06/03/2017
GASKIYAR LAMARI A AIKIN RUWAN BICHI
...RIJIYA TA BADA RUWA....
Hakika murnar da nayi ta ganin an dauko hanwar warware matsalar ruwan famfo a Bichi ta nemi komawa ciki, danaga aikin ya tsaya cak! Dole hankali ya tashi in aka lura da yadda alummar garin Bichi ke dandana kunarsu wajen samun ruwansha, musamman idan anyi la'akari da yadda gidan ruwa na Bagwai ya zamewa Bichi inuwar giginya.
A binciken da na gudanar, na fuskanci cewar Mutane sun damu kwarai, ganin cewar Danmajalissar Tarayya, Ahmed Garba ne tun asali, kimanin watanni uku, ya kawo aikin a karkashin hukumar koramun Hadeja - Jamaare. Inda hukumar ta turo injiniyanta tare da Dankwangila s**a zauna a ofishin Danmajalissar a Bichi tare da wakilansa. Daga nan s**a dung umma gidan Mai girma Sarkin Bichi tare da wakilin ma'aikatar Ruwa ta Kano, Aminu Kabiru Abubakar da Engr. Mamuda Musa Tahir, don tattauna yadda za'a tsara, a kuma gabatar da aikin. Sai dai daga baya an fara cece - kuce, inda wasu ke jayayyar hakan, har takai wasu tsoffin "Yan-Majalissa sun yi hira a gidan rediyo suna ganin aikin yafi karfin Danmajalisa, musamman dayake kasonsa na ayyukan Mazabarsa baya wuce Miliyan 40, kuma tuni ya sakasu a samarda fitulun t**i masu aiki da hasken rana da rijiyoyin burtsatse.
Yana da muhimmanci jama'a su san cewa Dan-majalisa na da hanyoyi 2 da zai kawowa alummarsa ayyukan alheri.
Hanya ta farko itace ta kason ayyukan Mazabarsa (constituency projects). Wannan hanya itace gama-garin hanya, wadda koda Danmajalissa na kwance a kauyensu, koda ba ya Jin Turanci zai sameta. Bata bukatar wani kokari ko shige da fice.
Hanya ta biyu itace ta yin kokari da fafutuka, shige da fice, neman alfarma, sanin mutane da makamar aiki. Itace hanyar dake bambance tsakanin hazikin Danmajalissa da Cikon Majalisa. Itace hanyarda da duk wani hazikin mamba ke amfani da ita wajen samowa alummarsa ayyuka. Ana iya neman alfarma wajen masu gudanarwa, ko ka nemi a sanyama aiki a Budget.
Hon. Ahmed Garba yayi amfani da hanya ta 2 wajen samo aikin ruwan Bichi da ma wasu ayyukan irinsu; Madatsan ruwa na Beli, Kungu da Malikawa, ginin ajujuwan karatu a makarantar yan-mata ta Bichi, samarda cibiyoyin habbaka kimiyyar sadarwa da sauransu.
Ahmed Garba ya gabatarwa da Ministan albarkatun Ruwa bukatunsa na aikin ruwan Bichi da na Madatsun ruwan da na lissafa a rubuce, kamar yadda na gani, a kwafen tankardar kuma ba tare da bata lokaciba aka amince, aka kuma turowa hukumar Hadeja Jamaare aikin Bichi, shi kuma na Dam din Beli da aka kaddamar aka turawa hukumar koramun Upper Niger. Kuma dukkansu aka sasu a kasafin kudi na 2016 tun a shekarar 2015, a lokacin Sanata Masudu Doguwane shugaban hukumar ta Hadeja Jamaare.
Yadda aka gudanar da aikin shine; Da farko an samarda injinan turo ruwan daga gidan ruwa guda 2. Sannan aka bi cibiyoyin ruwan dake rarraba ruwa a gari aka budesu aka sake hada masu sabon bututun ruwa, ya kewaye cikin garin ko ina. Haka kuma an fadada aikin har zuwa kauyen Dandushe da Unguwar Santar Namama, aka yi masu sabon hadi. Duk wannan an gudanar dashi a kan kudi kasa da Naira Miliyan N25. Abinda ya rage shine a hada bututun dake baiwa wadannan cibiyoyi da babban bututu mai inci 24, Wanda ake neman Izinin hukumar ruwa ta jihar Kano tunda mallakartane.
Kash! Abin takaici! Har yau shugaban hukumar yayi biris, yaki bada Izinin. Kodayake bayanan dake kewayawa sunce wai Umarni aka bashi daga sama, cewar in ya kuskura ya hada ruwan a bakin aikinsa. Majiyata tace wai wasu masu kishin Gwamnatin Jiharne, ciki harda wani Dankwangila dake kwadayin a bashi aiki s**a ruga wajen Lamba 1 s**ai masa koken muddin aka Bari aikin nan ya tabbata to kuwa tasu ta kare, a Bichi. Wannance tasa ba tare da la'akari da bukatar talakawaba aka dakile aikin.
Biri yayi K**a da mutum, idan muka lura da yadda rana tsaka! Babu wani shiri, babu tsari ko taswira, b***e batun budget, Gwamnatin jihar ta bada sanarwar ta ware kudi sama da Naira Miliyan 137 don gudanar da aikin ruwan Bichi. Aikin da tuni an kammalashi akan kudi kasa da Naira Miliyan 25.
A daya bangaren, akwai masu batun cewar wani Daraktan hukumarne Mai suna Habibu Shattima ya kawo aikin. A hakikanin gaskiya ba haka bane. Sai dai Habibu ya yi yunkurin yin amfani da alfarmar da shugaban hukumar Mas'ud Doguwa yayi musu tare da sauran takwarorinsa. Amma kuma an rigashi, domin tuni Danmajalisa ya nemi wannan alfarma har an sa masa shi a budget. Don haka Habibu ya nemi a bashi wata damar shima kamar takwarorinsa, amma akace hakan ba zai yiwuba, a linkawa Bichi abinda aka baiwa sauran. Muna fatan Allah ya bashi wata damar a gaba, ya kuma bashi Ladan niyya.
Daga karshe ina Kira ga shugabanni da sauran yan siyasa da su ji tsoron Allah su dubi talaka, su ajiye son zuciya. Ina Kira ga Gwamnatin Ganduje da ta taimaka ta Bari a jona mana wannan ruwa, don azabar ta isa. In yaso ta karkatar da wadancan makudan miliyoyin zuwa wani aikin, tunda abin da yawa. Kuma "dodo daya akewa tsafi" .. Inji Maguzawa. Sai dai kuma in wani Dan-lelen ake son arzurtawa, ko kuma anason yin "fasa-fasa Mu sha Kwai".
Ganduje a tausaya a sakarwa talakan Bichi Mara ya sha ruwa, ko ya Sami yin fitsari.
Mun Tuba!
Yusuf Salmanu Bichi — with Sani Mato Bichi and 16 others.