17/04/2025
“Samaru da Kewayenta: Garuruwa masu Albarka na neman sauyawa!”
Samaru, Bomo, Basawa dama Jama'a garuruwa ne da Allah ya albarkace su da manyan mutane masu fada aji — tun daga malamai, sarakuna, 'yan siyasa, sojoji, da 'yan sanda. Garuruwan da s**a haifi jagorori da shugabanni da dama a tarihin wannan ƙasa. Amma abin takaici, yau garuruwan suna cikin wani hali na gurbacewar tarbiyya musamman ga matasa da yara ƙanana.
Shaye-shaye, sata, sara s**a, da karuwanci sun zama ruwan dare a tsakanin matasa da mata ‘yan yara. Wannan ba shine mahaifanmu da muka sani ba! Wannan ba shine cigaba da ake fata ba!
Muna kira ga shugabanninmu — masu mulki, sarakuna, malamai, da iyaye — da su tashi tsaye domin ceto al'ummar mu daga wannan halin. Wannan ba al’amari ne da za a yi shiru akai ba.
Tarbiyya gida take farawa, amma gyara na bukatar hadin kai.
Duk shugaban da ya shirya yakar wannan gurbacewar tarbiyyar to muna tare dashi ba tareda nuna wani bangaranci na addini ko na siyasa ba.
Allah ya tsare garuruwanmu, Allah ya tsare matasanmu.
God bless Samaru, Bomo, Basawa and Jama'a wards.
God bless Basawa Constituency.
God bless Sabon Gari L.G.A.
God bless Kaduna State.
God bless Federal Republic of Nigeria.