29/10/2025
SHEHU IBRAHIM NIASSE (RTA) YANA CEWA -:
Shehi mai gaskiyar nufi yana ɗaukar mabiyan sa a matsayin ‘yan uwa, ba bayi ba Wannan ne yake jawo albarka a tarbiyya, domin zuciyar da aka girmama tana buɗewar haske
Ku riƙe hanyar Tijjaniyya da ƙarfi da himma kada mutum ya shiga darika da rauni ko gajiyawa, sai da jajircewa daidaitaciyar, niyya, da kuma dagewa da rashin sarewa.
Kalmar Darika tana nufin Hanya zuwa ga Allah ta hanyar tsarkake ruhi darikar Tijjaniyya tana nufin hanyar da Allah ya buɗeta ta hannun maulanmu Shehu Ahmad Tijjani (RTA) domin gyaran zuciyar musulmi da kai su ga ma’rifa sanin Allah da gani da zuciya Shehu Ibrahim Niasse (RTA) yana nuna cewa wannan hanya ba ta son mai wasa Riƙeta da ƙarfi wato Shehu yana nufi da haƙuri da tarin istik**a dauwamammen tsayuwa da kuma ladabi
1. Tarbiyya tana buƙatar Jagora
Ba'a iya kaiwa ga Allah da kai kadai sai ka sami wanda ya kaika ta hanyar sirrin ma’rifa.
2. Shehi mai gaskiyar nufi yana da tausayi, ba wai girman kai ba. Ya koma tsarin masaurata
Saboda haka ne Shehu Ibrahim Niasse (RTA) yake mana nuni da ‘yan uwana ba mabiyansa ba.
3. Darikar Tijaniyya hanya ce ta tsarkake zuciya Riƙonta yana buƙatar gaskiya da daidaitaccen nufi ba surutu ba da kasala.
Wal ABDULILLAH
Baye Niasse Alkairi nee
____SHEHU Ibrahim Niasse Fardun Nee ☝☝