13/04/2026
Tafiya mabuÉ—in ilimi
Lokacin da nazo india, na kwashe kusan shekara É—aya abincinsu baya mini daÉ—i, saboda karatu ne yakaini bana yawo gurare daban daban, duk lokacin da muka fita zuwa waji waje bana yadda naci wani abinci har sai na dawo makaranta.
A makaranta kuma akwai masu dafa mana abinci, abincin da suke dafawa a gaskiya shinkafa tafi yawa, saboda kunsan mu yan nigeria muna son shinkafa. Hostel đin namu ba iya yan nigeria bane, international hostel ne yan kasashe daiwa, amma yan nigeria sunfi yawa sosai. Tun zuwana banason abunda zai sa naci abinci awa i waje, saboda ina ga kamar abincin da ake bani a hostel baima kai na wanda zan samu a waje ba. Ashe abun ba haka bane!
Har na taɓa yin rubutu, akan rashin daɗin abincin yan india, ashe abun ba haka yake ba.
Wata rana kawai sa wani ba indiye ya gayyacemu shan ruwa cikin watan ramadan, a gaskiya ban taɓa cin abincin yan india da ya burgeni kamar wannan ba, zan nemu sunan abincin in yi rubutu akai nan gaba. malam flower ce aka gasata kuma aka kawo wata dafaffiyar nama har wajen kala uku, daban-daban. Duk wanda kaci ɗanɗanonsa dabanne. Shiyasa ba'a saurin yanke hukunci.
Ai ina gama ci nace na janye rubutun da nayi a baya🤣
Adam Adam