Al Hadaf Online

Al Hadaf Online Shafi domin amfanin Al'ummar Musulmi.

*ADDU'O'I GA SU JAGORA (H) A NAJAF*Ƴan'uwa Ɗalibai Almajiran Sayyid Zakzaky (H) masu karatu a Najaf, Iraq sun gudanar da...
26/09/2025

*ADDU'O'I GA SU JAGORA (H) A NAJAF*

Ƴan'uwa Ɗalibai Almajiran Sayyid Zakzaky (H) masu karatu a Najaf, Iraq sun gudanar da Addu'o'i ga Jagora Sayyid Zakzaky (H) da maiɗakinsa Umma Zeenah da sauran Ƴan'uwa, kamar yadda s**a saba a kowane sati.
Ana yin Addu'o'in ne a cikin Haramin Amirul Muminina Ali (A.S) da ke birnin Najaf, tare da fatan Allah ya ƙara ma su Sayyid (H) nisan kwana da lafiya da kariya ta musamman, ya kuma ƙwato muna Ƴan'uwanmu da ake tsare dasu bisa Zalunci.

*Najaf Media Forum.*
03/Rabi'usThani/1447
26/September/2025

HANYAR KARBALA:RANA TA DAYA (1)Yanzu haka 'Yan Uwa Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) Masu Gudanar da ibadar Tattakin...
09/08/2025

HANYAR KARBALA:

RANA TA DAYA (1)

Yanzu haka 'Yan Uwa Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) Masu Gudanar da ibadar Tattakin Arba'een Sun Kamo Hanyar Karbala Daga Birnin Najaf Zuwa Birnin karbala A yau Asabar 09_08_2025 inda s**a fara Tattakin Arba’een.

_Iraq Media Forum
09_August_2025
14_Safar_1447H

*YADDA AKA GABATAR DA MUZAHARAR ASHURA A BIRNIN KARBALA*A yau Lahadi 10 ga Muharram 1447 (06/07/2025), Ƴan'uwa Ɗalibai A...
06/07/2025

*YADDA AKA GABATAR DA MUZAHARAR ASHURA A BIRNIN KARBALA*

A yau Lahadi 10 ga Muharram 1447 (06/07/2025), Ƴan'uwa Ɗalibai Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) da ke Iraqi, sun gudanar da Muzaharar Ashura a birnin Karbala mai tsarki.
Muzaharar wadda aka saba gudanar da ita a duk shekara a irin Wannan rana ta Ashura, an fara ta ne daga Funduq Bayariq Sham Muhallin 'yan uwa Ɗalibai na Karbala har Zuwa Haramin Imam Husain (A.S), sannan Haramin Abul Fadl (A.S).
'Ƴan uwa da yawa ne tafe cikin sahu, cike da juyayin musibar da ta samu Imam Husain (A.S) da sauran iyalan gidan manzo a irin wannan rana.

A ƙarshe bayan fitowa daga Haramomin biyu, an rufe Muzaharar a Maqam na Sahibul Asr (A.F), inda Sheikh Abuzarr Khamis ya gabatar da jawabin rufewa sannan aka sallami 'Ƴan uwa.




*Iraq Media Forum.*
10/Muharram/1447
06/July/2025

📸 *Cikin hotuna.*Zaman makokin Abu Abdullah Al-Imam Husain (A.S) daga Najaf, Iraq.A yau ta takwas da fara zaman, kuma it...
05/07/2025

📸 *Cikin hotuna.*

Zaman makokin Abu Abdullah Al-Imam Husain (A.S) daga Najaf, Iraq.
A yau ta takwas da fara zaman, kuma itace rana ta ƙarshe da akayi Khatma, ta kasance ranar Ma'atham ce zalla, inda bayan karanta ziyarar Ashura, aka saurari waƙoƙin juyayi daga bakin Ƴan'uwa mawaƙa;

_Malam Yaqoub Maula.
_Malam Husaini Zaria.
_Da sauransu.




*Najaf Media Forum.*
09/Muharram/1447
05/July/2025

05/07/2025
*ASHURA 1447*📸 NAJAF, rana ta bakwai.Zaman makokin Abu Abdullah Al-Imam Husain (A.S) wanda Ƴan'uwa ɗalibai almajiran Say...
04/07/2025

*ASHURA 1447*

📸 NAJAF, rana ta bakwai.

Zaman makokin Abu Abdullah Al-Imam Husain (A.S) wanda Ƴan'uwa ɗalibai almajiran Sayyid Zakzaky (H) suke gudanarwa a Najaf, a yau an shiga rana ta bakwai da fara wannan zama.
Bayan karanta ziyarar Ashura, an saurari jawabi daga bakin Sheikh Murtadha Malumfashi.
Bayan jawabinsa, sai mawaƙa s**a gabatar da Ma'atham kamar yadda aka saba.




*Najaf Media Forum.*
08/Muharram/1447
04/July/2025

*ASHURA 1447*📸 NAJAF, rana ta shida.A cigaba da zaman makokin Abu Abdullah Al-Imam Husain (A.S) wanda Ƴan'uwa ɗalibai al...
03/07/2025

*ASHURA 1447*

📸 NAJAF, rana ta shida.

A cigaba da zaman makokin Abu Abdullah Al-Imam Husain (A.S) wanda Ƴan'uwa ɗalibai almajiran Sayyid Zakzaky (H) suke gudanarwa a Najaf, a yau an shiga rana ta shida da fara wannan zama.
Bayan karanta ziyarar Ashura, an saurari jawabi daga bakin Sheikh Ibraheem Usman Na'ibi Kano.
Bayan jawabinsa, sai mawaƙa s**a gabatar da Ma'atham kamar yadda aka saba.




*Najaf Media Forum.*
07/Muharram/1447
03/July/2025

02/07/2025

*ASHURA 1447*

NAJAF, rana ta biyar

Cigaba da zaman makokin Abu Abdullah Al-Imam Husain (A.S) a birnin Najaf dake Iraqi, wanda Ƴan'uwa Ɗalibai Almajiran Sayyid Zakzaky (H) suke gudanarwa.
A yau rana ta biyar, Sheikh Nazifi Musa Sara ne ya gabatar da jawabi, bayan nan sai Ma'atham daga mawaƙa. A ƙarshe aka rufe taron da Addu'o'i kamar kullum.




*Najaf Media Forum.*
06/Muharram/1447
02/July/2025

*ASHURA 1447*NAJAF, rana ta biyarCigaba da zaman makokin Abu Abdullah Al-Imam Husain (A.S) a birnin Najaf dake Iraqi, wa...
02/07/2025

*ASHURA 1447*

NAJAF, rana ta biyar

Cigaba da zaman makokin Abu Abdullah Al-Imam Husain (A.S) a birnin Najaf dake Iraqi, wanda Ƴan'uwa Ɗalibai Almajiran Sayyid Zakzaky (H) suke gudanarwa.
A yau rana ta biyar, Sheikh Nazifi Musa Sara ne ya gabatar da jawabi, bayan nan sai Ma'atham daga mawaƙa. A ƙarshe aka rufe taron da Addu'o'i kamar kullum.




*Najaf Media Forum.*
06/Muharram/1447
02/July/2025

*ASHURA 1447*NAJAF, rana ta huɗu.Hotunan zaman makokin Abu Abdullah Al-Imam Husain (A.S) wanda Ƴan'uwa Ɗalibai Almajiran...
01/07/2025

*ASHURA 1447*

NAJAF, rana ta huɗu.

Hotunan zaman makokin Abu Abdullah Al-Imam Husain (A.S) wanda Ƴan'uwa Ɗalibai Almajiran Sayyid Zakzaky (H) suke gudanarwa a Najaf.
A yau rana ta huɗu, an saurari jawabi daga bakin Sayyid Alhassan Sufi. Bayan nan sai Ma'atham da mawaƙa s**a gabatar.




*Najaf Media Forum.*
04/Muharram/1447
01/July/2025

Address

Najaf

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al Hadaf Online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share