01/11/2025
JAGORA (H) YA RUFE MU’UTAMAR DIN MEDIA FORUM A ABUJA
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Da yammacin Asabar 10 ga Jimadal Ula, 1447 (1/11/2025) Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya rufe Mu'utamar da Dandalin Yaɗa Labaran Harkar Musulunci (Media Forum) a gidansa da ke Abuja.
Mu'utamar ɗin wanda Media Forum ta shirya na yini daya a garin Abuja, ya tattaro mahalarta daga dukkan sassan kasar nan, tare da wakilai daga bangarori daban-daban na Media din Harka Islamiyya, inda aka gabatar da jawabai akan Maudu'ai daban-daban da s**a shafi aikin jarida da Nizami Harka Islamiyya.
A yayin jawabinsa, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fara da bayyana tarihin yadda al’amarin isar da sako ta hanyar ‘media’ ya faro a Harkar Musulunci da buga ‘yan takardu masu isar da sako, daga bisani aka yi yunkurin samar da Mujallar Turanci mai suna Al-Mizan a farkon shekarun 1980s, inda a farkon shekarun 1990s aka samar da jaridar Hausa ta Almizan mai falle biyu, daga baya ta rika fadada tare da tasiri mai girma dukkan sassan kasar nan.
Harwayau, Jagora ya bayyana yadda aka rika samar da Jaridun Turanci na Pointer, da Pointer Express, da kuma Mujallu irin su Mujallar Gwagwarmaya, Mujallar Mujahida da sauransu, wanda duk daga baya s**a kwanta. Inda ya dauki lokaci yana bayani akan zuwan Intanet, da yadda ya rika cigaba har zuwa ga samuwar ‘Social Media’, wanda ya kunshi rubutu, hoto, da hoto mai motsi, kuma ake amfani da shi wajen yada sakon kaitsaye a cikin lokaci, ba kamar yadda jaridun takarda suke da jinkiri ba.
Shaikh Zakzaky (H) ya ja hankalin masu bibiyan kafafen sadarwa akan su rika bashi lokacin da za su rika dubawa a kowane rana, domin kar ya rika cinye musu lokaci. Ya ce, “in ka lura da lokacin da kake ci a Social Media, za ka kuma tambayi kanka, awa nawa na yi a karatun Alkur’ani da Sallah da sauransu. Kamata ya yi kowane abu ka bashi lokacinsa, in ba haka ba sai ka bannata lokacinka, domin shi wannan abin na da cin rai.”
Ya kuma bayyana yadda Yammacin Duniya ke kokarin sarrafa kakafen, wanda dama mafi yawa mallakinsu ne. Yace, wanda ma ba nasu din ba ne, to s**an yi kokarin kutse a cikinsa don su samu cikakken daman iko da shi. Inda ya bayar da misali da yadda Tiktok ya rika fallasa ta’addancinsu, alhali suna iya ‘control’ din sauran kafafe irin su Facebook, wanda hakan yasa yanzu s**a yi kokarin sayen ‘share a Tiktok din, don su rika sa ido akan wadanda suke ‘posting’ abinda bai yi daidai da ra’ayinsu ba kamar yadda suke yi a sauran kafofin.
Jagora ya kuma jaddada muhimmancin kafafen na sadarwa, inda ya bayyana cewa sun fi kowane kafa isar da sako a yanzu, saboda su suna zuwa ga mutane ne nan take.
Ya nuna takaicinsa matuka, akan yadda ganin amfaninsa mai kyau, sai kuma makiya ke amfani mare kyau da shi wajen kirkiran farfaganda da karairayi, da kuma kirkiran rigingimu da hayaniyar da wasu da gangan suke tado maganar da za a yi ta musu da musayar raddodi, in an kammala akan wani abin saisu kara kunno wani daban. Ya ce: “Kamar wasu sun dauka idan suna surutai irin wannan ana ta zuzutasu, kamar yana daukaka sunansu ne. Suna son su yi kaurin suna ne.”
Yace: “Kar wannan masu neman su yi kaurin suna su dauke ma mutane hankali, ya kamata a yi banza da su ne, a yi kokari a gina abin kirki, wanda kuma shi ke wahala.
Jagora ya nuna takaicinsa akan yadda makiya addini ke ta kokarin sai sun baiwa ‘yan uwa Musulmi sunan kungiya, ya ce: “Tunda su sun ce su kungiya ne, wai ala dole mu ma kungiya ne. Kuma yanzu ma suna wani yayi, wai suna neman su yi kungiya, su ce wai har da mu a ciki. Nace haba! Ai linzami ya fi karfin bakin kaza! wani bai isa ya ce ya yi kungiya ya saka mu a ciki ba, mu mun wuce nan! Ba dai akan addinin nan ba.
“Mutane yanzu kowane na ta fito da wani abu, wai mu kungiya ce. Wa ya ce maka? Mu mun ce muna addini ne, mu muke ‘representing’ din addinin. Amma sai s**a ce wai har da kungiyar kaza, wai kungiyar Mazhaba. A kafafen watsa labaru, wai kungiyar Mazhabar Shi’a, ko ‘yan Shi’a, ko kaza. Wai ala dole, tunda su sun yi kungiya, to ku ma kungiya ne. To ku kuke da kungiya, mu muna addini ne, mu bamu da wata kungiya, mu abinda muke yi sunansa addini ne. Ku ku yi ta kungiyoyinku!” Inji Shaikh Zakzaky (H).
Ya kara da cewa: “Na’am, ku kungiya ne, amma mu ba kungiya ba ne, ba kuma za mu taba zama kungiya ba. Ba kuma za a taba saka mu a cikin kungiya ba. Mu addini muke yi. Addinin Musulunci. Tun farko bamu taba ce muku addinin Musuluncin kuma ya kasu kashi-kashi ba, ba mu taba ganinsa a kashi-kashi ba, mu mun san addinin Musulunci bai kasu kashi-kashi ba! Abu daya ne rak! Sakon da Manzon nan ya zo da shi daga wajen Allah. Illa-iyaka, zance ya kare.”
Harwayau, Jagora ya ja hankali akan kokarin gina Fikira Sahihiya na sanar da mutane mene ne addini a hakikarsa, da kuma yunkurin dawo da ikonsa ya tabbata daram a doron kasa, wanda yace makiya kan kasa fahimtarsa, su yi ta masa fassara daban-daban.
Ya bayyana yadda Alkur’ani ya kawo tarihin Annabawa da s**a zo s**a kirayi al’ummarsu daban-daban, yace sam ba a kan kungiya ko mulki ko sarauta suke ginawa da’awarsu ba. “Ana ce mutane su zo su bauta ma Allah a bisa ka’idar da aka saukar ne, abinda ake ce ma mutane kenan. Ba an ce musu su zo su shiga wata kungiya ne ba.”
Yace: “To mu ma mukan ce, tunda mun yi sa’a mu dama al’ummar Musulmi ne, abinda muke cewa, al’ummar ta dawo bisa addininta. Illa iyaka. Amma sai s**a ce ku kaza ne.”
Jagora ya ja hankali akan kar mu daka ta mutane wajen amsa sunan ‘yan kaza da suke saka ma mutane. Ya bukaci “a dora mutane ne akan Fikira Sahihiya na cewa, addini ake yunkurin tabbatarwa, addinin nan kuma sunansa Al-Islam, shi kuma Al-Islam din nan ‘shaamil’ ne, karkashinsa ne aka sami fahimta daban-daban. Fahimta daban-daban ba addinai ne daban-daban ba, fahimtar shi wannan addinin ne. Kuma ana batun in addinin ya kafu, to shi zai tafi ne bisa shi ka’idan addinin, ba son ran wani ba, ba fahimtar wani ba.”
Jagora ya jadda jan hankalin ‘yan uwa akan kar su bari a rika shagaltar da su da wasu abubuwan da ba shi ke gabansu ba. “Na san wasu janibobi da s**an fada tarko, in an zage su su yi zagi, ka ga an yi batsattsale a ciki. Kuma abinda wadancan suke so kenan. To kai kar ka yarda a kautar da kai daga abinda kake kai. Ka yi ta fadan abinda yake shi ne daidai. Mai zagi ya yi ta zage-zagensa, kai kuma ka yi ta yi, in ka daka tasa, za ka koma ne ka zama kana bashi amsa, kuma abinda yake so kenan. To mu kar mu daka tasu, ya zama kullum kokarin kwakkwafa mutane akan abinda yake shi ne daidai, da kuma tsayawa kyam, da yi domin Allah, yi don Allah, yi don Allah, insha Allah.”
Ya karkare jawabinsa da nasiha kamar yadda ya saba akan yin kpomai saboda Allah. Ya ce: “Ana yi ne saboda Allah. Yi don Allah, yi don Allah, yi don Allah, ba don ka yi suna ba. Kuma in ana tare ana aiki kar ka dauka kowa zai ba da hadin kai a yi lafiya lau a tafi, a’a dabi’an mutum ne, in aka tara mutane, sai an ji abubuwa, sai an ce, wannan shi ya yi kane-kane, ko kuwa wannan dan bani na iya, wancan in ba shi aka ce ba rigima za a yi. Wannan an dinga yi kenan, dama dan Adam ba a raba shi da wadannan abubuwan. Kai dai ka yi abinka kawai, in kana yi saboda Allah ne. In kana yi saboda mutane ne, sai ka bari in dominsu ne, amma in kana yi domin Allah ne sai ka yi.”
A karshe, Jagora ya rufe da addu’ar, Allah Ya ba mu ladan abubuwan da muke yi, kuma ya kai mu ga kyakkyawan natija.
01/11/2025