15/07/2025
Cibiyar kirkire-kirkire da ci gaban aikin jarida (CJID) ta horar da ‘yan jarida sama da 15 a jihar Adamawa a karo na uku na shirinta na hada kai da sashin yada labarai, da nufin kara karfafa kwarin gwiwar masu yada labarai wajen tunkarar kalubalen shari’a akan aikin jarida da kuma tabbatarda‘yancin ‘yan jarida.
Taron na yini daya da aka gudanar a Yola, ya mayar da hankali ne kan batutuwa masu muhimmanci da s**a hada da rage kalubalen shari’a a aikin jarida, da dokokin da suke shafar aikin jarida.
Da yake jawabi a wajen taron, Mista Idris Akinbajo, Editan Jaridar Premium Times, ya gabatar da jawabi mai taken Dabarun Aiki ga ‘Yan Jarida da Kungiyoyin Yada Labarai don Gujewa Tauye Hakki daga fannin Shari’a.
Ya jaddada mahimmancin tsare-tsare da zasu inganta aikin yada labarai da samarda ilimin shari'a ga 'yan jarida da gidajen watsa labarai, yana mai gargadin cewa rashin bin Dokoki da ka'idoji-ciki har da dokokin haraji, ana iya amfani da hakan wajen durkusar da gidan watsa labarai.
Shima da yake jawabi shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) reshen Yola, Idi Ali, ya yabawa kungiyar CJID bisa shirya wannan horon, inda ya bayyana cewa yana da matukar muhimmanci musamman wajen tabbatarda kariya da kwarewar ‘yan jarida.
Ya bukaci 'yan jarida da su kiyaye ka'idojin aikin su don rage barazanar shari'a da kuma take hakkin su.
Mahalarta taron sun nuna godiya ga cibiyar CJID akan wannan shiri, tare da lura da cewa horon ya inganta fahimtar su game da SLAPPs da sauran matsalolin shari'a da ke fuskantar 'yan jarida.
Sun ce ilimin da s**a samu zai taimaka musu wajen kare kansu da aikinsu daga cin zarafi, muzgunawa da take musu Hakki.