22/08/2025
Na kusan shan duka a wajen sojoji wajen daurin auren Yusuf Buhari
Daga Salmanu Rabiu Gwarzo
A wajen gudanar da daurin auren Malam Yusuf Muhammad Buhari da amaryarsa Gimbiya Zahra Nasiru Ado Bayero wanda duk wanda ya je wannan guri ya ga yanda aka jibge jami'an tsaro.
Yayin da na shiga Garin Bichi na je daidai ‘gate’ din da ake shiga, na ga yanda jami'an tsaro su ke dukan mutane, sai wadansu masu goshi da kyalli kawai ake bari su wuce.
Nan na yi nazari na koma daya ‘gate’ din; shi ma na ga wane wancan na farko; domin idan sarakuna su ka taho da tawagar su, sai ka ji jami'an tsaro na cewa “only Emirs dey pass”. Na yi kwana na koma wancan gate din na farko da na bari.
Na yi shiga kai ka ce wani odilan ne ko DSS, na tsaya na kara karantar wurin daga nan wata tawaga ta taho shi ne fa sojojin nan su ka k**a tafkarsu da duka, su ka yo baya gabadaya har jagoransu. Ina ganin haka kawai na yi shahada, na tunkaro ‘gate’ din nan da ‘confidence’ di na, su kuwa su na dukan wadannan mutane, ni dai na cire tsoro a gefe kawai na tunkaro sojojin nan masu dukan mutane. Kawai sai mu ka hada ido da wani soja, na daga masa kai na ce masa “well-done, well-done”. Kawai Ina tsoron kada ya ce mini “identify yourself”, sai na ji yace mini “you’re welcome sir”, sai na yi ajiyar zuciya na kuma ce masa “how work?”, ya ce “fine sir”. Nan fa sauran sojojin nan su ka bude mini hanya, fuskata a murtuke, na shige.
Can ciki ma ‘gate’ biyu ne. Da Goodluck Ebele Jonathan ya shiga sai na shiga cikin tawagarsa na koma ta bangaren Orubebe. Bayan mun shiga gurin saukarsu na ga duk kusan mutanen da s**a yi shigar kayan jami’an tsaro ne wajen mutum 50. Na ce to fa, a zuciyata.
Na tsaya kusa da wasu ana ta hira ni kuma wajen minti 10 su ka ji ni shiru, shi ne fa wani ya juyo yace mini “Bros with who you dey?” Kawai da ‘confidence’ di na na ce ma sa “I dey with my boss, he is inside”. Sai kawai ya ba ni hannu na cafke, ya ce mini “you’re welcome”, na mayar masa “you’re welcome too”.
Daga nan na ji ‘yan ‘protocol’ din fadar shugaban kasa suna magana da turanci akan ana jiran shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya zo za su shige gurin da aka ware za'a yi daurin auren, inda nan jami'an tsaro ke tsananin tantance masu wucewa, tunda duk su Vice President Osinbajo da Atiku da Bua da sauran su duk su na gurin, kawai da na ga haka na yi maza-maza na fece.
Nan fa na dawo kofa na tsaya, na k**a taya jami'an tsaron nan sharar fage. Akwai wani ya zo wucewa, na dafe masa kirji na ce masa, “yeah who are you, identify yourself...” ya kasa ce mini komai, ni kuwa na saita masa hanya na ce masa “Go back!”
Bayan sun saba da ni k**ar tsawon minti biyar sai na sanya kai na shige kawai.
Nan na ga Nigeria fa iya Nigeria acikin gurin nan.
Har na je kusa da ango tunda dan uwanmu ne, aka yi ta zumunci.