
12/07/2025
DA ƊUMI–ƊUMI:— Jawabin Mai Girma Barden Yamma dangane da kiran da kungiyar New Breads Manifestation and Awareness Forum tayi masa:
"Da farko muna mika godiya tamusamman ga wonnan kungiyar da irin soyayar da s**a nuna mana. Ina mai kara mika godiya ga ɗaukacin Al'umma da irin soyayyar da suke nuna mana a dukkanin bangarori na kaitsaye ko a kaikaice."
"Ina mai sanar da Al'ummar mu cewar, SIYASA A YENZU BA TAMU BACE amma faɗa tamu, cikawa ta Ubangiji, muna iya tarar ta a gaba tunda dai bamusan iya inda ƙaddara mahaliccin mu zata kaimu ba. Bugu da ƙari kuma anan, duk wonda Al'ummah s**a aminta dashi har s**a ɗaukomana shi sannan muka yedda da ɗabi'un sa, tabbas zamu mara masa baya sannan zamu bashi gudunmowa ɗari—bisa—ɗari (100%)"
"Daga karshe, mu, muna bada gudunmawa ne kaso mai karfi a fanni ilimi da ilmantarwa, muna da makaranti a sassa daban² a faɗin Jahar Bauchi, musamman a Karamar Hukumar mu ta Toro. Zamuci gaba da wonnan aiki domin ilmantar da Al'umma dakuma samawa matasan mu ayyukan yi daidai abinda Allah ya nufa zamu iya. A karkashin wonnan, ina mai tabbatar da scholarship na ɗalibi/ɗaliba ɗaya wa wonnan ƙungiya a ɗaya daga cikin makarantin mu"
"Ina yiwa kowa fatan Alkhairi, tun daga kan sarakunan mu iyayen ƙasa, jagororin mu a Addini, Jagororin mu a siyasa, ƴanuwana Matasa da mata iyayen mu a ko ina suke, Allah ya fimu yabawa da irin goyon bayan da kuke nuna mana."
Naku
Alh. Musa Salihu Eggi
Barden Yamman Toro na Farko
Wazirin Doka
Chirman NAPPS
Director/Proprietor Al-Iklas
President Al-Iklas Group of Schools
C.E.O Al-Iklas Foundation
✍️
Comr. Anas Usman Tilde
Media Aid