EngHausa24

EngHausa24 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from EngHausa24, Media/News Company, .

Wannan shine Comrade Abdullahi Ghali Basaf Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso da ya dauki nauyin karatun Dalibai 1100 su ...
17/02/2025

Wannan shine Comrade Abdullahi Ghali Basaf Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso da ya dauki nauyin karatun Dalibai 1100 su Karanci NCE a Sa’adatu Rimi College of Education.

A tarihin Nigeria ko akwai shugaban karamar Hukumar da ya taba yin irin wannan?

GASKIYAR LAMARI AKAN TIRKA TIRKAR SHUGABANCIN KARAMAR HUKUMAR KUMBOTSO. Daga: Musa Ibrahim DanbareA farko Jagora Kwankwa...
08/11/2024

GASKIYAR LAMARI AKAN TIRKA TIRKAR SHUGABANCIN KARAMAR HUKUMAR KUMBOTSO.

Daga: Musa Ibrahim Danbare

A farko Jagora Kwankwaso ya bawa Yantakara na Karamar Hukumar Kumbotso dama su fitar da mutum daya a cikinsu. Bayan sun shiga daki s**a fito s**a shaida masa cewa sun gaza fitar da mutum daya a cikin su, Mutum 26 cikin 30 s**a ce masa sun yadda ya shi da kansa ya zabi dantakara a cikin su, amma basu yadda ya bawa jagororin Karamar Hukumar dama su zaba ba, yantakara sun kara da cewa already jagorori suna da yantakarar su saboda haka idan ya basu dama s**a zaba baza suyi adalci ba.
Duk da wannan roko da yan takara s**ayi amma Madugu ya bawa Jagoranci dama s**a zaba. Bayan zaben dukkanin yantakara s**a hakura s**a bi hardworker.

Tun a ranar da aka ce an ayyanna shi mutane da yawa s**a rubuta petition (korafin cewa yana da matsalar takardar makaranta bai kammala sakandare ba).

Wannan shi yaja hankalin kwamitin fitar da yan takara na jiha aka ya yi bincike wanda a karshe bincike ya zama gaske cewa Hardwoker bai Kammala makarantar Gundutse Secondary School ba kamar yadda ya rubuta da hannunsa a jikin form din screening na takara.

Wannan dalilin yasa Madugu yace da yantakara da Jagororin Karamar Hukumar su dawo a sake zabar wani , bayan doguwar muhawara Jagoranci na Karamar Hukumar s**a zabo mutum 4 wanda aciki aka cimma matsaya akan Basaf.

A gidan Jagora Kwankwaso shi Ali Musa Hardworker da kansa ya yarda yana da matsalar takarda kuma ya ce da bakin sa ya karbi Hukuncin da aka yanke. Inda madugu yayi masa alkawarin zai sa Gwamna ya yi masa appointment.

Tun daga ranar da aka yi abin ake neman hardworker a waya amma yaki samùwa anje har gidansa amma an kasa samunsa. Kwatsam ba zato ba tsammani sai ji akai ya kai kara kotu wai shine dantakara. Kuma Ana zargin wani Danmajalisar Jiha da na tarayya ne s**a hada kai da wani tsohon Chairman da kuma jigo a gwamnati wajen zugawa da tsayawa shi Ali Musa yakai kara.

Abin da mutane ya kamata su sani shine:
Shi fa hardworker babu inda Jam'iyya tace shine Dantakara Bashi da wata shaida a hukumance da tace shine dantakara. Kuma ikirarin da yake an canza sunan sa ba haka bane, tunda dama can ba akai sunansa KANSIEC ba, Sunan Abdullahi Ghali Basaf kawai Jam'iyya takai, kuma Basaf kadai Jam'iyya ta bawa Nomination Form. Basaf Gwamna ya bawa tuta, Sannan Basaf ne yayi Screening a KANSIEC kuma sunan sa KANSIEC s**a fitar a matsayin Dantakara kuma shi s**a sanar a matsayin wanda yaci zabe.

To Don Allah bisa Adalci ta ina Hardworker ya zama Shugaban Karamar Hukuma?

Kuma ko a shari'ance, idan Jam'iyya tace wane shine Dantakara to dole shine Dantakara, anyi case kuma anyi hukunci irin wannan akan Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma Ahmed Lawal tsohon Shugaban Majalisar Dattawa. In da Kotu tace Jam'iyya ce take da hurumin tsaida Dantakara, saboda haka Jam'iyya tace Basaf ne Dantakar ta.

Yadda Yakin neman zaben Dantakarar Shugabancin Karamar Hukumar Kumbotso Hon. Abdullahi Ghali Basaf ya gudana, yayin da y...
21/10/2024

Yadda Yakin neman zaben Dantakarar Shugabancin Karamar Hukumar Kumbotso Hon. Abdullahi Ghali Basaf ya gudana, yayin da ya ziyarci mazabun Chiranchi, Danbare da Panshekara.

Muna addu’a Allah ya bamu Sa’a🙏

18/09/2024

Gwamnan jihar Katsina
Gwamnan jihar Sokoto
Gwamnan jihar Jigawa
Gwamnan jihar Kano
Gwamnan jihar Zamfara
Gwamnan jihar Kaduna
Gwamnan jihar Niger
Gwamnan jihar Kebbi
Gwamnan jihar Filato
Gwamnan jihar Taraba

Sune sabbin Gwamnonin Arewa da suke Tenure ta farko.

Shin tsakani da Allah a cikinsu, su waye s**a fi kamanta kokari akan al-ummar jihohin su da gudanar da ayyuka masu muhimmanci?..

Farfesa Hadiza Hamma daga Yobe ta zama mace mafi karancin shekaru a fannin shari'a a Arewa maso Gabashin Najeriya. Ta yi...
16/09/2024

Farfesa Hadiza Hamma daga Yobe ta zama mace mafi karancin shekaru a fannin shari'a a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ta yi karatu kuma tana koyarwa a University of Abuja.

Ta fito daga garin Potiskum.

Ita ce ta farko da ta samu Masters a Liberal Arts, Development Practice daga Jami'ar Harvard. Kuma ta lashe kyautar Dean's Prize for External Development Practice Capstone a Jami'ar Harvard.

Daga Hassan Talba Judge potiskum

04/09/2024

Maza sunfi Mata kishi,
Yes or No?

04/09/2024

Ancewa Amarya ta
Kunna A.C tace ba
Ashana 😲🙉😂😂😂

Comrade Ghali Basaf ya yi Kiran ne a Wani Dogon rubutu da yayi a shafin sa na Facebook da yaren Na Sara. A cikin rubutun...
25/06/2024

Comrade Ghali Basaf ya yi Kiran ne a Wani Dogon rubutu da yayi a shafin sa na Facebook da yaren Na Sara. A cikin rubutun Ghali ya ce shugaban Yan sanda na kasa (IG) ya Tabbatar da cewa Nigeria tana fama da karancin Jami'an tsaro. Ghali ya Kara da cewa yadda Kano take karuwa da yawan Jama'a da Kuma fama da matsalar Fadan Daba da Sauran matsalolin tsaro, barazana ne ga Zaman Lafiyar Jihar, saboda Haka ya kamata Gwamnatin Kano ya kamata ta kirikiri irin Jami'an Domin taimakawa Yan sanda da Sauran Jami'an tsaro Domin Magance matsalar. Ghali ya Kara da cewa a Jihohin Zamfara da Katsina da Kuma Kudu maso Yamma Sun yi irin su, Kuma suna Bada gudun mawa Sosai.

25/06/2024
Comrade Muhammad Alasan
Correspondent,of Kwankwasiyya Reporters at Kano State Government House.

Me za kuce?

07/06/2024

Fadi sunan Wani Abu da Kuka sani Wanda yafi Kuɗi Muhimmanci a Rayuwa:

MÚHAWARA: A Cìkìn Manyan Ƴan Síyasar Nájeriya, Wanéné Kuké Túnanìn Céwa Zai Iya Tara Irín Waɗannan Mútanen Haka, Ba Tare...
28/05/2024

MÚHAWARA: A Cìkìn Manyan Ƴan Síyasar Nájeriya, Wanéné Kuké Túnanìn Céwa Zai Iya Tara Irín Waɗannan Mútanen Haka, Ba Tare Da Ya Basu Ko Sisin Kwabó Ba, Saí Dan Sabóda Ƙaunar Da Súké Masa ?

Da dumi-Duminta:Wata Kungiya mai rajin Kare Al'adun Jihar Kano ta bawa, Tsohon Sarki Aminu Ado tsawon awanni 48 ya bar J...
26/05/2024

Da dumi-Duminta:

Wata Kungiya mai rajin Kare Al'adun Jihar Kano ta bawa, Tsohon Sarki Aminu Ado tsawon awanni 48 ya bar Jihar Kano ko Kuma su Dauki matakin Shari'a a Kansa.

A wata Sanarwar da Kungiyar ta saki ga manema Labarai 26/05/2024, Shugaban Kungiyar Comrade A.G. Sh*tu ya ce "Zaman Aminu Ado a Kano a Halin yanzu barazana ne ga dorewar Zaman Lafiya a Kano, saboda haka Muna gargadin sa Daya bar Jihar ko Kuma duk Wani Abu da ya faru mara Kyau a wannan Lokaci, a Dora alhakin afkuwar Hakan akan sa".

Sh*tu ya Kara da cewa, a baya da doka ta kawo Aminu Ado a 2019 mutane sun karbe shi a Matsayin Sarkin su, haka zalika tunda yanzu doka ta tube shi ya kamata ya hakura ya tara gaba.

Kungiyar ta Yi ikirarin Maka shi Aminu Ado a kotu idañ har ya gaza bin Umarnin Kungiyar.

26/05/2024

TSOHON SARKI YA BARRANTA KANSA DA ZARGIN TADA ZAUNE TSAYE Tsohon sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero ya barranta kansa da z...
25/05/2024

TSOHON SARKI YA BARRANTA KANSA DA ZARGIN TADA ZAUNE TSAYE

Tsohon sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero ya barranta kansa da zargin tada zaune tsaye inda yace wasu bata garine makiyan jihar kano suke qoqarin amfani da wannan dama wajen kawo fitina ya qara da cewa ya karbi qaddara kuma yana adduar Allah ya kare jihar kano kamar yadda iyayen mu s**a mutu suna masu kishi da qaunar jihar kano.

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when EngHausa24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share