Morganable Hausa

Morganable Hausa Morganable Hausa jarida ne da ke rawaito muhimman batutuwa kan al'amuran yau da kullum, daga wurare maban'banta cikin Nahiyoyi.

Rahotanin mu nazuwa cikin sauti, da hoto mai motsi domin gani da ido....

An hango wani magidanci sanye da hijabi wajen cike form ɗin tallafin da za'a rabawa mata masu shayarwa da suke fama da m...
02/09/2026

An hango wani magidanci sanye da hijabi wajen cike form ɗin tallafin da za'a rabawa mata masu shayarwa da suke fama da matsalar rashin ruwan nono

2027: Zan doke Tinubu a zaɓe, in zama shugaban Najeriya mafi ƙanƙantar shekaru -  AdebisiMoses Adebisi, ɗan takarar shug...
28/08/2026

2027: Zan doke Tinubu a zaɓe, in zama shugaban Najeriya mafi ƙanƙantar shekaru - Adebisi

Moses Adebisi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar DLA, ya ce zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027, tare da zama shugaban Najeriya mafi ƙanƙantar shekaru da aka zaɓa.

Adebisi ya bayyana hakan ne a wata hira da Arise TV ranar Alhamis, inda ya ce ya shiga takarar ne saboda burinsa na taimakawa wajen magance matsalolin Najeriya.

Ya ce DLA ta yi amfani da dabarar “submarine approach” wajen gina tsarin jam’iyyar cikin sirri, kafin ta fito fili domin fafatawa da manyan jam’iyyun siyasa.

A cewarsa, zai haɗa wannan dabara da gangamin neman goyon bayan jama’a a matakin ƙasa domin samun nasara a 2027.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi wa DLA rajista a watan Fabrairun 2026, bayan da jam’iyyu da ƙungiyoyin siyasa 171 s**a nemi a amince da su.

Adebisi ya ce kafin shiga siyasa, ya gudanar da shirye-shiryen tallafa wa mata masu ƙananan sana’o’i da kuma koyar da ɗaliban sakandare dabarun amfani da kwamfuta.

Ya kuma bayyana cewa ya dawo Najeriya daga Amurka ne bayan kiraye-kirayen da wasu ’yan Najeriya s**a yi masa na ya shiga harkokin ƙasar kai tsaye.

Gwamnoni za su rage kudin sufuri ta hanyar amfani da CNGKungiyar gwamnonin Najeriya na shirin bullo da wani shiri na kas...
28/08/2026

Gwamnoni za su rage kudin sufuri ta hanyar amfani da CNG

Kungiyar gwamnonin Najeriya na shirin bullo da wani shiri na kasa da zai rage kudin sufuri ta hanyar amfani da iskar gas din CNG wajen zirga-zirgar jama'a.

A cikin wata sanarwa bayan taron kungiyar da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, kungiyar ta ce jihohi za su taimaka wajen sauya motocin sufuri daga man fetur zuwa CNG, samar da motocin sufuri da kuma abubuwan more rayuwa da ake bukata.

A karkashin shirin, kamfanonin sufuri da za su shiga za su rage kudin da suke karba daga fasinjoji, sakamakon raguwar kudin gudanar da motocin da CNG ke samarwa.

Gwamnan Bayelsa, Douye Diri, ya ce shirin na daga cikin matakan da gwamnonin ke dauka domin rage radadin tsadar sufuri da cire tallafin man fetur ya haifar.

Ya ce rage kudin sufuri zai iya taimakawa wajen saukar da farashin kayan abinci da sauran kayayyaki, saboda kudin jigilar kaya na daga cikin abubuwan da ke kara tsadar kayayyaki.

Kungiyar ta ce har yanzu ba a kayyade ranar fara shirin ba, yayin da ake ci gaba da aiki kan tsarin samar da kudade da yadda za a aiwatar da shi.

2027: Ku tabbatar Tinubu ya samu kuri'un ɗalibai Miliyan 10 - Ministan ilimi ga ƙungiyar NANSMinistan Ilimi, Dr Tunji Al...
28/08/2026

2027: Ku tabbatar Tinubu ya samu kuri'un ɗalibai Miliyan 10 - Ministan ilimi ga ƙungiyar NANS

Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ya bukaci kungiyar daliban Najeriya (NANS) da sauran shugabannin dalibai su tattara kuri’u miliyan 10 domin marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaben shugaban kasa na 2027.

Alausa ya yi wannan kira ne a Abuja yayin wata ziyara da shugabannin NANS da wasu kungiyoyin dalibai s**a kai masa.

Ministan ya ce ci gaba da mulkin Tinubu na da muhimmanci wajen dorewar sauye-sauyen da ake yi a bangaren ilimi, musamman tallafin dalibai, koyar da sana’o’i, gine-ginen makarantu da inganta samun damar shiga manyan makarantu.

Ya bayyana NELFUND a matsayin daya daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatin Tinubu, inda ya ce an ware kusan Naira biliyan 200, kuma sama da dalibai miliyan 1.6 sun amfana.

Ya kuma ce gwamnati na zuba jari wajen gidajen kwanan dalibai, ilimin sana’o’i (TVET), sufuri a jami’o’i, makamashin sabuntawa da tallafawa harkokin kasuwancin dalibai.

A nasa bangaren, Shugaban NANS, Babatunde Afeez Akinteye, ya yaba da shirye-shiryen gwamnati, amma ya bukaci a magance matsalolin tallafin karatu na tarayya, karbar dalibai ba bisa ka’ida ba da kuma matsalolin amincewa da wasu kwasa-kwasai.

Alausa ya tabbatar wa daliban cewa ma’aikatar za ta duba korafe-korafen tare da kara karfafa tsarin karbar dalibai da tabbatar da cewa ba a shigar da su cikin shirye-shiryen da ba su da sahalewar hukumomi ba.

Sanata Barau I Jibrin, ya yabawa Sheikh Jingir Daya cigaba da bawa Shugaba Tinubu goyon baya.  Jingir, Izala
24/08/2026

Sanata Barau I Jibrin, ya yabawa Sheikh Jingir Daya cigaba da bawa Shugaba Tinubu goyon baya.

Jingir, Izala

Bar. Bilya Hamza Karami Ya Jajanta Wa Wadanda Iftila’in ambaliyar ruwa Ya Shafa, Ya Yi Kira Da A Gaggauta Kai AgajiBar. ...
23/08/2026

Bar. Bilya Hamza Karami Ya Jajanta Wa Wadanda Iftila’in ambaliyar ruwa Ya Shafa, Ya Yi Kira Da A Gaggauta Kai Agaji

Bar. Bilya Hamza Karami ya jajanta wa al’ummar da iftila’in ya shafa, tare da yin addu’o’i na musamman ga wadanda lamarin ya rutsa da su.

Bar. Bilya Hamza Karami ya bayyana cewa, “A daidai wannan lokaci na iftila’i, muna fatan Allah Ya sauƙaƙa wahala, Ya mayar da wannan jarrabawa zuwa rahama, kuma Ya sa wannan lokaci ya zama alkhairi.”

Malamin ya ce ya kaɗu matuƙa da abin da ya faru, yana mai bayyana damuwarsa kan halin da al’ummar da lamarin ya shafa ke ciki.

Ya kuma yi kira ga Gwamnati da hukumomin da abin ya shafa, da ƙungiyoyin bayar da agajin gaggawa, da su gaggauta kai ɗauki da tallafi ga al’ummar da wannan iftila’i ya shafa.
Ya ce irin wannan lokaci na buƙatar haɗin kan kowa wajen tallafa wa waɗanda abin ya shafa, da kuma rage musu wahala da radadin da suke fuskanta.

A ƙarshe, Bar. Bilya Hamza Karami ya sake yin addu’ar Allah Ya sauƙaƙa wa waɗanda suke cikin wannan hali, Ya ba su haƙuri da juriyar jarrabawar, sannan Ya mayar da wannan iftila’i zuwa alheri da rahama.

Nijeriya ta samu fiye da Naira tiriliyan 15 cikin watanni 30 a sakamakon cire tallafin mai da sauran sauye-sauye - Gwamn...
19/08/2026

Nijeriya ta samu fiye da Naira tiriliyan 15 cikin watanni 30 a sakamakon cire tallafin mai da sauran sauye-sauye - Gwamnatin Tinubu

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa cire tallafin mai da sauye-sauyen tsarin canjin kudaden waje (FX) sun samar da karin kudaden shiga da s**a kai Naira tiriliyan 15.8 tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025.

Jaridar Punch ta ruwaito gwamnatin ta ce jihohi da ƙananan hukumomi ne s**a samu kaso mafi yawa daga cikin wadannan kudade, sakamakon yadda aka samu karin kudaden da ake rabawa tsakanin matakan gwamnati na kasar.

DA ƊUMI-ƊUMI: Adeleke ya lashe zaben gwamnan Jihar Osun da kuri'u 511,067INEC ta sanar da sakamakon zaben gwamnan Jihar ...
16/08/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Adeleke ya lashe zaben gwamnan Jihar Osun da kuri'u 511,067

INEC ta sanar da sakamakon zaben gwamnan Jihar Osun na daukacin ƙananan hukumomi 30 na jihar.

Bisa sakamakon da hukumar zaɓen ta sanar, ɗan takarar jam’iyyar Accord kuma gwamnan jihar mai ci, Ademola Adeleke, ya samu ƙuri’u dubu 511,067, inda ya doke babban abokin karawarsa, ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu kuri’u dubu 444,815.

Ɗan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Najeem Salaam, shi ya zo na uku da tazarar kuri’u mai yawa, inda ya samu kuri’u dubu 17,180.

Sakamakon da INEC ta bayyana ya nuna cewa Adeleke ya yi nasara a ƙananan hukumomi da dama, ciki har da Ede ta Arewa, Ede ta Kudu, Osogbo, Ife ta Gabas, Ife ta Kudu, Egbedore, Oriade, Odo Otin da Ila.

Oyebamiji kuwa ya samu nasara a wasu muhimman ƙananan hukumomi, ciki har da Irewole, Ife ta Kudu, Isokan, Atakunmosa ta Gabas, Obokun, Ilesa ta Gabas, Boripe da Olorunda.

Bisa jimillar sakamakon da aka gabatar yayin tattara sakamakon zaben na INEC, Adeleke ya samu tazarar kuri’u 66,252 a kan Oyebamiji.

An Jiyo muryan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Engr. Rabiu Musa Kwankwaso, cikin Wani tsohon faifan bidiyo, ya bayyana cewa, ...
14/08/2026

An Jiyo muryan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Engr. Rabiu Musa Kwankwaso, cikin Wani tsohon faifan bidiyo, ya bayyana cewa, a matsayinsa na injiniya, ya kasa fahimtar dalilin da ya sa aka halicci sauro da kuda.

Menene ra’ayinku kan wannan magana?

morganable.com

Address

Thanes Villa, Seven Sister's Road, Finsbury Park
London
N77PH

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Morganable Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Morganable Hausa:

Shortcuts

Share