Karfin Jama'a Sabuwar Duniya

  • Home
  • Karfin Jama'a Sabuwar Duniya

Karfin Jama'a Sabuwar Duniya Yunkuri ne na haɗin gwiwa, ƙarfafa jama'a da gina sabuwar duniya mai adalci, ilimi da ci gaba. Karfin Jama'a – Sabuwar Duniya.

10/07/2025

Farfesa yace babu Farfesa da albashinsa ke isarsa a wata. Yace ba zai iya saka ɗansa makaranta a Abuja ba don albashin yayi kadan!

10/07/2025

“Dan Bello da Barrister Abba Hikima zamu shigar da kara kotu ranar Litinin in sha Allah domin neman hakkin ‘yan N-Power.”
✊✊🏿✊🏼

10/07/2025

“Ba za mu zuba ido mu bar wannan zalunci ya wuce haka nan ba. Yancin magana ba laifi ba ne. Faɗar gaskiya ba laifi ba ne✊🏿”

10/07/2025

Jama'a ku kasance masu lura. Ku haɗu. Ku shirya. Kada ku dogara da alkawuran banza✊✊🏼✊🏿

10/07/2025

Sun zalunci Matasa da N- Power da L- Power, sun yaudari Ƴan Sanda da sunan karin matsayi, sun zalunci al'ummar da ta yarda da su⬇️

Alhassan Mai Lafia yace “Wannan zanga zangar ta neman yanci ce agarekuKar ku bari tsoron kora daga aiki yahanaku fitowaK...
09/07/2025

Alhassan Mai Lafia yace “Wannan zanga zangar ta neman yanci ce agareku

Kar ku bari tsoron kora daga aiki yahanaku fitowa

Ko ku fito ku nemi yanci, ko ku cigaba da zama acikin ƙasƙanci 📌

Ƙauye da birni duk kufito, kuyi cincirindo akan hanyoyi da ma’aikatun gwamnati.”

📅 Ranar Zanga-Zanga: 21 Yuli, 2025
📍 Wurin Taro: Gaban Majalisar Tarayya, Abuja

Idan kaima mai saka uniform ne da aka yi watsi da kai… kai officer ne da aka manta da kai… ko kai mai son ganin adalci ne — wannan kira naka ne.

✊🏽 Dan Bello | Muryar Wanda Aka Manta da shi.






Karfin Jama'a Sabuwar Duniya ✊

09/07/2025

Bayan saka dubban ‘Yan Sanda tafiya daga jihohinsu zuwa Abuja domin interview na karin matsayi, sun fasa interview ɗin!

09/07/2025

Duk abinda Mutum ya Aikata, Sharri ko Alkhairi bibiyar mutum suke har Ƙabari, saboda haka wanda yayi da Kyau zai ga da Kyau.

09/07/2025

Tun kana aikin Dan Sanda, don ka nemi hakkinka - shugabanni sun fara cutar da kai, to ina ga idan ka yi ritaya?

GA KIRA – ZUWA DUKKAN ‘YAN SANDA DA MASU RITAYA!Kwanan nan … za ku daina barci cikin bakin ciki.Kwanan nan … za ku daina...
09/07/2025

GA KIRA – ZUWA DUKKAN ‘YAN SANDA DA MASU RITAYA!

Kwanan nan … za ku daina barci cikin bakin ciki.
Kwanan nan … za ku daina karɓar cin zarafi a matsayin ƙaddara.
Kwanan nan … za ku farka da ƙarfi — a matsayin ‘yan sanda ba bayi ba.

1. Ku ne kuka ɗauki bindiga lokacin da ƙasa ke ci gaba da ci da wuta.
2. Ku ne aka yi wa alkawari — amma aka bar ku da fanshon tozarci.
3. Ku ne aka faɗa wa: “Zamu duba ku.” Amma har yau babu komai sai shiru da mutuwa cikin talauci.

Yanzu lokaci ya yi.
Ba don siyasa ba. Ba don jam’iyya ba. Ba don wani shugaba ba.
Sai don mutunci.
Sai don yaranku da ke jira a gida.
Sai don zaman lafiya da kuka sadaukar da rayuwar ku a kai.

✊🏽 Ku fito! Ku tsaya! Ku faɗa!

Mun haɗu a gaban majalisa — ba da bindiga ba, ba da fada ba — amma da GASKIYA.
Gaskiyar da ke da ƙarfi fiye da duk wata ƙarya da gwamnati ke gaya mana.

*Wannan ba zanga-zanga ba ce kawai —
Wannan isar da saƙo ne daga ran wadanda aka ci amanarsu.
Daga ran wadanda s**a fi kowa saka rayukansu a cikin hadari don a zauna lafiya.
Daga ran wadanda yanzu sun gane: idan ba mu tsaya ba, ba wanda zai tsaya mana.

📅 Ranar Zanga-Zanga: 21 Yuli, 2025
📍 Wurin Taro: Gaban Majalisar Tarayya, Abuja

Idan kaima mai saka uniform ne da aka yi watsi da kai… kai officer ne da aka mantar da kai… ko kai mai son ganin adalci ne — wannan kira naka ne.

✊🏽 Dan Bello | Muryar Wanda Aka Manta Da Shi.

Karfin Jama'a Sabuwar Duniya ✊


Barr. Abba Hikima ya maka hukumar kiyaye haɗurra FRSC Kotu.Babban Lauya Barr. Abba Hikima ya maka hukumar kiyaye afkuwar...
08/07/2025

Barr. Abba Hikima ya maka hukumar kiyaye haɗurra FRSC Kotu.

Babban Lauya Barr. Abba Hikima ya maka hukumar kiyaye afkuwar haɗura FRSC Kotu, bisa tuhumar tauye hakkin dan Adam. Wannan ya faru biyo bayan tare lauyan da s**a yi a jihar Kano, tare da sauran masu ababen hawa suna yi masu tambayoyi takardu.

Muna roƙon Allah Ya taimake shi akan dukkan azzalumi.
Karfin Jama'a Sabuwar Duniya ✊

08/07/2025

Gaskiya ya kamata a gƴara albashin Ma'aikatan Ilimi a Nigeria, domin yaran mu su samu Ilimi mai Inganci!

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Karfin Jama'a Sabuwar Duniya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share