwa na jamiar tarayya ta Dutse dake Rashed Shekoni
A jawabinta wajen mika kayayyakin, wakiliyar shirin kula da lafiyar Ido na CMB a Nigeria Mrs Angela ta ce gudunmawar na daga cikin yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin su da asibitin koyarwa na jamiar tarayya ta Dutse.
Ta ce kayayyakin zasu taimaka wajen kula da lafiyar ido na kananan Yara, inda ta ce shirin na hands da CMB ya dade yana hadin gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa wajen kula da lafiyar ido
Mrs Angela ta yi fatan za su cigaba da yin hulda da asibitin koyarwa na jamiar tarayya ta Dutse k**ar yadda suke da gwamnatin jihar Jigawa
A jawabinsa babban likitan asibitin koyarwa na jamiar tarayya na Rasheed Shekoni Dr Salisu Muazu ya yaba da wannan gudunmawa da shirin hands ya baiwa asibitin tare da alkawarin yin cikakken amfani dashi wajen cimma manufofin samar da kayayyakin
Ya yi fatan zasu cigaba da yin hulda da shirin wajen bunkasa harkokin kiwon lafiyar ido a asibitin
Dr Salisu Muazu ya ce kofar asibitin a bude take domin yin hulda da duk wata kungiya ko shiri da yake da muradin cigaban alummar jihar Jigawa

14/04/2025

Mita 93…5

12/10/2024

12-10-2024 COMMITTEE
Gwamnatin jihar Jigawa ta kafa kwamiti domin binciken kalaman riga malaman masalaci kan batun aiwatar da biyan sabon tsarin albashi ga maaikatan jihar nan
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jiha Malam Bala Ibrahim ya sanyawa hannu
Sanarwar ta nuna damuwarta bisa kalaman da aka yi kan batun aiwatar da biyan sabon tsarin albashi na naira dubu sabain, yayinda kwamitin bada shawara kan aiwatar da biyan sabon tsarin albashin karkashin shugaban maaikata bai kammala aikin sa ba domin gabatar da rahotansa
A cewar gwamnati, kwamitin zai yi bincike akan hanyoyin da labarin ya fito da kuma wanda ya bada labarin
Malam Bala Ibrahim ya ce kwamitin yana karkashin jagorancin kwamishinan sharia Barista Bello Abdulkadir Fanini
Sauran wakilan kwamitin sun hadar da kwamishinonin yada labarai Sagir Musa Ahmed da na lafiya Dr Muhammmad Abdullahi Kainuwa da babban sakataren harkokin maaikata Muhammad Yahaya Jabo yayinda babban sakataren sashen bincike da harkokin siyasa Abba Mustapha Yola zai kasance sakataren kwamitin
An baiwa kwamitin waadin makonni biyu domin gabatar da rahotansa
Haka kuma gwamna Umar Namadi ya amince da dakatar da mai bashi shawara kan harkokin fansho da albashi Alhaji Bashir Ado Kazaure har zuwa lokacin kammala aikin kwamitin bincike da aka kafa domin bada rahotan sa nan da kwanaki 14

20/09/2024
22/08/2024

22-08-2024 WOMEN
Jigawa State Ministry of Women Affairs and Social Development has spent over three million naira on the purchase of items at the Reformatory home in Kafin Hausa.
Commissioner of the Ministry Hajia Hadiza Tamuri AbdulWahab disclosed this while inspecting the items.
She said the gesture will go a long way in improving the living standard of the inhabitants.
The items provided include beds, mattresses, blankets, household materials and uniforms.
The Commissioner also pledged to liaise with the ministry of Justice on the issue of the over-aged inhabitants.

MAG/BS

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jigawa FM 93.5 Andaza posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share