
14/07/2025
Mutane 4 sun mutu sannan 7 sun jikkata a rushewar wani gini a jihar Kano
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane huɗu da kuma jikkatar bakwai sakamakon rushewar wani gini a Abedi, Sabon Gari, ƙaramar hukumar Fagge, Jihar Kano.
Dr. Nuraddeen Abdullahi, Kwamishina a NEMA na Ofishin Shiyyar Kano ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Litinin a Kano.
Ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa a jiya Lahadi, 13 ga Yuli, da misalin ƙarfe 6:49 na yamma cewa wani bene mai hawa uku da ba a kammala ba ya rushe a Abedi Sabon Gari, Kano.
Malam Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:42 na yamma bayan mamakon ruwan sama da aka shafe tsawon lokaci ana yi.
“muna samu bayanin, sai mu ka
hanzarta tura tawagar ceto da neman agaji (SAR) zuwa wurin tare da haɗin gwiwar sauran hukumomi masu ruwa da tsaki,” in ji shi.
Abdullahi ya ƙara da cewa, shaidu sun tabbatar da cewa mutane da dama na kasan ginin lokacin da ya rushe, kuma da dama sun makale ƙarƙashin baraguzan ginin.
Kwamishinan NEMA ya ce, zuwa ƙarfe 1:56 na safe a yau Litinin, an tabbatar da mutuwar mutane biyu, sannan an ceto mutane shida da s**a jikkata.
A cewarsa, karin mutane biyu sun mutu, sannan wani mutum guda ya ji rauni da misalin ƙarfe 5:41 na safe, kuma duk an garzaya da su zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano domin kulawar likita.