24/07/2025
A shekarar 1996, wani yaro dan shekara 8 da ba a san ko waye ba ya sulale daga wajen mahaifiyarsa, ya haura katanga, ya fadi cikin wurin gorilla a gidan namun daji (zoo). Saboda faduwar da ya yi daga tsawon kafa 20 (kimanin mita 6), yaron ya karye hannunsa, sannan ya sami mummunan rauni a fuskarsa.
A cikin wurin, akwai gorilla guda bakwai. Ana san gorilla da tsananin kare yankinsu — suna iya fada har mutuwa don kare danginsu.
Amma, daya daga cikin gorillan, wadda ake kira Binti Jua (ma’ana “’Yar Rana”), ta zo wajen yaron, ta dauke shi a hankali cikin hannayenta, duk da cewa tana da danta karami a bayanta.
Sai ta tafi da shi kusa da bakin wurin da ake shiga, ta tsaya tana jira masu kula da namun daji su zo su karbi yaron. Binti ta mika yaron cikin lumana, sannan ta koma wurin sauran gorilla.
An yaba da abinda Binti ta yi a duniya baki daya, kuma an rika ba ta kyaututtuka na abinci na musamman tsawon makonni. Har yanzu ba a gano sunan yaron ko na mahaifiyarsa ba, amma an tabbatar cewa yaron ya kwana kwana 4 a asibiti.
Masana halayyar dabbobi sun bayyana cewa Binti ta yi amfani da halayen uwa wajen kula da yaron. Wannan yana iya zama saboda tana dauke da danta ƙarami a lokacin, wanda sunansa Koola.