03/09/2023
CIKAKKEN BAYANI GAME DA TSARIN CUG KO TSARIN ME AND YOU
MTN CUG Tsari ne da za a ɗora maka nambarka ta MTN akai domin ka riƙa kiran duk wani layi na MTN da shima yake kan tsarin na CUG, ɗoraka akan tsarin shi ake kira da Activation
bayan an ɗoraka akan tsarin zaka yi subscription na 600 domin fara yin kira free, zaka saka kati ka danna wasu lambobi.
Kasani cewa Koda ka danna wanan code din bazaka iya shiga tsarinba dole sai munsaka
Idan ka danna kamfani zasu ɗebi kuɗin subscription ɗin, daga nan sai ka fara kiran duk wani layin MTN da shima yake kan tsarin na CUG
Subscription ɗin yana ƙarewa zuwa ƙarshen wata, duk farkon wata zaka ƙara saka kati na 600 ka sake danna waɗancan nambobi
Sai dai kuma wanda yayi subscription a tsakiyar wata ko kuma dai wasu kwanakin na watan sun wuce to kamfani ba zai chaji mutum 600 ba, ma'ana abinda za'a chaje shi ba zai kai 600 ba tunda ba farkon wata bane anci wasu kwanakin a cikin watan
KA LURA
- Layinka na MTN da kake amfani da shi shi ake yiwa activation ba sabo zaka siya ba, kawai lambar layin zaka bada
- Sannan dole layinka ya zama yana da rijista, idan ba shida rijista baya yi
- Bayan an maka activation ma'ana an ɗoraka akan tsarin dole sai kayi subscription kafin ka fara kira free
- Kai zaka riƙa yin subscription da kan ka bamu zamu riƙa yi maka ba
- Iya waɗanda suma suke kan tsarin MTN CUG zaka kira free
- Idan ka kira waɗanda basa kan tsarin na CUG koda MTN number ka kira to ba zaka yi waya dasu free ba, hakama idan ka kira Airtel, 9mobile, Glo
- Iya waya zaka yi free banda browsing, sannan ba kuɗi MTN zasu tura maka ba a layin naka, kawai dai za kayi waya ne free
- Sannan koda ana binka kuɗi a layinka za a iya yi maka activation, amman idan kazo yin subscription dole sai ka fara biyan bashi.
- Bayan anyi maka activation, sannan kuma kayi subscription, ana so ka riƙa barin kuɗi a layinka ko kaɗanne, saboda idan balance ɗinka 0 yake to kira free baya yi. A ƙalla ace akwai N1 ko 5 zuwa sama
a ciki
Gamai bukata yamun magana 07035951245