25/05/2025
Matsalar Rashin Tsaro a Jihar Sokoto
Jihar Sokoto na fama da matsalolin tsaro musamman a yankunan karkara. Ayyukan 'yan bindiga sun addabi al'umma, inda ake kai hare-hare, sace mutane, da kashe-kashe ba tare da kakkautawa ba. Haka kuma, akwai matsalar garkuwa da mutane a hanyoyi da kauyuka, lamarin da ke jefa jama'a cikin fargaba da rayuwa cikin tsoro.
Barayin shanu da masu hari a daji na cin karensu babu babbaka, suna hana manoma fita gona da makiyaya fita kiwo. Wannan ya shafi tattalin arzikin kauyuka da noma gaba daya. Sakamakon haka, dubban mutane sun bar gidajensu, suna zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira (IDPs) da ke cike da kalubale.
---
Matakan Da Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Dauka
Gwamnatin jihar ta hada kai da jami’an tsaro don shawo kan matsalolin tsaro. Ana kara tura jami’an tsaro zuwa yankunan da ake fama da rikici tare da samar musu da kayan aiki da motocin sintiri.
An kuma dauki mataki na bayar da tallafi ga 'yan gudun hijira ta hanyar abinci, matsuguni da kula da lafiyarsu. Haka nan ana yunkurin samar da tsaro domin su koma garuruwansu idan al’amura s**a daidaita.
Gwamnati na shirin kafa rundunar matasa masu sa ido da tsaro a al’umma karkashin tsarin hadin gwiwa da jami’an tsaro. Hakanan, ana tattaunawa da sarakunan gargajiya da malamai don samun hadin kai wajen inganta zaman lafiya da wayar da kai.
A wasu lokuta, gwamnati ta saka dokar hana fita ko hana amfani da babura a wasu yankuna domin dakile matsalolin tsaro da kuma takaita motsin masu laifi.