25/01/2026
Wlhy Seda nayiwa tsohon nan kuka Amma Ba Damuwa Arxiqin lahira shine Arxiqi Baba.😭
Wannan bawan Ãllah a kastina yake kullum da Sassafe Seya kawo Wannan yalon bakin nan gurin domin siyarwa kuma bakowa ke siya ba shide Yyi sana'a kuma koda be Siyar ba gobe xeqara dawowa Dashi,
Nasan dayawa Masu ganin irin stofafin nan wani lkc har abinda suke siyarwa ya lalace Amma xe iya xowa yakasa Sbd stufa.
Haka wani bawan Ãllah yaje ake cemasa baba yalo ake siyarwa!?? wlhy da qarfi yatashi domin yaga xa'a masa ciniki se bawan Ãllah yace Baba koma ka xauna seya koma ya xauna yake cemasa baba nawa yalo Tom kunsan de irin stofafin nan harna goma suna badawa cinikin ashirin ma dadi yakemusu.
Se Akace baba nawa duka yalon abin yabashi mamaki yace Duka!?😳 Akace ehh yace dari biyar!🥹 Allah sarky abin dari biyar ayi sati ana kai tallar sa.😭
Aeko yace baba nasiya baba yaji dadi an siye yalon sa kawae bawan Ãllah nan yaciro 10k yace baba gasu dubu goma😥 kae Jama'a baba yarasa ina xesa Kansa sbd farin ciki, seya fara qirga kudin seya sunkuyar da kansa wlhy sunkuyar da kansa din nan yabani tausayi irin kamar yayi kukan Nan😭💔
Dan girman Allah idan mun hadu da irin stofafi nan bakin hanya idan da kudi hanunmu muna riqa siyan kayansu Koda bama da Buqatar Hakan Idan kuma xamu basu Kyauta mubasu batare da mun kar6i abinda suke siyarwa ba.
Komu Kar6a muyi sadaqa idan sukaga bbu Kayan sunfi farin ciki Sosae. Ãllah Kamana Arxiqn da xamu Temakawa mabuqata ameen