
04/04/2025
Innalillahi Wa Inna Ilaihiraji'un.
Ina mika sakon ta'aziyya ta ga iyalai da dalibai da gaba daya al'umar musulmi bisa rasuwar Sheikh Dr. Abdulaziz Dutsen-Tanshi. Koyarwar da ya yi da taimakon da ya yi wa addinin musulunci da musulmi zai ci daga da wanzuwa a zukatan mutane. Tabbas ya yi kokari wajen yada addini da taimakawa mabukata.
Ina addu'ar Allah ya jikansa da rahama ya bashi Aljanna Firdausi, ina kuma addu'ar Allah ya bawa yan'uwa da iyalai da dalibai hakurin jure wannan babban rashi da aka yi.