Hausa Trust News

  • Home
  • Hausa Trust News

Hausa Trust News Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hausa Trust News, TV Channel, .

Na Je Har Wurin Shugaban Kasa Ya Kira Ni Da Dakta, Haka Gwamnoni Ma Suna Kirana Da Dakta, Sai Kuma Wani Can Ya Zo Yana K...
30/11/2025

Na Je Har Wurin Shugaban Kasa Ya Kira Ni Da Dakta, Haka Gwamnoni Ma Suna Kirana Da Dakta, Sai Kuma Wani Can Ya Zo Yana Kokwanto, Cewar Dauda Kahutu Rarara

OPA Ta Soki Naɗin Amupitan a Matsayin Shugaban INEC, Ta Ce Cancantarsa Ba Ta Kai Ya Riƙe Hukumar Zaɓe BaOdua People’s As...
28/11/2025

OPA Ta Soki Naɗin Amupitan a Matsayin Shugaban INEC, Ta Ce Cancantarsa Ba Ta Kai Ya Riƙe Hukumar Zaɓe Ba

Odua People’s Assembly (OPA) ta fito fili ta bayyana rashin gamsuwarta da nadin Joash Ojo Amupitan, SAN, a matsayin sabon Shugaban INEC, tana cewa wannan nadin na iya zama barazana ga sahihancin zaɓe da kwanciyar hankali na demokradiyya a Najeriya.

A cikin sanarwar da Richard Olatunji Kayode ya fitar, OPA ta ce kasar tana fuskantar mawuyacin hali na rashin amincewa da sakamakon zaɓe, don haka wajibi ne INEC ta samu shugaba mai gaskiya, kwarjini da cikakken tarihin tsayuwa kan adalci wanda duka wannan halayen Amupitan bai cika su ba.

Kungiyar ta goyi bayan ƙungiyar kwararrun lauyoyi sama da 1,000 (ALDRAP), wadda ta riga ta yi tir da nadin, tana cewa akwai bayanan da ke nuna alakar siyasa tsakanin Amupitan da Ministan Abuja, Nyesom Wike, wasu majiyoyin ma na zargin yaron Wike ne, alakar da OPA ta ce na iya haifar da shakku game da ikon Amupitan na yin aikin da bai dace ba.

OPA ta yi gargadin cewa duk wani shugaban INEC da ke da inuwa ko kusanci da manyan ‘yan siyasa ba zai iya gina sahihin tsarin zaɓe ba. Ta ce idan aka yi watsi da waɗannan korafe-korafe, za a iya sake fadawa cikin rikici, rashin tabbas da asarar amincewar jama’a ga INEC.

Ta bukaci Majalisar Dattawa da ta yi amfani da mukamin amincewa cikin gaskiya, ba tare da siyasa ta shige ciki ba, domin kare demokradiyyar Najeriya.

A ƙarshe, OPA ta kira kungiyoyin farar hula, matasa, lauyoyi da ‘yan jarida su kasance masu sa ido, su kare muradun kasa, domin a samar da INEC da za ta yi aiki bisa gaskiya, ba tare da fargaba ko tsoron siyasa ba.

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Najeriya tayi Allah-wadai da yin juyin mulkin da Sojoji s**a yi a kasar Guinea-Bissau.
27/11/2025

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Najeriya tayi Allah-wadai da yin juyin mulkin da Sojoji s**a yi a kasar Guinea-Bissau.

ALLAHU AKBAR: Yanzu haka jama'a sun fara taruwa a harabar masallacin Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Allah Ya jikan...
27/11/2025

ALLAHU AKBAR: Yanzu haka jama'a sun fara taruwa a harabar masallacin Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Allah Ya jikanshi da rahama, ya gafarta masa kura-kuransa.

📷 Albarka Radio

NDYC Ta Caccaki Wike da INEC Kan Yunkurin Rusa Dimokuraɗiyyar NajeriyaƘungiyar Niger Delta Youth Congress (NDYC) ta yi t...
25/11/2025

NDYC Ta Caccaki Wike da INEC Kan Yunkurin Rusa Dimokuraɗiyyar Najeriya

Ƙungiyar Niger Delta Youth Congress (NDYC) ta yi taron ’yan jarida domin bayyana damuwa kan yadda Ministan FCT, Nyesom Wike, da kuma yadda INEC ke nuna rashin adalaci game da sakamakon gangamin PDP na Ibadan ke zama babbar barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya.

NDYC ta zargi Wike da amfani da muƙaminsa wajen tsoma baki cikin jam’iyya, tayar da rikici, tsoratarwa da kokarin tilasta ra’ayinsa, abin da ke yi wa tsarin dimokuraɗiyya mummunar illa. Ta ce halayensa na nuna girman kai, raina doka da neman iko su na iya tarwatsa ƙasa.

Kungiyar ta roki Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi Wike, ya tunasar da shi cewa shi bawa ne na jama’a, ba sarki ba.

A bangaren INEC kuwa, NDYC ta nuna damuwa kan yadda take jan kafa wajen tabbatar da zababben shugaban PDP Kabiru Turaki, tana nuna fifiko ga Damagum. Ta ce wannan ya tauye adalci, ya kuma lalata amincewar jama’a da hukumar zabe.

NDYC ta jaddada cewa sakamakon taron Ibadan halastacce ne, kuma INEC dole ta tsaya kan doka ba tare da shiga hannun masu son murde sakamakon siyasa ba don biyan buƙatar Wike.

Ta kuma bayyana cewa halayen Wike ba sa wakiltar mutanen Niger Delta gaba ɗaya.

A ƙarshe, NDYC ta ce za ta ci gaba da kare dimokuraɗiyya da doka, domin Najeriya ta fi kowane mutum girma, kuma duk wanda ya yi barazana ga tsarin mulki dole a tsawatar masa.

Da hannun
Comr. Israel Uwejeyan, National Coordinator, NDYC

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Matar Sarkin Zazzau-Suleja, Wato Hajiya Ramatu Awwal Ibrahim Ta RasuTa rasu ne a bi...
22/11/2025

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Matar Sarkin Zazzau-Suleja, Wato Hajiya Ramatu Awwal Ibrahim Ta Rasu

Ta rasu ne a birnin Cairo dake kasar Masar, inda tuni aka yi jana'izar ta a can.

Allah Ya gafarta mata.

Tsayuwar Daka a Ibadan: Yadda Kauran Bauchi, Dauda Lawal da Makinde S**a Ceto Mutuncin Jam'iyyar PDPA babban taron da ja...
21/11/2025

Tsayuwar Daka a Ibadan: Yadda Kauran Bauchi, Dauda Lawal da Makinde S**a Ceto Mutuncin Jam'iyyar PDP

A babban taron da jam’iyyar PDP ta gudanar a Ibadan ranar Asabar da ta gabata, an ga wani sabon salo na shugabanci da jajircewa wanda ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa PDP har yanzu tana da waɗanda za su tsaya tsayin daka domin kare darajarta.

A cikin waɗanda s**a fito fili wajen nuna wannan kwazo, akwai Kauran Bauchi, wanda ya jagoranci aikin gyara da tsaftace jam’iyya da tsantseni. Tsayuwarsa wajen korar masu tada zaune tsaye a ciki, musamman waɗanda ke aiki da boyayyun manufa don rusa jam’iyyar daga cikin gida, ya zama abin yabo da koyi. A gaskiya, Kauran Bauchi ya zama ginshiƙin da ya hana jam’iyyar durkushewa.

Baya ga haka, Gwamnan Zamfara Dr. Dauda Lawal ya nuna irin kishinsa ga dimokuraɗiyya. Goyon bayansa ga sahihin tsari da adalci a cikin jam’iyya ya karfafa gwiwar mambobi da magoya baya, ya tabbatar masu cewa PDP na da shugabanni da ba za su lamunci karya ko shisshigi ba.

A bangaren Seyi Makinde, Gwamnan jihar Oyo, ya ba da cikakken gudunmawa wajen tabbatar da cewa taron Ibadan ya kasance sahihi, kuma cikin tsarin da ya dace. Makinde ya tabbatar da cewa jam’iyya ta gudana bisa ka’ida, ba tare da batan batu ko rikice-rikice ba, aikin da ya kara tabbatar da cewa PDP jam’iyyar da take da ni’imar shugabanni masu hangen nesa.

A tare, waɗannan manyan shugabanni uku sun yi abin da ake kira ceto martabar PDP, tare da dawo da yarda da kwarin gwiwar jama’a. Sun nuna cewa jam’iyyar adawa ba ta mutu ba, kuma ba za ta mutu ba, muddin akwai shugabanni irin su Kauran Bauchi, Dr. Dauda Lawal da Seyi Makinde.

A Ibadan, PDP ta sake tsayawa kan kafafunta kuma hakan ya sake busawa dimokuraɗiyya a rai.

INEC Tayi Watsi Da Buƙatar Masu Yiwa PDP Zagon Kasa, Ta Tabbatar Da Damagun a Matsayin Shugaban Jam'iyyar Daga Jimoh Ism...
19/11/2025

INEC Tayi Watsi Da Buƙatar Masu Yiwa PDP Zagon Kasa, Ta Tabbatar Da Damagun a Matsayin Shugaban Jam'iyyar

Daga Jimoh Isma'il Adetunji

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da cewa Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya na ƙasa Kabiru Tanimu Turaki (SAN) ita ce hukuma ɗaya tilo da ta dace a doka.

INEC ta ƙi yarda da takardar bogi da wasu korarru Mohammed Abdulrahman da Samuel Anyanwu s**a aika suna kiran a dage zaben fidda gwani na gwamnan Jihar Ekiti, matakin da ya fallasa yunƙurinsu na rugujewa jam’iyyar adawa ta ƙasa ta hanyar karya doka da son zuciya.

INEC ta jaddada cewa wannan takardar da waɗannan haramtattun shugabanni s**a turo a ranar 6 ga Nuwamba, 2025, ba ta da wani inganci. Su kansu sun yi ikirarin shugabanci ne bisa ƙarya, inda s**a jingina dalilan karya na wai “matsalolin shirye-shirye” domin su kawo tangarda ga zaɓen ranar 8 ga Nuwamba.

Hukumar ta bayyana a fili cewa kawai sa hannun shugaban jam’iyya na ƙasa da sakataren ƙasa na halastattaccen NWC ne ake karɓa a hukumance.

Matakin INEC ya yi daidai da hukuncin da jam’iyyar PDP ta yanke tun farko na dakatar da Anyanwu, Abdulrahman da wasu abokan aikinsu a ranar 1 ga Nuwamba, 2025 saboda aikata laifukan karya tsarin jam’iyya, wanda ya sabawa sassan 57(3), 58(1)(a)(b)(c)(h), da 59(1) na kundin tsarin PDP (2017 da aka gyara).

Wadannan hukunci an tabbatar da su ne a babban taron jam’iyyar da aka yi a Ibadan a ranar 15 ga Nuwamba, 2025, inda aka zaɓi Barrister Tanimu Turaki a matsayin sabon shugaban jam’iyya na ƙasa, tare da tsige manyan masu tada fitina ciki har da Anyanwu, Abdulrahman, Nyesom Wike da Ayo Fayose saboda aikata manyan laifuka na tafka ayyukan adawa da jam’iyyar, ƙirƙiro bangarori, da amfani da kotu wajen rugujewa jam’iyya.

DA DUMI-DUMI: Jam'iyyar APC ta jihar Zamfara karkashin ministan tsaro Dr Bello Matawalle da Sanata Abdul'aziz Yari, sun ...
14/11/2025

DA DUMI-DUMI: Jam'iyyar APC ta jihar Zamfara karkashin ministan tsaro Dr Bello Matawalle da Sanata Abdul'aziz Yari, sun goyi bayan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027, inda dubunnan yayan jam'iyyar s**a yi cikar kwari a wurin taron da Dr Bello Matawalle ya jagoranta yau Jumma'a a jihar Zamfara.

Daga Al'Mansoor Gusau

Wike Na Kawo Barazana Ga Demokradiyyar Najeriya – Ƙungiyar Nigeria Unite Ta Gargadi EUƘungiyar Nigeria Unite ta aika wa ...
14/11/2025

Wike Na Kawo Barazana Ga Demokradiyyar Najeriya – Ƙungiyar Nigeria Unite Ta Gargadi EU

Ƙungiyar Nigeria Unite ta aika wa ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) da wasika mai zafi, tana zargin Ministan Abuja, Nyesom Wike, da haifar da barazana ga dimokiraɗiyar Najeriya ta hanyar murkushe ‘yan adawa da goyon bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin tabbatar da wa’adi na biyu ba tare da hamayya ba.

Ƙungiyar ta ce bayan rugujewar dimokiraɗiya a Mali, Burkina Faso da Nijar, yanzu haka Najeriya ma na kan layin tangal-tangal, saboda irin matakan zaluntar ‘yan adawa da kuma amfani da cin hanci wajen tilasta sauya sheƙa.

Ta gargadi cewar idan ba a dauki mataki ba, lamarin zai iya jefa Najeriya cikin rikici, ya kawo bacewar tsaro a yankin Sahel, tare da tura miliyoyin ‘yan Najeriya zuwa Turai da Amurka a matsayin ‘yan gudun hijira.

Nigeria Unite ta kuma bukaci EU, AU, Amurka da Birtaniya su sanya takunkumi kan Wike da dakatar da shi daga tafiye-tafiye, tare da daukar mataki kan wasu manyan alkalan ƙasar, kwamishinan ‘yan sanda Abuja da hukumar INEC, domin cewar suna sabawa dokokin siyasa da na aikinsu.

Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara da ya gabata 2019-2023 kuma Ministan ‘Kasa a Ma’aikatar Tsaro, (Dr.) Bello Muhammad Mata...
13/11/2025

Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara da ya gabata 2019-2023 kuma Ministan ‘Kasa a Ma’aikatar Tsaro, (Dr.) Bello Muhammad Matawalle,MON (Barden ‘Kasar Hausa), tare da tawagarsa, sun sauka filin saukar Jiragen sama na Kwalejin Koyon Tukin Jirgin sama dake garin Zaria a jihar Kaduna a hanyarsu ta zuwa gida jihar Zamfara, domin ganawa da masoya da magoya bayan jam’iyyar APC.

Daga Al’mansoor Gusau

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHIR RAJI'UN Masu wannan mashin din sunyi accident a hanyar Bojude sun taso daga Gombe za suje G...
10/11/2025

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHIR RAJI'UN

Masu wannan mashin din sunyi accident a hanyar Bojude sun taso daga Gombe za suje Gona kuma duka Allah ya musu rasuwa, babu yadda za'a gane su.

Duk wanda ya gane lambar mashin din ya gaggauta sanarwa ga 'yan uwansu. Yanzu haka suna nan a kan hanyar Bojude gaba da Tashar Tappi.

A taimaka da Sharing, ko Allah zaisa agane 'yan uwansu.

Daga Abba Sani Pantami

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Trust News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share