
30/08/2025
Tsohon Gwamnan jihar Kano,Engr Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, yace ’yan Najeriya sun riga sun yanke shawara kan zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar NNPP, Kwankwaso ya ce: “A yau, yawancin ’yan Najeriya na kokarin yadda za su samu abinci. Wasu sun rasa matsugunansu saboda rashin tsaro. Wasu kuma suna asibiti ba tare da kulawa ta gari ba—ko kuma ba za su iya zuwa ba saboda babu kuɗi a hannunsu.
Mutanen wannan kasa sun yanke shawara kan abin da za su yi a 2027. Shi ya sa muke farin ciki da kanmu—saboda muna tare da jama’a. Kuma jama’a sun san muna tare da su. Ba mu gamsu da abubuwa da dama ba da suke faruwa a faɗin kasar nan, musamman batun talauci.
Talauci ya mamaye ƙasar nan, musamman a wannan yanki (arewa). Talauci ne mai tsanani. Al’ummomi da dama ba za su iya zuwa gona ba. Wasu ba za su iya zuwa kasuwa ba. Wasu ma ba za su iya komawa gidajensu ba.
Kwankwaso ya gargaɗi mambobin NNPP da kada su bari sauya sheƙa da tattaunawar kawance tsakanin ’yan siyasa su ɗauke hankalinsu.
Bari in tunatar da mu: kada mu bari sauya sheƙa da jita-jita su ɗauke mana hankali.
Wasu mutane na sauya jam’iyya cikin sauki, suna tunanin sun san komai—alhali ba su fahimta sosai ba. Idan suna son sanin gaskiya, sai su zo su tambaye mu,” in ji shi.