FREE SHAIKH DR AHMAD MAHMUD GUMI

FREE SHAIKH DR AHMAD MAHMUD GUMI La'ilaha illallah muhammadur rasulullah...

09/12/2023

ISLAMIC BANKING: WATA FATAWAR DAGA PENTAGON TAKE FITOWA

Dr Ahmad Gumi

05/12/2023

Taya za'ace an jefa bom kan mutane wani da ya raina muna wayau yace wai kuskure ne

Toh me yasa ba'ayi kuskuren jefawa a bariki ba

28/11/2023
MUHADARA! MUHADARA!! MUHADARA!!!Assalamu Alaikum Warahmatullah!Muna gayyatar daukacin Al'ummar Musulmi na garin Kaduna z...
16/11/2023

MUHADARA! MUHADARA!! MUHADARA!!!

Assalamu Alaikum Warahmatullah!

Muna gayyatar daukacin Al'ummar Musulmi na garin Kaduna zuwa wurin Muhadara da Sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi zai gabatar kamar haka:-

MAIDU'I: SIYASAR KASASHEN MUSULMAI GAME DA RIKICIN FALASTIN

👉 Darasi da ke cikin yakin GAZZA da abin kiyayewa
👉 Kungiyar HAMAS da Gwamnati: jituwa ko rashinsa
👉 Alakar yakin Falastin da bayyanar Mahadi da dawowar Annabi Isah
👉 Igiyoyi guda biyu na ya hudu: suna nan ko sun tsinke

RANA: Lahadi 05 Jimadal Ulah 1445AH (19 NOV. 2023)
WURI: MASALLACIN KWANAR CHANCHANGI
TUDUN WADA KADUNA.
LOKACI: TSAKANIN MAGRIBA DA ISHA’I

Ga wadanda suke wajen Kaduna zasu ga wannan muhadara kai-tsaye In Sha Allah a wannan shafin na Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi da kuma audio ta WhatApp ta wannan lambar +2348038892030

Allah ya bada ikon halarta amin.

Salisu Hassan
08038892030
01 Jimadal Ulah 1445AH
15/11/2023

13/11/2023

Jama'a wallahi sai an dage dayin Azkhar don gujewa masifun rayuwa. Allah ka mana tsari da irin wadannan azzaluman mutanen.

01/11/2023

Wannan bawan Allah shine wanda Allah yama baiwar karban addinin musulunci lokacin da yaron sheikh Zakir Naik ke wa'azi a garin Sokoto.

22/10/2023

Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya gayyaci ambassador Palestine a Nigeria don basu gudumawar da aka nema karkashin masallacin sultan Bello

Allah ya bamu ikon taimakawa su kuma Allah ka kawo masu mafita.

20/10/2023

Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bude gidauniyar taimako don taimakawa al'ummar Palestine. Allah ka bamu ikon taimakawa

SHEIKH DR. AHMAD GUMI YA BUƊE ASUSUN TAIMAKAWA MUTANEN PALESTINEDuk wanda yake son ya taimakawa mutanen saboda wannan ya...
20/10/2023

SHEIKH DR. AHMAD GUMI YA BUƊE ASUSUN TAIMAKAWA MUTANEN PALESTINE

Duk wanda yake son ya taimakawa mutanen saboda wannan yaki da ake yi na Gaza da ke PALASTINE domin siyan musu magani da kayan taimako zai iya aikowa ta wannan account number,

Account Number: 2000886661
Bank: FCMB
Name: Dr. Ahmad Gumi students forum

Allah ya saka da alkairi ya daukaka musulunci da musulmai baki daya.

Salisu Hassan Webmaster
08038892030
20/10/2023

18/10/2023

Malam yaja hankali game da bawa Wike ministan Abuja, wanda yai kira da shugaban kasa Tinubu da ya sauke shi ko su saka kafar wando daya.

17/10/2023

Sharri da illar wayar zamani ga ma'urata!

28/05/2022

Winning or loosing an election is not a reason to mock someone, considering this verse of the holy Quran.

{ قُلِ ٱللَّهُمَّ مَٰلِكَ ٱلۡمُلۡكِ تُؤۡتِي ٱلۡمُلۡكَ مَن تَشَآءُ وَتَنزِعُ ٱلۡمُلۡكَ مِمَّن تَشَآءُ وَتُعِزُّ مَن تَشَآءُ وَتُذِلُّ مَن تَشَآءُۖ بِيَدِكَ ٱلۡخَيۡرُۖ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ }
[Surah Âl-`Imrân: 26]

Yusuf Ali:
Say: "O Allah! Lord of Power (And Rule), Thou givest power to whom Thou pleasest, and Thou strippest off power from whom Thou pleasest: Thou enduest with honour whom Thou pleasest, and Thou bringest low whom Thou pleasest: In Thy hand is all good. Verily, over all things Thou hast power.

Abubakar Mahmoud Gumi:
Ka ce:* "Yã Allah Mamallakin mulki, Kanã bayar da mulki ga wanda Kake so, Kanã zãre mulki daga wanda Kake so, kuma Kanã buwãyar da wanda Kake so, kuma Kanã ƙasƙantar da wanda Kake so, ga hannunKa alhẽri yake. Lalle ne Kai, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne."

Abubakr Bello Zuntu 28/05/2022

Jama'a Koda wannan zancen karya ne ya kamata mu gane cewa daukar doka a hannu ba shine addini ba duba da ayar dake cikin...
19/05/2022

Jama'a Koda wannan zancen karya ne ya kamata mu gane cewa daukar doka a hannu ba shine addini ba duba da ayar dake cikin suratul Hujrat.

{ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِن جَآءَكُمۡ فَاسِقُۢ بِنَبَإٖ فَتَبَيَّنُوٓاْ أَن تُصِيبُواْ قَوۡمَۢا بِجَهَٰلَةٖ فَتُصۡبِحُواْ عَلَىٰ مَا فَعَلۡتُمۡ نَٰدِمِينَ }
[Surah Al-Hujurât: 6]

Yusuf Ali:
O ye who believe! If a wicked person comes to you with any news, ascertain the truth, lest ye harm people unwittingly, and afterwards become full of repentance for what ye have done.

Abubakar Mahmoud Gumi:
Yã kũ waɗanda s**a yi ĩmãni! Idan fãsiƙi* Yã zo muku da wani babban lãbãri, to, ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma.

18/05/2022

Zaben 2023 yakamata muyi aiki da ayar dake cikin suratul Qasas wurin ganin wa zamu zaba

Dalili kuwa shine so da dama mukan yi kuskuren ganin cewa wurin zabe gaskiyar mutun ce take bashi damar zama shugaba

Shugaba ya kamata ya zama mai karfi ba mai rauni ba. Ina nufin ya zama mai capacity sannan kuma ya zama yana da gaskia.

Har gara ku zaba shugaba mai capacity mara gaskia da shugaba mai gaskia mara capacity don kowa yaga halin da muke ciki yanzu a Nigeria no need to talk further.

Saboda raunin shugaba akan al'umma take gaskiyar sa kuma akan shi take.

{ قَالَتۡ إِحۡدَىٰهُمَا يَٰٓأَبَتِ ٱسۡتَـٔۡجِرۡهُۖ إِنَّ خَيۡرَ مَنِ ٱسۡتَـٔۡجَرۡتَ ٱلۡقَوِيُّ ٱلۡأَمِينُ }
[Surah Al-Qasas: 26]

Yusuf Ali:
Said one of the (damsels): "O my (dear) father! engage him on wages: truly the best of men for thee to employ is the (man) who is strong and trusty"....

Abubakar Mahmoud Gumi:
¦ayarsu ta ce, "Yã Bãba! Ka bã shi aikin ijãra, lalle ne mafi alhẽrin wanda ka bai wa aikin ijãra shi ne mai ƙarfi* amintacce."

Abubakar Bello Zuntu

17/05/2022

Majority of those criticizing Dr Ahmad Gumi suna tsammanin bai san me yakeyi bane. Wasu ma suna kafirta shi kawai don sun samu data da waya da kuma Facebook subhanallah!

Yanzu duk mai hankali yasan cewa in wanda ba musulmi ba s**a hana wanda suke musulmi amfani da kayan ALATU da suke kerawa a duniya ina tabbatar muku da cewa addinin ma wlh bazamu iya yadashi ba!

Alokacin da wayar dake hannunka wanda ba musulmi bane s**ayita DATA dakake amfani da ita sune JIRGIN da kake tunanin hawa kaje bautawa Allah a Saudi Arabia sune, kayan da kake sawa duk suke kera su amma kace kai kawai a kashe su! Bacin yanzu a duniya nahiyar turai itace yankin da musulunci yafi yaduwa a duk duniya saboda shi musulunci da Zaman lafia yake yaduwa bada yaki ba. Halaye da koyarwar musulunci kesa suji sha'awar addinin.

Bawani musulmin kirki da zaice in anzagi manzon Allah bazai ji Bakin ciki ba saboda shine Allah ya Aiko mana da musuluncin da muke alfahari dashi Wanda kuma muntabbatar da shine addinin tsira duniya da lahira.

Addinin musulunci ya koya mana tsari da bin doka da maida duk wani al'amari zuwa ga shuwaganni don tsabar tsarinsa baka tafia tafiyar mutun uku Sai ace maka ka nada jagoran tafi saboda Koda wani Abu yazo kuna da shugaba da kuka aminta dashi

Mu dauki sallah kawai tana koya mana biyayya ga shugabanci tunda limami shine shugaba a sallah

Yaku malaman Nigeria musamman masu ganin kisa shine addini wlh ba inda kisa ya zama addini tunda Allah da kanshi yace mana muyi hakuri zamuji suna munana maganganu akan addinin mu toh tabbas zamuji, sai yace mana muyi hakuri muyi taqawa don shine kadai hanyar samun tsira

Allah ka daukaka musulunci da musulmi a duk fadin duniya Ameen.

Abubakr Bello Zuntu 17/05/2022

Address

New Delhi
Delhi
110017

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when FREE SHAIKH DR AHMAD MAHMUD GUMI posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share