Labarai Informations de contact, plan et itinéraire, formulaire de contact, heures d'ouverture, services, évaluations, photos, vidéos et annonces de Labarai, Société de médias/d’actualités, Democratic Republic of the.

14/05/2023

Bai Halatta Ka Auri Mace Ƴar Soshiyal Midiya Wacce Take Ɗora Hotunanta Da Videos Ɗin Ta A Kafofin Sada Zumunta Ba. - Inji Dr Bashir Ahmad Sani Sokoto.

Daga Faisal Sadauki Jos

14/05/2023

Wannan Yaron Damfara Ne Kawai Domin Neman Abun Duniya Ake Amfani Dashi.
Bansan saurin me iyayensa suke yi ba da s**a tura shi kasuwa da sunan tafsiri.
Ko gezau bazan yi idan nace wannan yaron baida illimin da zai yi tsafsiri koda kuwa yana da haddar Alkurani. Shi yasa ma idan an lura da kyau za aga shirya masa ma abunda zai yi tafsirin akai suke yi. Kuma mai yasa bai karantarwa bayan azumi sai dai kawai yayi tafsirin da azumi ?
Kamin Kayi tafsiri sai an karantar da kai, illimin tasirai musamman littafen tafsirin da s**a shahara a duniyar musulunci.
Haka nan duk mai wannan illimin za a ganshi da daliban da yake karantar dasu a zahiri. Kawai dai so suke Yaudari mutanen da sunan shi wannan yaron waliyi ne. Domin karbar kudi wajen jahilai.
Mutane Aji Tsoron Allah.

Daga: Abdul A U Tonga

14/05/2023

WATA SABUWA: Kamfanin Revival Technology Suna Cigaba Da Samun Makudan Kudade Da Hannun Jarin Miliyoyin Daloli Saboda Yunkurinsu Na Samar Da Wata Fasaha Da Zata Iya Dawo Da Wanda Ya Mutu Duniya.

A yanzu haka akwai sama da mutum dubu shida wanda s**a biya makudan kudade da zummar duk lokacin da s**a mutu a ajiye gawarsu har sai an gama binciken yanda za'a dawo dasu duniya a inda wasu kuma s**a biyawa yan uwansu wadanda sun jima da mutuwa.

Daga Usman Umar Dagona

13/05/2023
13/05/2023

Gidan Da A ka Haifi Annabi SAW, Amma Yanzu Dakin Karatu Ne.

Wannan dakin karatu da ke She'eb Banu Hashim a garin Makkah an gina shi ne bisa tunawa da haihuwar Manzon Allah (SAW) wanda aka haifa a Rabi'ul Awwal, a shekarar giwaye (Afrilu, 571 miladiyya) . Za a iya samun zuriyarsa tun daga Annabi Ibrahim (عليه السلام).

Mahaifin Annabi (SAW)

Mahaifin Manzon Allah (SAW) Abdullahi (RA) ya rasu kimanin watanni shida kafin haihuwarsa. Ya yi Tafi fatauci zuwa Gaza da Sham a arewa kuma a kan hanyarsa ta dawowa ya sauka a Yasriba (daga baya aka fi sani da Madina ). Ya yi rashin lafiya, ya Rasu aka binne shi a can. Don haka aka haifi Annabi (SAW) maraya.

Haihuwar Annabi (SAW)

A lokacin da mahaifiyarsa Amina na da ciki, ta yi mafarki, an yi mafarki wani haske ya haskaka daga jikinta wanda ya haskaka fadojin Sham. Lokacin da ta haihu, Shifa bint Amr, mahaifiyar Abdul Rahman bin Auf (رضي الله عنها) ta yi mata ungozoma.

Abdul Muddalib (RA) ya samu labarin haihuwar jikansa cikin farin ciki. Ya kai jaririn da aka haifa zuwa dakin Ka'aba yana godiya ga Allah Ganin cewa jikansa zai girma har a yaba masa sosai, Abdul Muttalib ya sa masa suna Muhammad, wanda ke nufin 'wanda ake yabo'. A bisa al'adar Larabawa, sai ya aske kan jaririn, sannan ya gayyaci 'yan uwansa Makka Don liyafa.

Kamar yadda Abul-Fida ya ruwaito, a lokacin da mutane s**a tambayi Abdul Muddalib dalilin da ya sa ya kira jikansa Muhammad, yana fifita sunan akan na kakanninsa, sai ya ce: “Don ina da buri ne a yaba wa jikana. kuma an yaba wa masa a ko ina duniya. "

Shayar Da Manzon Allah (SAW)

Mahaifiyarsa ta fara shayar da Annabi Muhammad (ﷺ), sannan kuma Ummu Ayman, kuyangar mahaifinsa. Bahabashiya (Habasha) wacce ainihin sunanta Barakah, wacce daga Baya ta musulunta ta kuma yi hijira zuwa Madina, inda ta rasu bayan wafatin Manzon Allah da wata shida. Don haka ne Barakah (رضي الله عنها) ta ke da banbanta saboda kasancewarta wanda ta fi kowa sanin Annabi (SAW) tsawon lokaci.

Thuwaybah, baiwar kawun Annabi Muhammad (ﷺ) Abu Lahab, itama ma ya shayar da Annabi, a lokacin Thuwaybah ita ma tana renon danta Masruh da Hamzah bn Abdul Muttalib da Abu Salamah bn Abdul Makhzoomi. Saboda haka, waɗannan mutanen sun zama ’yan’uwan Reno domin an shayar da su nono ɗaya. Thuwaybah ta shayar da Manzon Allah (SAW) na tsawon kwanaki bakwai, a rana ta takwas kuma aka ba shi amana ga Haleemah ta cikin gidan Banu Sa’ad domin ta rene shi a cikin sahara.

Nasaba

Nasabar Annabi (s.a.w) mai daraja ita ce, shi ne Muhammad dan Abd-Allah, dan Abdul-Muddalib, dan Hashim, dan Adb Manaf, dan Qusayy, dan bin Kilab bin Murrah bin Ka’b bin Lu’ay bin Ghalib bin Fihr bin Malik bin al-Nadr bin Kinanah. dan Khuzayaymah bin Mudrikah bin Ilyas bin Mudar bin Nizar bin Ma’add bin Adnan har Annabi Isma’il (عليه السلام) dan Annabi Ibrahim (A.S). عليه السلام).

Me ya faru da Gidan Haihuwar Annabi (SAW)?

Lokacin da Annabi (SAW) ya yi hijira zuwa Madina, Aqil bin Abi Talib ya kwace gidan. Shi kani ne ga Annabi (SAW) bai musulunta ba a lokacin.

Bayan wafatin Annabi (ﷺ) a shekara ta 632 miladiyya, da farko wannan gida ya kasance a hannun iyalan Aqil bIn Abi Talib. Sannan Muhammad bin Yusuf al-Thaqafi, Hajjaj bin Yusuf ya saya. Wannan shine dalilin da ya sa yawancin litattafan farko s**a rubuta wannan Wajen da cewa mallakin Muhammad bin Yusuf ne.

Lokacin da al-Khayzuran, mahaifiyar khalifa Abbasiyawa Haruna al-Rashid, ta yi aikin Hajji a shekarar, ta sayi wannan wajen. Ta mayar dashi don Tunawa da haihuwar Manzon Allah (SAW) ta gina masallaci inda mutane za su yi Sallah su kuma ziyarci inda aka haifi Manzon Allah (SAW).

Gidan ya ci gaba da zama karamin masallaci tsawon karnoni da dama, kuma halifofi daban-daban sun kula da shi, da kuma gyara shi a tsawon karnoni, ciki har da khalifan Abbasiyawa, Ahmad al-Nasir, wanda ya gyara shi a shekara ta 576 bayan hijira. Hakanan an kiyaye tsarinsa.

Juyawa zuwa ɗakin karatu

Masallacin an Rushe shi shekara ta 1950. Sakamakon matsin lamba daga manyan malaman addini na lokacin, sabuwar gwamnatin Saudiyya ta mayar da gidan ( muhimman wajen tarihi) saboda fargabar cewa mutane za su sa su mayar da Wajen Abin Girmanawa.

Sai dai wannan lamari ya ba wa magajin garin Makkah na lokacin Shaikh Abbas Yusuf Qattan mamaki. Ya yi nasara wajen samun takardar doka don samun iko da wurin kuma ya kafa ƙaramin ɗakin karatu a saman harsashin gida a 1953.

Laburaren ya ƙunshi ƙananan benaye guda biyu masu a yamma yana fuskantar Masjid al-Haram. Dakin karatun Yana dauke da tarin rubuce-rubuce da kuma jaridun gida, na Larabawa da na Musulunci.

12/05/2023

WAIWAYE: Ko zaku iya tuna 'Username' dinku na 2go ?

Waɗannan sune iyalan gidan  dangin Banu Shayba. Banu Shayba sune iyalan da suke riƙe da makullan ɗakin Allah wato Ka'aba...
09/05/2023

Waɗannan sune iyalan gidan dangin Banu Shayba.

Banu Shayba sune iyalan da suke riƙe da makullan ɗakin Allah wato Ka'aba kuma suna masu mata hidima a koda yaushe. Sune suke buɗeta, kulleta da wanke ta.

Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam ne ya wakilta wannan zuri'ar ta Abu Shayba da wannan gagarumin aikin kuma yayi umarnin cewa su zasu dinga yi har abada.

Zuri'ar Abu Shayba sun samo asali ne daga Usman Ibn Ɗalha, wanda a ranar da aka buɗe Makkah Annabi ya ɗamƙa mishi makullan Ka'aba tare da umarnin cewa zuri'arsa su cigaba da kula da ita har zuwa ranar ƙiyama.

Allah ya karawa Annabj Daraja.

Daga Auwal Saleh

Duk Wanda Yake Ganin Man City Za Ta Yi Nasara Akan Real Madrid Na Saka Wayata Kirar iPhone 12pro Da Kuma Kudi Naira Dubu...
09/05/2023

Duk Wanda Yake Ganin Man City Za Ta Yi Nasara Akan Real Madrid Na Saka Wayata Kirar iPhone 12pro Da Kuma Kudi Naira Dubu 50, Inji Sarki Havila

An gudanar da sunan ƴaƴan Magen wata Matashiya a unguwar Sheka Kudu dake ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano.Matashiyar mai ...
09/05/2023

An gudanar da sunan ƴaƴan Magen wata Matashiya a unguwar Sheka Kudu dake ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano.

Matashiyar mai suna Halima Adam mai laƙabin ƴar Madara, ta ce, har kwana biyu ta yi a gadon Asibiti, lokacin da aka sace ma ta uwar Magunanta.

Adresse

Democratic Republic Of The

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Labarai publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Contacter L'entreprise

Envoyer un message à Labarai:

Partager