02/09/2025
Gwamnatin Tarayya Ta Yaba wa Ƙasar Finland Kan Hukuncin Daurin Shekaru Shida da Aka Yankewa Simon Ekpa Ɗan Ƙungiyar Biafra
Gwamnatin Tarayya ta yi maraba da hukuncin da Kotun Gundumar Päijät-Häme da ke ƙasar Finland ta yanke a ranar Litinin, inda ta ɗaure Simon Ekpa, wanda ya bayyana kansa a matsayin mai rajin Biafra, shekaru shida a gidan yari bisa laifukan ta’addanci.
A cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa hukuncin ya kasance babbar nasara ga Najeriya da kuma al’ummarta da aka dade ana zalunta ta hanyar ayyukan ta’addanci da Ekpa da abokan aikinsa s**a haddasa. Ya ce hukuncin na da muhimmanci ƙwarai wajen ƙarfafa dangantakar Najeriya da Finland.
“Shekaru da dama, kiran tayar da tarzoma da shirya tashin hankali da Simon Ekpa ya yi ta hannun ayyukan ta’addancin IPOB sun haddasa bakin ciki da ba za a misalta ba. Iyalan mutane sun tarwatse, kasuwanci ya rushe, yara sun zama marayu, al’ummomi kuwa sun kasance cikin tsoro. An rasa rayuka da dama, wasu kuma sun ji raunuka sakamakon bin wata manufa ta karya da ta yi ƙoƙarin lalata zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da ikon mulkin Najeriya,” in ji Ministan.
Ya ƙara da cewa hukuncin da kotun Finland ta yanke ya tabbatar da matsayin Najeriya tun da farko, tare da aika saƙo a fili ga masu tsattsauran ra’ayi a duniya cewa idon duniya na kansu, kuma shari’a za ta cimma duk wanda ya nemi tayar da hankali ta hanyar ta’addanci.
Ministan ya nanata cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nan daram wajen kare ikon mulkin Najeriya da mutuncin kowane ɗan ƙasa, tare da ci gaba da amfani da dukkan kayan hanyoyin diflomasiyya, soja, shari’a da sauran su – domin kiyaye zaman lafiya, haɗin kai da iyakokin ƙasa.
Haka kuma, gwamnatin ta yi kira ga duk masu bin sawun Simon Ekpa da sauran abokan aikinsa da su ajiye makamai su rungumi zaman lafiya. “Najeriya ƙasa ce mai faɗi da za ta iya ɗaukar kowa, amma babu ci gaba a inda tashin hankali da rarrabuwar kawuna ke faruwa,” in ji Ministan.
A ƙarshe, Gwamnatin Tarayya ta yaba da jajircewa da sadaukarwar Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, Rundunar Sojin Najeriya, hukumomin tsaro da leƙen asiri, Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya da Rundunar ‘Yan Sanda, bisa gudummawarsu wajen tabbatar da tsaron ƙasa duk da ƙalubalen da ake fuskanta.