05/06/2026
Akpabio Ya Yabawa Shugabannin NILDS Kan Cika Nauyin Da Aka Dora Musu
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, a ranar Alhamis ya yaba wa shugabannin Cibiyar Nazarin Dokoki da Dimokuraɗiyya ta Ƙasa (NILDS) bisa yadda suke cika manufofi da ayyukan da aka kafa cibiyar domin aiwatarwa.
Akpabio ya musamman yabawa Darakta Janar na cibiyar, Farfesa Abubakar Suleiman, da tawagarsa ta gudanarwa bisa, kamar yadda ya ce, “sanya ya zama mai yiwuwa gare mu mu samu kwasa-kwasan sabunta ilimi da ƙwarewa.”
Akpabio, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Gudanarwa na cibiyar, ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar taron kwamitin a hedikwatar NILDS da ke kan titin Filin Jirgin Sama an Abuja.
Taron ya samu halartar Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Gudanarwar.
Akpabio ya shaida wa kwamitin cewa, “manufar kafa wannan cibiya tana ci gaba da tabbata,” yana mai nuni da shirye-shiryen karatu da NILDS ke gudanarwa ga ɗaliban digiri na biyu har zuwa matakin digirin digirgir (PhD), tare da haɗin gwiwar wasu jami’o’i a ƙasar.
Ya nuna farin cikinsa da jin cewa NILDS ta fara horas da ma’aikatan Majalisar Dokoki ta Ƙasa, sannan ya ba da shawarar a bai wa cibiyar alhakin gudanar da kwas ɗin gabatarwa ga sabbin sanatoci da mambobin Majalisar Wakilai da za a zaɓa.
Ya ce:
“Lokacin da muka zo a shekarar 2023, an gudanar da kwas ɗin gabatarwarmu a Cibiyar NAF. Na yi imanin cewa ga sabbin sanatoci da mambobin majalisa da za a zaɓa, wannan wuri ya dace sosai domin gudanar da irin wannan shiri ga sabuwar majalisa.
“Ina roƙon mambobin majalisar gudanarwa su yi la’akari da yanke hukunci a wannan fanni. Bayan kammala zaɓen shekarar 2027, ya kamata a gudanar da kwas ɗin gabatarwar a nan. Hakan zai ƙara jawo hankali ga wannan wuri tare da ƙara ɗaukaka martabar cibiyar.”
Shugaban Majalisar Dattawar ya kuma yaba wa shugabannin NILDS bisa kyakkyawan kula da ginin hedikwatar cibiyar.
Ya ce:
“Lokacin da na zo nan, na matuƙar gamsu da yadda aka kula da wannan katafaren gini. Kula da irin wannan gini ba abu ne mai sauƙi ba. Kai da tawagarka ta gudanarwa, Farfesa Suleiman, ina ganin kun yi aiki mai kyau ƙwarai.”
Tun da farko a farkon taron, Farfesa Suleiman ya yi wa kwamitin bayani kan ci gaban da cibiyar ta samu.
Ya ce babban aikin cibiyar shi ne ƙara wa ‘yan majalisun Najeriya ƙwarewa da ilimi, a matakin tarayya da na jihohi, har ma da yankin yammacin Afirka.
Farfesa Suleiman ya bayyana cewa yanzu NILDS tana da sassa 12, ciki har da gidan rediyo, kuma tana aiki tare da cibiyoyi da jami’o’i da dama, ciki har da Jami’ar Benin, Jami’ar Abuja da Jami’ar Tarayya ta Lokoja.