Asset growth

Asset growth Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Asset growth, Media/News Company, .

*ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH*Muna farin cikin sanar da ɗaukacin Al'ummar Musulmi cewa insha Allahu daga yau litinin 3...
31/01/2022

*ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH*

Muna farin cikin sanar da ɗaukacin Al'ummar Musulmi cewa insha Allahu daga yau litinin 31/01/2022 za'a fara saka karatun Littafin Muwadda Malik na Dr Ahmad BUK (Rahimahullah) a Rahma Radio Dake Kano Insha Allahu.

Ranakun da za'a ke sakawa sune:

👉. Ranar Litinin-Juma´a Karfe 9:00 na dare

👉 Asabar da Lahadi 9:00 na safe bayan shirin Fatawoyin Rahma

Allah yasa mu amfana da abun da zamu Saurara.

Allah ya gafartawa malam yasa jannatul firdaus itace makomarsa Ameen.

05/03/2021

Wannan Tasha Ta Alheri Hausa Tv Zata Rika Kawo Muku Shirye Shirye Masu kayatarwa Da Nishadantarwa Da kuma ilmantarwa ...

Don't forget to fast tomorrow, is a day of Arafat.
29/07/2020

Don't forget to fast tomorrow, is a day of Arafat.

24/03/2020
Ya kamata hukumar BBC Hausa ta binciki ma'aikatanta!Imma dai akwai 'yan shi'a a BBC kuma suna anfani da BBC don yada shi...
06/08/2019

Ya kamata hukumar BBC Hausa ta binciki ma'aikatanta!

Imma dai akwai 'yan shi'a a BBC kuma suna anfani da BBC don yada shi'ancinsu ko suna gefe suna kitsa hakan, ko kuma rashin sanin makamar aiki ya fara yawa a BBC. Ko ma ya ne, hakan zai watsa suna da nagartar da BBCn ta gina tsawon shekara-da-shekaru.

A kwanaki can BBC ta yi labarin gidan yi wa hadisan Manzo SAW hidima na Saudiya a gurbatance, ta kwaso labarin da 'yan shi'a suke yadawa a kan Saudiyyan na qarya, ta tattauna da wani malami maqiyin Saudiyya kan Saudiyyar ta na yaye 'yan ta'adda ba tare da sun yi balancing ba.

A makon da ya gabata, s**a je Wikipedia su ka kwaso labarin da 'yan shi'a su ka qaga a na qarya wai Muhammad Yusuf ya yi karatu a Jami'ar Madina, alhalin qarya ne, ko a Wikipedia din ma ba source.

Yanzu kuma Kotu ta ba wa jagoran 'yan shi'a izinin zuwa Indiya don a duba tunbinsa da sauran sassan jikinsa da na matarsa, sai ga BBC sun buga labarin qarya wai mutanen Indiya sun fara maraba da Zakzakiy (https://www.bbc.com/hausa/labarai-49240955?ocid=wshausa.chat-apps.in-app-msg.whatsapp.trial.link1_.auin).

Abin takaici shi ne, wai fa madogarar BBC ita ce wani mutum daya jal dan shi'a, wai shi Hashmi, ya yi twitting cewa Indiya na maraba da Zakzakiy. Mutumin nan ba wani sananne bane, duka-duka fa a watan March din nan da ya wuce ne ya yi joining Twitter, followers dinsa 11 ne kacal, haka ma yawan "like" da aka yi wa labarin nasa, retwit 2 qwal, amma wai a kan haka ne har BBC za su buga dogon labarin cewa wai 'yan Indiya sun fara maraba da Zakzakiy.

Sannan a labarin sai s**a ce:

"Daya daga cikin sharuddan shi ne dole ne jami'an gwamnati su yi wa Zakzaky da matarsa rakiya zuwa Indiya."

Abin da za a fahimta anan shi ne kotun ta martaba Zakzakiy da matarsa don ta bada umarnin dole jami'an gwamnati su yi musu rakiya. Wannan ba gaskiya bane, domin kotun cewa ta yi:

"...under the strict supervision of the respondent and to return to Nigeria (for continuation of trial)"

Wato ta bada izini Zakzakiy ya je Indiya amma qarqashin sa idon qud-da-qud na Gwamnati kuma da ya gama dole ne ya dawo a dora daga inda aka tsaya. Gwargwadon umarnin na kotu fa in ma Zakzakiy ya dawo to za a garqame shi, ba wai ta bada belinsa bane.

Sannan sai BBC su ka shiga sharhin nuna kamar akwai wata alaqar qauna tsakanin Zakzakiy da Indiyawa amma duk sai su ka qare a labarin da Wikipedia ta wallafa, shi ma marar tushe. BBC ta ce:

"...kasar India na daya daga cikin kasashen da ba na Musulmi ba, amma masu yawan mabiya mazhabar Shi'a a duniya, inda bayanai s**a ce akwai 'yan Shi'a da dama a Musulman kasar."

Ga kuma rubutun Wikipedia:

"India, the only non-Muslim nation in the world with Shiite population of 2–3 percent of its entire population"

Don Allah wannan ba wanki bane kai tsaye? To shi kuma rubutun na Wikipedia ba shi da tushe, ga shi: https://en.m.wikipedia.org/wiki/Shia_Islam_in_India

To a hakan ma, ai Wikipedia cewa su ka yi 'yan shi'ar na Indiya 2-3% ne, kuma a hakan ba wai iya irin 'yan shi'ar Zakzakiy bane 2% din, a'a suna da yawa brijik ciki har da jama'ar su Shaikh Hamza Lawal da Saleh Zaria.

An yi qididdigar yawan jama'ar Indiya a karo na 15 a 2011, mutanen indiya 1,210,854,977 ne (http://www.census2011.co.in). Musulmi ne na biyu a yawa bayan addinin Hindu da kashi 14.2% (http://www.census2011.co.in/religion.php)

Ida ka ja lissafi, mutum 1,210,854,977 ÷ 100 x 14.2 zai baka kusan Musulmi 169,761,868 a Indiya. Su kuma 'yan shi'ar, idan ma an yarda da lissafin na Wikipedia, shin 2% na jama'ar qasar har ya kai adadin da zuwan Zakzakiy zai zama wani batun tattaunawa?

Gaskiya ban ga abin da BBC za su fada na gamsu ba shi'anci su ke tallatawa ba. Sun dora BBC a tafarkin watsa ta. Muna kira, kuma za mu bi matakan hurawa hukumar BBC wuta don ta gaggauta bincika lamarin nan ta dauki matakan da su ka kamata.

Allah ya kyauta.

*BBC HAUSA: GANGANCI KO RASHIN KWAREWA?*✒ Mansur Sokoto30 ga July, 2019Akwai mamaki matuka irin yadda tashar BBC Hausa R...
30/07/2019

*BBC HAUSA: GANGANCI KO RASHIN KWAREWA?*
✒ Mansur Sokoto
30 ga July, 2019

Akwai mamaki matuka irin yadda tashar BBC Hausa Radio ta wallafa tarihin jagoran Boko Haram Muhammad Yusuf jiya a shafinta, bayan ya cika shekaru 10 da mutuwa tare da alakanta shi da Jami'ar Musulunci ta Madina.
Wannan ba zai yiwu ya zama kuskure ba. Musamman in muka yi la'akari da yadda a cikin rahoton s**a yi biris da kasancewarsa jagoran Zakzakiyya na jihar Yobe kafin ya rungumi kungiyar Tajdid, sannan ya sauya sheka daga baya zuwa abinda aka kira Salafiyya, da kuma yadda BBCn s**a fito da sunan Ibnu Taimiyyah baro baro a matsayin wanda Muhammad Yusuf yake da'awar koyi da shi. Amma abin tambaya shi ne: Don wace manufa s**a yi haka?
To, ko don mine ne dai muna sanar da su cewa, al'ummar kasar Hausa ta ga alheran wadanda wannan Jami'a mai albarka ta yaye a tsawon kusan shekaru 60 da ta yi tana hidimar karantar da yayan Musulmin duniya sahihin karatun addinin Musulunci kyauta. Kuma _alhamdu lillahi_ ba a san dan ta'adda ko daya wanda ita wannan Jami'ar ce ta kyankyashe shi ba. Muhammad Yusuf kuma ko bangon Jami'ar bai taba gani ba.
Makaryaci ba ya zama gwani kowane ne.

27/06/2019

FARFESA A GIDAN MIJINTA :

Idan aka tambayi matar aure menene aikinta ? Sai tace zaune nake ba aiki!!!

Damuwa bayyane a fuskarta koda ko tana yin wata sana'ar cikin gida .

Ashe ba ke bace mai kula da kayan mijinki ?
Lura da tarbiyyar yara da lafiyarsu;
Tattali da kasafi;
Shirya abinci da tsaftace muhalli;
Kare mutuncin mijinki dana 'ya'yanki?

Ashe wannan ba aiki bane?!!.

Wallahi duk mata da ta tsare wannan kuma ta kiyaye ibadarta da yin biyayya ga mijinta lallai ne itace me kololuwar shedar digirgir wadda batada sakamako sai aljannah!!!.

Duk mizanin da mace zata hau muddin ya sabawa shari'a to zakaga ba abinda yake kara mata sai koma baya da rikicewar lamurranta.

Ya Allah ka nusar da mata su gane 'yancin shegantakar da ake ikirarin samar musu hanyace ta rabasu da Allah da Manzonsa , ana tunbukesu daga rayuwar mutunci su watsar da 'ya'yansu su fita titina da ma'aikatu suna gwagwarmaya da maza ba tare da wani dalili na shari'a ba.

Wallahi musulunci shine addinin da ya kwatowa mace cikakkaken 'yancinta ya lazimtawa namiji kula da ita ta hanyar dora masa wasu hakkoka wadda a da bata dasu.

Fifikon yaudara ne ake nuna muku dan ku rike fita a rika saukin samunku a sanga!!

Ya Allah ka karemata shiga wadannan tarkuna na Shaidanu, ka ganar dasu gakiya, duk masu kokarin sauya tunanin mace a kan fidirar da Allah ya halicceta akai kayi mana maganinsa , ya Allah mun barsu da kai.

Daga: Fatima Aliyu

Abubuwa 15 Gameda Shugaba Muhammad Mursi..1- An haifi Mursi a jihar Sharqiyya a Masar a shekarar 1951 ya rasu 2019 (shek...
18/06/2019

Abubuwa 15 Gameda Shugaba Muhammad Mursi..

1- An haifi Mursi a jihar Sharqiyya a Masar a shekarar 1951 ya rasu 2019 (shekaru 68). Ya na da mata daya da 'ya'ya biyar, maza hudu mace daya.

2- yayi digiri na farko a fannin Engineering a shekarar (1975), da na biyu a shekarar (1978) a kan Metals Engineering duk a Jami'ar Alkahira (Cairo University).

3- Ya tafi Amurka inda ya yi digirinsa na uku a Jami'ar (Southern California University) a shekarar 1982, inda ya karantar a Jami'ar har zuwa shekarar 1985

4- Bayan dawowarsa ya karantar a Jami'ar Zaqaziq a Masar daga shekarar 1985 zuwa 2010. , inda ya rike bangaren (Materials Engineering) a Jami'ar.

5- Ya shiga cikin kungiyar 'Yan'uwa Musulmi a shekarar 1977 inda ya rike makamai da dama a cikin kungiyar.

6- Mursi ya cigaba da gwagwarmayar siyasa, inda ya yi takara lokuta da dama a matakin majalisa ta kasa. ya zama dan majalisa a shekarar 2000.

7- Kungiyarsa ta 'Yan'uwa Musulmi ta tsaida shi a matsayin dan takarar matakin shugaban kasa, inda aka kara tsakanin manyan yan takara guda biyar a kasar bayan boren da ya yi awon gaba da shugaba Muhammad Husni Mubarak a shekarar 2011

8- Mursi ya ci nasarar zama shugaban kasa na farko bayan lashe zaben da ya yi da kashi 52% a kan babban abokin hamayyarsa Ahmad Shafiq a shekarar 2012 , a zaben da ya zamto mafi tsafta a tarihin Masar.

9- Ministan tsaron da ya nada Abdulfattah al-Sisi ya yi awon gaba da shi bayan zanga-zangar da 'yan adawa da shi musamman (secularists) su ka yi akan dole ya sauka ya shirya wani zaben cikin gaugawa su na masu zarginsa da kokarin cusa musulunci a tsarin gwamnatinsa da karawa Kansa karfin iko.

10- Sisi wanda ya samu cikakken goyon baya daga wadansu daga cikin gwamnatocin kasashen waje na larabawa da da Isra'ila ya yi amfani da damar wajen shirya juyin mulki ga shugaba Mursi a shekarar 2013

11- Magoya bayan Mursi sun cigaba da gudanar da zanga-zangar lumana ta nuna rashin amincewarsu da juyin mulkin da Sisi ya yi wa zababben shugabansu, kuma ya ke cigaba da tsare shi, tareda wadansu dubban magoya bayansa, da kashe wasu, da tilastawa da dama daga cikinsu yin gudun hijira zuwa kasashen ketare. Sisi ya aiwatar da kisan kiyashi ga magoya bayan Mursi, wanda mafi muni shine kisan da sojoji su ka yi wa magoya bayan Mursi mutum 2000+ da su ka taru su ka yi zaman dirshen a dandalin Rabia da ke Nasr city a cikin birnin Alkahira.

12- A shekara daya da yayi yana mulki, Mursi ya samu kauna ta ban mamaki daga al'ummar larabawa da sauran musulman duniya, wanda su ke ma kallon jagoran da zai dawo musu da kimarsu a duniya, musamman yanda ya ke nuna damuwarshi da al'ummar musulmi da yadda ya ke nuna goyon bayan shi ga mutanen Palastinu da Zirin Gaza.

13- A daya daga cikin zqman da aka yi bayan gabatar da shi a kotu, Mursi ya bayyanawa kotu cewa rayuwarshi na cikin hatsari, amma ba a dau wani mataki ba.

14- Gidan talabijin din Masar ya sanar a ranar litinin 17/6/2019 cewa Mursi ya rasu a kotu yayin da ake masa shari'a , amma wasu na ganin wannan shiri ne kawai na boye hakikanin dalilin rasuwarshi, musamman da ya ke an hanashi magani a kurkuku.

15- Dr. Muhammad Mursi cikakken mahaddaci Alkur'ani ne mai kishin addininsa da al'ummarsa, wanda ke kokarin baiwa al'ummarsa da addinin sa kariya duk inda ya samu kansa kuma ya Samu dama.

Muhammad Mursi daya ne daga cikin miliyoyin musulmai a duniya da ke gwagwarmayar dawowa al'umma da karfinta da izzarta ta kowane bangare, kuma su ke bada jinanensu a matsayin farashin wannan aiki, kuma ba za su taba juya baya ba har sai hasken Allah ya cika.

Allahu Akbar Allah ya yi gaskiya:

"من المؤمنين رجال صدقوا ما عاهدوا الله عليه فمنهم من قضى نحبه ومنهم من ينتظر وما بدلوا تبديلا"

Mu na yi wa al'ummar musulmin duniya ta'aziyya na rasuwar wannan babban gwarzo wanda ya bada rayuwarsa domin hidimtawa al'ummarsa da addininsa. Ya Allah ka jikansa ka gafarta masa ka karbi shahadarsa ka sanya jininsa ya zamto la'ana ga makasansa.

Umar Mansur
[email protected]
17/6/2019

22/11/2018

ILIMI shine d'aya-d'ayan abunda yafi komai daga darajar dan-adam sama da komai, kamar yadda da ilimi Ubangiji ya fifita farkon mutum (Adam A.S) akan bayinSa tsarkaka (Mala'iku),
Da ilimi da kwakwalwa me tunani ubangiji ya fifita Ya kuma jagorantar da Dan-Adam abanQasa, wannan yasa ilimi ya zama jigo na Samar da duk wani ci-gaba adoron wannan duniya. Da ilimi ake yin zarra a tsakanin tsaraiku, da ilimi ake amfanan al-umma, da ilimi ake sanin hanyar kawo ci-gaba, kamar yadda da ilimi ake sanin matsala sannan ta hanyarshi ake kawo gyara.
Me ilimi acikin al'umma shine wayeyye kuma me amfanan mutane, kamar yadda jahili acikin al'umma yake liability kuma maras amfani. Tarihi ya nuna duniya bata taba amfanuwa da jahilcin jahilai ba acikin ko wani bangare na rayuwa ta kusa ko ta nesa, wannan yasa ko wace kasa/al'umma take cike da buqatuwan "Yayanta su zam masu ilimi cikin ko wani bangare na rayuwa.

Mu sani babu ilimi maras amfani saidai wanda me shi ya nufaci sharri ko ya aikata sharri dashi. Ilimi haske ne, jahilci kuwa duhu ne...
Mu tashi mu nemi sani don samun tsira anan da cen.
Allah yasa mu dace.

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Asset growth posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share