15/08/2024
Abin Da Ya K**ata Ku Sani Kan Ƙudirin Cire Kudin Harajin Shigo Da Wasu Kayan Abinci A Najeriya
1. Hukumar Kwastam ta Najeriya ta yi amfani da umarnin shugaban kasa Bolo Ahmad Tinubu da nufin rage wahalhalun da 'yan Najeriya ke fuskanta sak**akon tsadar kayan masarufi, inda ta ke farin cikin sanar da Mai Girma Shugaban Tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ta hannun mai girma Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki na Kasa, Olawale Edun wanda ya amince da dokar da ta bada damar cire haraji kan kayan abinci da ake kira Zero Percent Duty Rate (0%) da kuma keɓancewar ƙarin haraji wato VAT akan wasu zaɓaɓɓun kayan abinci.
1. Wannan manufar ta fara aiki daga ranar 15 ga watan Yulin 2024 kuma za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 31st ga Disamba 2024.
2. Wannan matakin na da nufin rage tsadar kayan abinci a kasuwannin Najeriya ta hanyar samar da kayayyakin masarufi mafi sauki ga ‘yan kasa, kuma shirin na zuwa ne a wani bangare na kokarin da gwamnati ke yi na magance kalubalen samar da abinci da kuma tabbatar da cewa kayan abinci na yau da kullun sun isa kuma sun wadaci ɗaukacin ‘yan Najeriya, kuma , yana da mahimmanci a jaddada cewa, duk da cewa wannan matakin na wucin gadi ne, yana da nufin magance matsalolin da ake ciki a halin yanzu, ba kuma zai lalata dabarun da aka dade ana yi don kare manoma na gida da kuma kare masu masana'antuumu na cikin gida.
3. Ya k**ata a lura cewa aiwatar da wannan manufa za ta mayar da hankali ne wajen magance gibin wadata kasa da abinci, ta hanyar shigo da kayan abinci na yau da kullun ba tare da biyan haraji ba, dole ne duk wanda zai amfana da damar ya zamana yana da kamfani Najeriya wanda kuma ya yi aiki na aƙalla shekaru biyar.
Dole ne ya zaman kamfani ne da ya ke bayar da bayanan al'amuransa na shekara-shekara da bayanan kuɗi da biyan haraji da wajibcin biyan albashi na shekara biyar da s**a gabata.
Kamfanonin da ke shigo da buhunan shinkafa, ko hatsi da s**a haɗarda dawa, ko gero suna buƙatar mallakar masana'antar niƙa wacce ke saraffa aƙalla tan 100 a kowace rana, tsawon shekaru huɗu, kuma suna da isasshen filin noma, haka suma masu shigo da masara, alk**a, ko wake dole ne su zama kamfanonin noma da masu mallakar isassun filayen noma ko kuma masana'antar niƙa ko kamfanin sarrafa amfanin gona tare da hanyar sadarwa don amfanin gona.
4. Kayayyakin abinci na yau da kullun da s**a cancanci janye kuɗin harajin sun haɗar da;
ISamfarerar Shinkafa,Dawa, Gero,Masa Masara,Alk**a da wake
5. Ma’aikatar Kudi ta Tarayya za ta ba hukumar Kwatsam jerin sunayen masu shigo da kaya da kuma adadin da aka amince da su don saukaka shigo da wadannan kayan abinci na yau da kullun bisa tsarin wannan manufa. Manufar tana buƙatar a sayar da aƙalla kashi 75% na abubuwan da aka shigo da su ta hanyar musayar kayayyaki da aka sani, tare da rubuta duk ma'amaloli da ajiya.
Kamfanoni dole ne su adana cikakkun bayanan duk ayyukan da ke da alaƙa da hakan, waɗanda gwamnati za ta iya nema don tabbatar da yarda da kuma bibiya, Idan kamfani ya kasa cika wajibcinsa a ƙarƙashin izinin shigo da kaya, zai rasa duk wata dama na cire harajin, kuma dole ne ya biya harajin VAT, da haraji, da kudaden da s**a shafi ayyukan shigo da kaya. Haka kuma wannan hukuncin ya shafi kamfanin da ya fitar da kayan da aka shigo da su ta wannan manufa, ko kuma yayi yunƙurinn sarrafa su a wajen Najeriya.
6. Hukumar Kwastam ta Najeriya karkashin jagorancin Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi MFR, ta jajirce wajen tallafa wa manufofin gwamnati don inganta samar da abinci da inganta tattalin arziki. Hukumar ta bukaci masu ruwa da tsaki da su ba da cikakken hadin kai wajen aiwatar da wannan shirin domin amfanin daukacin ‘yan Najeriya.
Sanarwar daga ABDULLAHI MAIWADA
Babban Sufeto na Kwastam, kana
Jami'in Hulda da Jama'a na ƙasa
Na Kwanturola Janar na Kwastam.
AID Multimedia Hausa