DW Hausa

DW Hausa π‹πšπ›πšπ«πšπ’ | π’π‘π’π«π²πž-π’π‘π’π«π²πž | π–πšπ¬πšπ§π§π’ | 𝐍𝐒𝐬𝐑𝐚𝐝𝐒 Shirye-shiryen DW suna isa ga masu sauraro da masu kallo miliyan 86 a ko'ina cikin duniya.

Deutsche Welle, tashar da ke watsa shirye-shiryenta zuwa Ζ™etare, tana gabatar da labarai da rahotanni ta yanar-gizo da rediyo domin baiyanar da yadda Ζ™asashen Turai suke kallon al'amura ga masu sauraro a ko'ina cikin duniya. Burinmu shi ne: "Mu Ζ™arfafa fahimtar yadda Jamus take a matsayin 'yantacciyar Ζ™asa da tushenta yake tare da al'adun Turai, kuma a matsayinta na Ζ™asa mai matsakaicin ra'ayi, ta demokradiyya, mai bin dokokin tsarin mulki da shari'a. Legal notice: http://bit.ly/dwlegalnotice

12/01/2026

Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar ya jagoranci bikin nada sabbin Sarakunan Hausa a kasashen Turai ciki har da Jamus.
An gudanar da bikin ne a fadar Sarkin Hausawan Turai da ke birnin Paris na Faransa a karshen mako.

Bayan da ta kaddamar da gangamin rijistar sabbin magoya baya, jam'iyyar APC ta ce yanzu haka mutane miliyan 2 ne s**a yi...
12/01/2026

Bayan da ta kaddamar da gangamin rijistar sabbin magoya baya, jam'iyyar APC ta ce yanzu haka mutane miliyan 2 ne s**a yi rijistar, kuma tana da burin samun wasu karin magoya baya miliyan 9 kafin nan da makon gobe a cewar Sanata Ajibola Basiru

12/01/2026

Labaran DW na Yau I 12.01.26 I Shirin Yamma

12/01/2026

Shugaban Amurka Donald Trump ya k**a takwaransa na Venezuela Nicolas Maduro ta hanyar amfani da sojojin yakin Amurka.

Matakin Trump na ci gaba da haifar da muhawara a sassa daban-daban na duniya.

Shirin YammaNijar: Sabuwar dokar kasafin kudin Nijar na tayar da kura inda ake hasashen cewar harajin da gwamnati za ta ...
12/01/2026

Shirin Yamma

Nijar: Sabuwar dokar kasafin kudin Nijar na tayar da kura inda ake hasashen cewar harajin da gwamnati za ta tsakura zai karu da kaso mafi tsoka.

Najeriya: Burtaniya za ta mayar wa Najeriya makudan kudaden da aka sace a Najeriya, to amma kuma ta gindaya sharadi na yin aikin gina titin Abuja zuwa Kano da kudaden.

Najeriya: Zanga zanga ta barke a jahar Edo kan yawaitar satar mutane don karbar kudaden fansa da kuma kashekashen gillar jama'a.

Kamaru: An fara shari'ar wadanda aka k**a a yayin zanga-zangar kin jinin sak**akon zaben da ya ba wa Paul Biya nasa

Benin: Turawan zabe sun fara tattara sak**akon tagwazen zabukan 'yan majalisa da na kananan hukumomi da s**a gudana a jiya Lahadi.

Muna dakon ra'ayoyinku

Batu ake na kawata gidajen shugaban kasa Tinubu da mataimakinsa Shettima, inda kasafin wannan shekara 2026 aka ware kusa...
12/01/2026

Batu ake na kawata gidajen shugaban kasa Tinubu da mataimakinsa Shettima, inda kasafin wannan shekara 2026 aka ware kusan naira biliyan biyu don inganta gidajen.

Ya kuke ganin wannan?

Idan dokar ta fara aiki, za a karbi harajin kaso biyar cikin 100 na kudaden da duk wani dan kasar zai aika, haka za a ka...
12/01/2026

Idan dokar ta fara aiki, za a karbi harajin kaso biyar cikin 100 na kudaden da duk wani dan kasar zai aika, haka za a kara cire kudaden haraji ga ma'aikata da kuma sauran harejin da ya wajaba kan 'yan kasar.

To ya kuke ganin wannan matakin?

A daidai lokacin da yake shirin karbar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a jam'iyyar APC, da za ku samu dama ta wayar tarho ...
12/01/2026

A daidai lokacin da yake shirin karbar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a jam'iyyar APC, da za ku samu dama ta wayar tarho da Ganduje, me za ku ce mishi kan siyasar Kano?

Idan komai ya kammala, yarjejeniyar sulhu da 'yan bindiga da za a rattaba hannu kanta a Katsina, za ta saki 'yan ta'adda...
12/01/2026

Idan komai ya kammala, yarjejeniyar sulhu da 'yan bindiga da za a rattaba hannu kanta a Katsina, za ta saki 'yan ta'adda 70 da ke tsare a kurkuku a wani mataki na sasanci da masu dauke da mak**ai.

To amma ku ya kuke ganin wannan yunkuri?

A yayin da saura kiris Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka zuwa APC an kara karfafa matakan tsaro a gaban fadar gwamnatin Ka...
12/01/2026

A yayin da saura kiris Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka zuwa APC an kara karfafa matakan tsaro a gaban fadar gwamnatin Kano

Shin ya kuke kallon wannan lamari?

12/01/2026

Labaran DW na Yau I 12.01.26 I Shirin Rana
RanaDW

Shirin Rana Iran :  Zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa da ta rikide ta koma ta yaki da salon mulki a Iran na kara bazuwa...
12/01/2026

Shirin Rana

Iran : Zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa da ta rikide ta koma ta yaki da salon mulki a Iran na kara bazuwa.

Najeriya : Ana cece-kuce kan matakin gamwantin Katsina na kokarin sakin 'yan bidniga kusan 70 idan aka kulla yarjejeniyar sulhu da su

Nijar : An rusa kungiyoyin agaji kusan 2000 bisa zarginsu da rashin cika ka'idodin zama a Nijar

Uganda : Bashin da ke kan kasar Uganda a halin da ake ya haura dala biliyan 32 kwatankwacin euro biliyan 27.

Muna jiran ra'ayoyinku

Adresse

Bonn
53113

Benachrichtigungen

Lassen Sie sich von uns eine E-Mail senden und seien Sie der erste der Neuigkeiten und Aktionen von DW Hausa erfΓ€hrt. Ihre E-Mail-Adresse wird nicht fΓΌr andere Zwecke verwendet und Sie kΓΆnnen sich jederzeit abmelden.

Service Kontaktieren

Nachricht an DW Hausa senden:

Teilen

Our Story

Deutsche Welle, tashar da ke watsa shirye-shiryenta zuwa Ζ™etare, tana gabatar da labarai da rahotanni ta yanar-gizo da rediyo domin baiyanar da yadda Ζ™asashen Turai suke kallon al'amura ga masu sauraro a ko'ina cikin duniya. Burinmu shi ne: "Mu Ζ™arfafa fahimtar yadda Jamus take a matsayin 'yantacciyar Ζ™asa da tushenta yake tare da al'adun Turai, kuma a matsayinta na Ζ™asa mai matsakaicin ra'ayi, ta demokradiyya, mai bin dokokin tsarin mulki da shari'a. Shirye-shiryen DW suna isa ga masu sauraro da masu kallo miliyan 86 a ko'ina cikin duniya. Legal notice: http://bit.ly/dwlegalnotice