10/04/2025
An Fara Taron Mu'utamar Na Kasa Da Ƙasa "International Conference" A Birnin Kano Nigeriya.
An shiga babban taron nan na Mu'utamar ɗin ƙasa da ƙasa a garin Kano Nigeriya wanda aka masa take da (Halin Da Ake Ciki Ina Mafita) wanda Harkar Musulunci Ƙarƙashin Jagorancin Sheikh Zakzaky (H) s**a saba shirya wa Lokaci bayan lokaci. Wannan Mu'utamar shine Karo na Huɗu (4) wanda aka fara yi a Ƙasar Nijar , sannan Katsina, Biyo baya garin Lafiya sai wannan na Kano shine karo na Hudu.
An fara taron na yau Alhamis 10 ga watan Afrilu 2025 bayan sallah Isha wanda Wakilin Ƴan uwa na Funtuwa Sheikh Rabi'u Funtuwa ya bude da addu'a, sannan an Gabatar da karatun Alqur'ani Mai Girma domin samun albarka da rahma Allah ga taron da za'a yi. An Gabatar da Majalisin mawaƙa daga bakin mawaƙan harka Islamiyya cikin da Nasiru Fudiyyah, Zahraddini Koɗe, da sauran mawaƙa da s**a Gabatar da ƙasidu a wajen.
Malam Abubakar daga ɓangaren Academic Forum ya wakilci Forums ɗinda suke da alhakin jagorancin shirya Mu'utamar na Harka Islamiyya wanda yayi bayanin maƙasudin taron da za'a Gabatar. Malama Maryam Sani ta daura jawabin ta akan manufa da hadafin Mu'utamar tare da kiyaye tsari da mizanin harka, tayi bayanin kiyaye Sallah, yin abu da ƙa'ida girmama mutane da nuna kyakkyawar mu'amala.
Mau'du'in Farkon da aka gabatar a wajen taron shine "Mujahada Da Makarimul Aklak" daga bakin Malama Hauwa'u Taheer daga garin Kaduna da take bayani akan kyawawan dabi'u ta kawo qyar Alkur'ani da Allah yake cewa, muna da kyakkyawan misali a gare ku, wato shine Annabi Muhammad (S). A wani ruwaya kuma Annabi yana cewa, "An Aiko nine domin na cika kyawawan ɗabi'u"
Cikin jawabin ta ta kawo kyawawan dabi'u na Manzon Allah (S) wanda ake do kowanne mutum yayi koyi da su. Wani hadisi daga Imam Sadiq yana cewa, Manzon Allah an zabe shi ne da kyawawan dabi'u duk wanda ya tsinci kansa da kyawawan dabi'u guda 10 zai kasance ya yi koyi da Annabi (S) daga ciki akwai, Gaskiya , Sajaa, hakuri, kishi, kyauta, Jarumta, kyawawan dabi'u, sadar da zumunci.
Imam Ja'afar Assadiq (As) Yana Cewa, "Ku kasance masu kira gamu ba tare da kun yi magana ba" wannan hadisi yana magana ne akan cewa ku yi kyakkyawan mu'amala da mutane da nuna musu kyakkyawar dabi'u ga mutane har su fahimce ka su fahimci da'awar addinin ka.