23/08/2021
ZUWA GA Dr. JALO JALINGO, AKAN BATUN TAUYE ALFARMAR KHUSUSIYAR MANZANNI.
Duk zantukan da ya fadi a game kalubalantar "Ismar" ANNABAWA ya ciro su ne cikin littafin Majmu'al Fatawa na Sheikh Ahmad Ibnu Taimiyyah duk da yayi kokarin boye hakan.
Kamar zancensa da ya baiwa lamba na biyu cewa.
2. Tabbatacciyar Ismar da Annabawa da Manzanni ke da ita ita ce Isma cikin isar da sakon Allah Madaukakin Sarki kawai.
Sheikh Ibnu Taimiyyah Yace" yace zancen cewa ANNABAWA an kare su daga aikata manyan zunubai (Kaba'irai) amma ba'a katange su daga aikata kananan zunubai ba (Saga'ir), yace hakan shine fahimtar akasarin Malaman Musulunci, na Tafsiri, Hadisi, da kuma Faqihai, babu wani abu da aka ruwaito daga wani magabaci (Salaf) kamar imamai, Sahabbai, ko kuma tabi'ai ko kuma halifofi da dayansu bai amince da wannan fahimta ba (Majmaa’ al-Fataawaa, 4/319).
Sannan zancen Malamin mai lamba na 3 , 4, 6 da 7 suma duk ya fitar dasu ne kamar haka.
3. Sam ba aibi ba ne ga Annabawa da Manzanni su yi mantuwa ko su yi kure cikin wani Ijtihadi da s**a yi.
4. Allah Madaukakin Sarki ba ya tabbatar da Annabawa da Manzanni a kan kure da s**a yi, a’a da sun yi kuren to nan da nan zai gyara musu kuren nasu.
6. Ayoyin Alkur’ani masu yawan gaske ne da suke tabbatar da cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah yana iya yin mantuwa, kuma yana iya yin kure.
7. Lalle aqidar cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ba zai yiwu ba a ce ya yi kure, haka nan ba zai yiwu ba a ce ya yi mantuwa, Aqida ce ta batattun ‘yan bidi’ah. Allah Ya tsare mu. Ameen.
Shima ya ciro su ne a wannan littafi, inda Sheikh Ibnu Taimiyyah yake cewa :
Mafi yawa daga ruwayoyi, daga Ijma'in Malamai sun bayyana cewa ANNABAWA ba ma'asumai bane game da aikata kananan kusakurai, sai dai ba'a basu damar zarcewa a cikin aikatasu, kuma ba su ce hakan bazai taba faruwa ba har abada, bayanan farko shine "su dukkan su ma'asumaine hakan yazo ne daga Rafidawa, wadanda suke cewa dukkan ANNABAWA ma'asumai ne basu taba aikata wani kuskure ko da ta hanyar mantuwane, ko kuma rashin fahimta. (Majmu’ al-Fataawaa, 4/320).
Shehin Malamin ya kara da cewa "Ayar da take bayyana Annabtar ANNABAWA, kuma take bayyana cewa su ma'asumaine cikin sha'anin isar da sako daga ALLAH, to abinda s**a fadi shine kawai yake na gaskiya, wannan shine ma'anar ANNABTA, wanda ke nufin ALLAH na gaya musu wani abu na gaibu su kuma sai su gayawa mutane, kuma shi Manzo akan umarceshi da ya kira mutane zuwa ga ALLAH, kuma ya isar da sakon ubanginjinsa.
(Majmu’ al-Fataawaa, 18/7).
Duk da Shi Dr. Jalo bai kawo ba, amma wasu daga ababen da s**a rika a matsayin hujjarsu ta cewa ANNABAWA na yin kuskure sune:-
An ruwaito daga Raafi' Ibn Khudaij yace "MANZON ALLAH (S.A.W) yazo birnin Madina, su kuma sun kasance suna yiwa dabinai wasu dabaru na samun yabanya, sai yace dasu " me kukeyi haka? Sai s**a bashi amsa da cewa "ko da yaushe s**an yi masa wannan abin, sai yace dasu " amma da zaku daina yin hakan da yafi alkairi, sai s**a dena yi, sai ya zamo sun samu tawaya cikin abinda s**a saba samu, sai s**a sanar dashi abinda ya faru, sai yace dasu " ni kawai mutum ne kamarku, idan nayi muku umarni cikin abinda ya shafi Addini, to ku bi, amma idan na gaya muku wani abu akan sha'anin duniyarku to ku auna ku gani,......!."( Muslim, 2361)
Sannan da wasu daga kissoshi da s**a zo cikin Al-kur'ani kamar .
Ayayin da Kabeel ya kashe Habeel, da lokacin da Mala'iku biyu s**a zo ga ANNABI Dauda ya saurari dayan, amma bai saurari dayan ba, da kissar ANNABI YUNUS (A.S) sadda kifi ya hadiyeshi, da kuma abinda yazo daga Surar Abasa aya ta 1-2. da kuma abinda ya faru na cin itaciyar da ALLAH ya hani ANNABI ADAM(A.S) da ci.
Sai Malamin ya kawo cewa...!
5. Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 401, da Muslim na 572 daga Abdullahi Bin Mas’ud Allah Ya kara masa yarda ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: انما انا بشر مثلكم انسى كما تنسون فاذا نسيت فذكروني Ma’ana: ((Ni mutum ne irinku ina mantuwa kamar yadda kuke mantuwa, idan na manta ku tunatar da ni)). Bukhariy ya ruwaito hadithi na 6398, da Muslim na 2719 daga Abu Musal Ash’ariy Allah ya kara masa yarda ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya kasance yana rokon Allah da wannan addu’a: اللهم اغفرلي خطيئتي Ma’ana: ((Ya Ubangijina Ka gafarta mini kuskurena)). Ahmad ya ruwaito hadithi na 19,925, da Bazzar na 3,525, da Tabaraniy na 242 daga Imran Bin Husain Allah Ya kara masa yarda ya ce: ya kasance daga cikin addu’ar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah cewa: اللهم اغفرلي ما اخطات Ma’ana: ((Ya Ubangijina Ka gafarta mini abin da na yi kuren shi)).
WAR-WARA.
1- Idan muka tambayi Mallam, shin wannan abu da yakeson karantarwa, wacce Maslahace cikinta da idan mabiya s**ayi riko da ita zata zame musu silar kyautata makomarsu ta lahira shin wacce amsa zai bamu...?
2- Malamin ya kamata ya sani cewa "Lallai rayuwar ANNABAWA Misaline ga Al'ummar Zamaninsu, sam basu kuskure, sai dai ALLAH ya kaddara musu aikata wani abin da silarsa zai fitar da wata hukunci ga al'umma, ko aikata wani abin da zai zamo silar samun wani sauki ko rahama ga Al'ummarsu, idan kuma suna kuskure sai ya gaya mana hukuncin Kuskurensu a wajen ALLAH.
Domin ALLAH yana fadi a hakkin MANZON ALLAH (S.A.W) Suratu Taubat Aya ta 128
لَقَدْ جَآءَكُمْ رَسُولٌ مِنْ أَنْفُسِكُمْ عَزِيزٌ عَلَيْهِ مَا عَنِتُّمْ حَرِيصٌ عَلَيْكُمْ بِالْمُؤْمِنِينَ رَءُوفٌ رَحِيمٌ
3- Kaddarama ANNABAWAN na yin kuskure, ai kai ba hurumin ka bane tattaunawa akai, domin ko kai mahaifinka na da hurumin bayyana kuskuren mahaifiyarka, amma kai ai baka da hurumin bayyana kuskurenta idan kayi hakan kayi mata rashin kunya da rashin ladabi, haka zalika hurumi ne da ya kadaita da ALLAH shi kadai yayi zance cikin sha'anin MANZONNIN SA dashi, ba dan hakan ya zamo abin tattaunawa tsakanin mutane ba, sai dan mu fahimci wata hikim dake cikin hakan.
4 Ya kamata Malamin ya fahimci hadisan da ANNABI (S.A.W) yake zance a babi na Zuhudu, Da Tawadi'u, kamar fadinsa
-KADA KU GIRMAMANI SAMA DA YUNUSA BIN MATTA, KO ISA DAN MARYAMA DA SAURANSU, SUNE MISALIN HADISAN DA YA KAWO GAME DA KUSKURE KO MANTUWA DA YAKE NASABTAWA ANNABI (S.A.W) amma hakan sam baya nufin cewa "SHI BA ABIN GIRMAMAWA BANE SAMA DA SU DOMIN SHINE YACE SHINE SHUGABAN DUKAN 'YA'YAN ADAMU BA ALFAHARI BA" ". Amma me Malamin zaice akan wasu hadisan kuma da ANNABI (S.A.W) da kansa yake cewa "SHI BA MUTUM BANE KAMAR SAURAN MUTANE" ka duba hadisi na 182 a kitabus siyam cikin Sahihul Bukhari.
Sannan da Malamin ya lura, zai gane cewa ANNABI (S.A.W) ya wuce mukamin da duk yake zato, domin shi akansa ALLAH bai aje mizanin dai-dai da kuskure ba, duk abinda ya aikata dai-dai ne, ba mamaki shi yasa ayoyi kamar haka s**a sauka cikin fadin ALLAH.
Kamar fadinsa a sura ta 3 aya na 31
قُلْ إِن كُنتُمْ تُحِبُّونَ ٱللَّهَ فَٱتَّبِعُونِى يُحْبِبْكُمُ ٱللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَٱللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Da kuma fadinsa a Surata ta 4 aya na 80
مَّن يُطِعِ ٱلرَّسُولَ فَقَدْ أَطَاعَ ٱللَّهَ وَمَن تَوَلَّىٰ فَمَآ أَرْسَلْنَـٰكَ عَلَيْهِمْ حَفِيظًا
Lallai ya kamata Malamin yaje yayi Tafaqquri akan wadannan ayoyi, anan zai gane cewa "BIN ANNABI (S.A.W) CIKIN DUK ABINDA YA TA'ALLAKA DASHI, SHINE HAKIKAR BIN ALLAH" TO TAYAYA YAKE TUNANIN ANNABI (S.A.W) ZAI KUSKURE CIKIN ABINDA YA SHAFI RAYUWA, ALHALI BABU WANI ILMI DA ALLAH BAI BASHI SHI BA".
ME YASA KAFIRAN MAKKAH SUKE KIRANSHI DA SUNA AL'AMIN TUN KAFIN A AIKO SHI DA RISALA A ZAHIRI, HALA MU'AMALAR DA YAYI DASU ABUNE DA YA SHAFI WAHAYI, KO KUMA ABUNE DA YA SHAFI RAYUWA...?
Mai yiwuwa manufar Malamin so yake ya yaki wata daraja Khususiyya da ALLAH ya kebenceta ga ANNABI (S.A.W) wanda hakan kuma dama sanannen al'amarine game da Malamin da ya fito da zantukanshi daga gareshi.
ALLAH YA SHIRYA.
ALHAMDULILLAH.