Aminiya

Aminiya Sahihin Shafin Jaridar Aminiya. Jaridar Hausa Ta Rukunin Kamfanin Media Trust; Mamallakin Jaridar Daily Trust, Trust TV Da Kuma Trust Radio.
(397)

Burinmu shi ne: Zama wata babbar kafar yada labarai a duniya wadda za ta samu amincewar jama'a. Bayani kan kamfanin da ke wallafa Aminiya:
Kamfanin Media Trust da ke Abuja ne ya ke wallafa jaridar Aminiya da shafukan Aminiya na intanet. Shi ne kuma ya ke buga jaridar Daily Trust, da Daily Trust on Saturday, da Daily Trust on Sunday, da kuma shafukan intanet na Daily Trust. Adireshin Hedikwatar Kamfanin:
Lamba 20, P.O.W. Mafemi Crescent, Gundumar Utako, Abuja.

Gaskiya da rikon amana suna cikin dalilan da s**a sa tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi fice a siyasar Arewacin...
15/07/2025

Gaskiya da rikon amana suna cikin dalilan da s**a sa tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi fice a siyasar Arewacin Najeriya



Wasu masana da ma makusantan tsohon Shugaban kasar dai suna ganin Arewa ta yi rashi kuma zai yi wuya a samu makwafansa.

Yayin da ake binne marigayin, hankalin wasu 'yan Najeriya ya fara komawa ga yiwuwar samun wanda zai iya maye gurbinsa a fagen siyasar Najeriya.



wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin latsa nan
👇👇👇

Yayin da ake binne tsohon Shugaban Ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari, hankalin wasu ’yan Najeriya ya fara komawa kan yiwuwar samun wanda zai iya maye gurbinsa a fagen siyasar Najeriya.

Wasu mazauna garin Jos, babban birnin Jihar Filato, sun gudanar da sallar jana’iza ta salatul ga’ib ga marigayi tsohon S...
14/07/2025

Wasu mazauna garin Jos, babban birnin Jihar Filato, sun gudanar da sallar jana’iza ta salatul ga’ib ga marigayi tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Wasu mazauna garin Jos, babban birnin Jihar Filato, sun gudanar da sallar jana’iza ta salatul ga’ib ga marigayi tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

APC ta samu nasara a kujeru 375 daga cikin 376 na kansiloli a faɗin jihar, inda jam’iyyar PDP ta samu kujera guda ɗaya.
14/07/2025

APC ta samu nasara a kujeru 375 daga cikin 376 na kansiloli a faɗin jihar, inda jam’iyyar PDP ta samu kujera guda ɗaya.

Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkan kujerun shugabancin kananan hukumomi guda 30 a zaben kananan hukumomin da aka gudanar a Jihar Legas.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai tarbi gawar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Katsina, wanda za a yi wa jana’iza ...
14/07/2025

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai tarbi gawar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Katsina, wanda za a yi wa jana’iza a Daura.

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ne zai tarbi gawar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Katsina, wanda za a yi wa jana’iza a Daura.

Shettima ya isar da gaisuwar ne ga mai ɗakin mamacin Aisha Buhari da kuma ɗan uwansa Mamman Daura.
14/07/2025

Shettima ya isar da gaisuwar ne ga mai ɗakin mamacin Aisha Buhari da kuma ɗan uwansa Mamman Daura.

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima ya yi wa wasu daga cikin iyalan marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta’aziyya a birnin Landan.

An ɗora wa kwamitin nauyin shiryawa da tsara yadda jana’izar ƙasa ta musamman da za a yi wa mamacin.
14/07/2025

An ɗora wa kwamitin nauyin shiryawa da tsara yadda jana’izar ƙasa ta musamman da za a yi wa mamacin.

Gwamnatin Tarayya bisa amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙaddamar da kwamitin da zai jiɓinci jana’izar ƙasa da za a yi wa tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari wanda ya riga mu gidan gaskiya a jiya Lahadi.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana gobe Talata a matsayin ranar hutu saboda ’yan ƙasa su yi jimamin rasuwar tsohon Shugaban Nij...
14/07/2025

Gwamnatin Tarayya ta ayyana gobe Talata a matsayin ranar hutu saboda ’yan ƙasa su yi jimamin rasuwar tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana gobe Talata a matsayin ranar hutu saboda ’yan ƙasa su yi jimamin rasuwar tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.

14/07/2025
Rahotanni na cewa da misalin ƙarfe 2:00 na ranar gobe Talata za a yi jana’izar tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari...
14/07/2025

Rahotanni na cewa da misalin ƙarfe 2:00 na ranar gobe Talata za a yi jana’izar tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.

A jiya Lahadi ne dai aka sanar da rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Yadda garin Daura ya kasance wayam a ranar Litinin saboda alhinin rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Muhammadu Buhar...
14/07/2025

Yadda garin Daura ya kasance wayam a ranar Litinin saboda alhinin rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari.

📸: Ahmed Kabir S/Kuka

Wani gini mai hawa uku da ba a kammala ba a unguwar Sabon Gari da ke Jihar Kano, ya rushe tare da danne mutum 15 da s**a...
14/07/2025

Wani gini mai hawa uku da ba a kammala ba a unguwar Sabon Gari da ke Jihar Kano, ya rushe tare da danne mutum 15 da s**a fake lokacin da ake ruwan sama.

Rahotanni sun tabbatar mutum huɗu sun rasu, yayin da wasu 11 s**a jikkata.

📸: Salim Umar Ibrahim

Address

Dankuni

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aminiya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Aminiya:

Share