15/02/2025
JAGORA (H) YA GABATAR DA JAWABIN NISF-SHA’ABAN A ABUJA
Daga Ofishin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
Da yammacin ranar Juma’a 15 ga watan Sha’aban 1446 (14/2/2025) Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya gabatar da jawabin Nisf-Sha’aban a gaban dimbin al’ummar Musulmi a garin Abuja.
A yayin jawabin wanda ya fara da taya al’umma murnar haihuwar Imam Mahdi (AS) wadda ta auku a rana mai kamar yau shekara ta 255 bayan Hijira, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana haihuwar Imam Mahdi (AS) a matsayin albishir ga wannan al’umma cewa tana da fata. Yace: “Wannan shi ne fatan wannan al’umma, shi ne jigonta.”
Ya bayyana yadda mahukuntan zamanin Imam Hasan al-Askari (AS) wadanda s**a san da lokacin haihuwar Imam Mahdi, har ma da ranar da za a haife shi da lokacin, s**a rika saka ido da tunanin hana aukuwar hakan, amma Allah Ta’ala ya nufi a haife shi ba tare da sun sani ba. Yace: “Don haka s**a kashe Imam Al-askari (AS) da nufin za su hana yiwuwar abin da Allah Ya kaddara na haihuwar Imam Mahdi (AS), amma sai s**a ga magoya bayan Imam Askari suna cikin natsuwa, suna cewa ai Imam yace kaza. Sai suna mamakin dama suna da Imam ne?”
Jagora (H) ya yi bitan yadda mahukunta s**a rika kokarin kashe Imam Mahdi (AS) bayan da s**a gano tabbas an haife shi, amma Allah Ta’ala ya hana su har zuwa sadda Allah Ta’ala Ya shigar da shi Gaiba.
Yace: “In muna magana dangane da Imam (AJ), mukan ce, gaskiya fahimtar Imam ba daga Imam din ne za ka fara fahimta ba. Sai ka san Allah, ka san ManzonSa, sannan za ka san Imam. Kamar yadda Amirulmuminin aka ce masa, ba za ka yi kira izuwa kanka ba? Kace ma mutane ai kai ne Allah Ya umurci ManzonSa ya nasabta? Sai yace a’a, ai shi Manzo shi ne ke kira izuwa ga kansa. - Kowane Manzo zai ce ma mutane ‘Inni Rasulallahi ilaikum’ -, amma Wasiyin Annabi shi baya kira ga kansa. Imaninka da Annabi ne zai sa ka san shi Annabin da ka yi imani da shi, yace bayansa ga wanda za ka bi. In ka bi wannan wasiyin, shi Annabi ka bi, in kuma ka saba wa wannan wasiyin to Annabi ka sabawa.”
Ya kara jaddada cewa: “In mutum ya san Annabi, zai san cewa Annabi (S) ya yi wasiyya. Kuma ya zama wajibinsa ya bi abinda Annabin ya fada.”
Jagora yace: “Ba don wannan hikima ta Allah Ta’ala na wanzar da Sahibul Asr Waz Zaman ba, da sai mu ce babu fata. To amma akwai fata ga wannan al’umma, shi ne jigon wannan al’umma, shi ne fatanta, kuma an masa alkawari, tabbas alkawari ne tabbatacce; zai kafa mulki a doron kasa, ya jiyar da shi dadi, zamani mai tsawo, shi yasa kullum muke addu’ar F***j.”
Da yake tsokaci dangane da zuwan jami’an tsaro wajen taron Nisfu Sha’aban da aka yi da rana, wanda wannan ne ya sabbaba canza muhallin taron zuwa nan don kammalawa, Jagora (H) ya furta cewa: “Wadanda s**a yi abin da s**a yi, da ma sun bari an yi an kare lafiya, ba ma za a san an yi wani taro ba, amma yanzu sun yayyada mana.” Yace: “Mutanen da s**a dauki hotunansu suna abubuwan da s**a yi duk sun yayyada, yanzu ma za su cigaba da yayyadawa ne.
Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “Da ma gwagwarmaya haka take, tsakanin makiya Allah da masoya Allah an dinga fafatawa kenan har ya-zuwa rushewar su (makiya Allah) insha Allah!”
Yace: “Irin wannan bai ma faru a gwamnatin kama-karyar da ta wuce ba, domin muna tarurrukanmu, ko bara mun yi irin wannan taron lafiya lau. Ko kwana 20 da s**a wuce nan an yi taro lafiya lau, wato wanda s**a ga daman dai su zo su kawo hargitsi ne suke neman su kawo hargitsin.”
Shaikh Zakzaky ya jaddada cewa: “Ba wata ka’ida da tace wai in za ka yi taro ka nemi izinin wani. Sai dai idan kana neman kariya, shi ne za ka ce kana neman kariyar dansanda. Amma ba a neman izinin wani wajen yi taro. ‘Freedom of Association’ da ‘Constitution’ ya bayar ya baka wannan damar. Ba ka da yadda wai mutum zai yi taro sai ya fada maka! Ya tambayi wa? A ina? Wace doka tace haka nan”
Ya karkare bayaninsa da albishir da cewa: “Tabbas alkawarin Allah gaskiya ne, watan-watarana Daular Sahibul Asr waz Zaman za ta kafu daram a doron kasa. Jiran lokaci ake yi, kuma mu nan ‘yan zaman jira ne.”
Ya bayyana jiran a matsayin abu mai wahala, tunda aka ce shi ne mafificin aiki. “Za ka dake ne daram akan tafarkin Al-Qa’im (AS), har izuwa bayyanarsa… Amma F***j din tabbas alkawari ne na Allah kuma tabbas Zai cika shi.”
15/Shaaban/1446
14/02/2025