04/11/2024
IBNU MUSDIY
Abinda na rubuta a sama, haka malamai da yawa su ke rubutawa, wato za a yi wa "mimun" ɗin "rufu'a" sai a yi wa "sinun" ɗin "ɗauri". Wasu malam kuma su na rubutawa k**ar haka: IBNU MASDIY, wato za a yi wa "mimun" ɗin "fat'ha". Wasu kuma su na rubutawa k**ar haka: IBNU MUSDIN, wato k**ar dai na farkon kenan, amma a ƙarshe za a yi wa "dalun" ɗin "tanwini" (a sanya masa "kasra" guda biyu maimakon a sanya harafin "ya'un" a ƙarshen sunan).
Sunansa Muhammad bin Yusuf bin Musa bin Yusuf bin Musa bin Yusuf bin Ibrahim bin Abdillahi. Abubakr Al-azdiy, Al-andalsiy. An haife shi a shekara ta 598 ko 599 a wani gari da ake kira Ash a Garnaaɗah da ke Andalus. Babban malamin hadisi ne mahaddaci, limami, mai khuɗuba a Haramin Makka. Ya yi karatu a hannun malaman Tunusia da Dimashƙa da Magrib. Ya zauna a Masar, kuma ya yi karatu a hannun Masarawa.
Mudallisi ne, Ibnu Hajar ya ambace shi a cikin littafinsa "Ɗabkƙaatul Mudallisina", shi ne mutum na 26 a cikin su 33 ƴan martaba ta farko. Haka nan ya siffanta shi da wahami da shi'anci a cikin littafin "Lisanul Mizan" (7/601/7587) k**ar yadda Zahabi ya siffanta shi da hakan a cikin "Al-mizan" (4/73/8346). Malamai da yawa su na siffanta shi da shi'anci da bidi'a (wato ya wuce gona da iri a harkar), domin an ce ya na faɗin maganganu a kan Uwar muminai - Allah ya ƙara mata yarda, amin.
Ya yi rubuce-rubuce ma su yawa, daga cikinsu akwai "Musnadul Garib", wanda ya tattaro mazhabobin malaman hadisi. Ya na da littafin Araba'una Hadis, wanda ya yi magana a kan hadisan aikin hajji da ziyara. Ya na da littafin "Mu'ujam" da ya yi tarjamar malamansa a cikin mujalladi uku manya. Ya na da malamai masu yawan gaske (har da waɗanda ya yi riwaya da ijaza a wurinsu). Ya yi karatu a hannun kakansa Musa bin Yusuf. Daga cikin ɗalibansa akwai Al-hafizud Dimyaaɗi (malamin su Imamuz Zahabi). Haka nan Imamud Daraƙudniy ya na da riwayar hadisansa.
Ya rasu (an kashe shi) a Makka a shekara ta 663 bayan hijira.
Allah ya gafarta masa. Allah ya sa ya na cikin aminci, amin.
,
Cairo, Egypt.
4th Nov., 2024.