
28/03/2021
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN.
'Yan Bindiga Sun Masa Kisan Gilla a Gaban Matansa da 'Ya'Yan Sa a Cikin Garin Sokoto Cikin Daren Jiya.
wasu 'yan bindiga dauke da munanan bindigogi sun Afka Unguwar Gidan Bahure dake tsakiyar birnin sokoto inda s**a shiga gidan Alh. Mustapha (Sarkin Albasa) s**a masa kisan gilla ta hanyar halbeshi da bindiga a gaban matansa da kuma 'ya'yan sa.
'Yan Bindigar dai, sun Afka gidan margayin ne da misalin karfe 3 na daren jiya inda s**a dinga halbe-halbe har s**a kutsa kai cikin gidan sa daga bisani s**a halbeshi har lahira.
Alh. Mustapha (Sarkin Albasa) Babban dan kasuwa ne mai sana'ar sayar da Albasa a birnin sokoto, ya rasu yanada shekaru 40 a duniya.
Haka kuma, margayin ya bar mata biyu da 'ya'ya fiye da goma a duniya.
Tuni da sanyin safiyar yau lahadi aka yi zana'izar sa kamar yadda Addinin Allah ya Tanada.
Allah Gafartamasa, Ya Kuma Kyautata Makwanciyar sa, Allah Ya Kawomana Zaman Lafiya Amin.
Jaridar Sokoto