
20/07/2025
Ziyarar Mataimakiyar Sakataren Ƙungiyar Ƙasashen Duniya (UN), Hajiya Amina J. Mohammed, Zuwa Wajen Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin Mataimakiyar Sakataren Ƙungiyar Ƙasashen Duniya (UN), Hajiya Amina J. Mohammed, wadda ta kai ziyarar aiki zuwa Kano.
Ziyarar na cikin yunƙurin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar Ɗinkin Duniya wajen aiwatar da manyan manufofin cigaban duniya (SDGs), musamman a fannonin ilimi, ƙarfafa matasa da mata, da sauya fasalin muhalli.
Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna godiya bisa wannan ziyara tare da yabawa irin tallafi da goyon bayan da ƙungiyar ke baiwa jihar Kano. Ya kuma bayyana aniyar gwamnatinsa na ci gaba da aiki tukuru don cimma burin ci gaban al’umma da daidaito.
A nata jawabin, Hajiya Amina J. Mohammed ta bayyana jin daɗinta da kokarin da gwamnatin Kano ke yi wajen inganta rayuwar jama'a, tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyi domin kawo ci gaba mai ɗorewa.
Ziyarar ta haɗa da ganawa da manyan jami’an gwamnati, wakilan ƙungiyoyin haɗin gwiwa, da wakilan al’umma, domin tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin kai.
© Shehu Saleesu Farawa ✍️