Rabe Issa stores

Rabe Issa stores Domin ganin bidiyoyinmu a kowane lokaci,

ku bi shafin Rabe Issa Stores. Follow • Like • Share

Nagode da dukkan followers ❤️

Rabe Issa stores

Iran ta Bayyana cewa ta lalata jirgin Amurka F-35 mafi hadari. BBI HausaKafofin yaɗa labarai na Iran, masu alaƙa da Isla...
03/04/2026

Iran ta Bayyana cewa ta lalata jirgin Amurka F-35 mafi hadari. BBI Hausa

Kafofin yaɗa labarai na Iran, masu alaƙa da Islamic Revolutionary Guard Corps, sun fitar da hotuna da suke ikirarin cewa ragowar wani jirgin yaƙin Amurka ne nau’in F-35 Lightning II da aka harbo a tsakiyar ƙasar Iran
Rabe Issa stores

A ranar Alhamis Iran ta bayyana cewa Mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a bude ga jiragen ruwa na duniya amma "a...
02/04/2026

A ranar Alhamis Iran ta bayyana cewa Mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a bude ga jiragen ruwa na duniya amma "a rufe" ga maƙiyanta da sansanoninsu na yankin.

Ali Akbar Velayati, mai ba da shawara ga Jagoran Addini na Iran Mojtaba Khamenei, ya fada a cikin wani jawabi da ya yi a shafin sadarwar yanar gizo na X cewa sakamakon yakin zai dogara ne da sharuddan da Iran za ta gindaya maimakon abin da ya bayyana a matsayin "mafarkin" maƙiyanta.

"Mashigar Hormuz a bude take ga duniya, amma za ta ci gaba da kasancewa a rufe ga maƙiyan mutanen Iran da sansanoninsu a yankin," in ji shi

Babban Janar na rundunar sojin Iran, Major Ganar Hatami, ya ce:“Idan Amurka da Isra'ila s**a kaddamar da hari ta kasa, k...
02/04/2026

Babban Janar na rundunar sojin Iran, Major Ganar Hatami, ya ce:

“Idan Amurka da Isra'ila s**a kaddamar da hari ta kasa, kada a bar ko guda daga cikinsu ya tsira da rai.”

Zamu rushe tsarin kariyar Isra'ila da Amurka cikin mako biyu masu zuwa a Yankin Gabas ta tsakiya”— Dakarun Iran. Iran ta...
02/04/2026

Zamu rushe tsarin kariyar Isra'ila da Amurka cikin mako biyu masu zuwa a Yankin Gabas ta tsakiya”— Dakarun Iran.

Iran ta yi ikirarin cewa za ta iya lalata muhimman tsarin kariyar Amurka da Isra’ila cikin makonni biyu kacal. Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.

Mahukunta a Tehran sun bayyana cewa hare-haren da suke ci gaba da kaiwa ta hanyar makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuki sun riga sun rage ƙarfin tsarin kariyar abokan gaba. A cewarsu, wannan ci gaba na iya kai ga rushewar wasu muhimman na’urorin gano hari da kariyar sama idan aka ci gaba da matsin lamba.

Sai dai duk da wannan ikirari, rahotanni daga yankin sun nuna cewa har yanzu ana samun nasarar dakile wasu daga cikin hare-haren, lamarin da ke nuni da cewa tsarin kariyar na ci gaba da aiki, kodayake ana iya samun ƙalubale

Kungiyar mayakan Houthis a Yemen ta bayyana cewa ta kai hari da makami mai linzami kan Isra’ila, inda ta ce harin ya gud...
01/04/2026

Kungiyar mayakan Houthis a Yemen ta bayyana cewa ta kai hari da makami mai linzami kan Isra’ila, inda ta ce harin ya gudana ne tare da hadin gwiwar Iran da kuma kungiyar Hezbollah.

A cewar sanarwar da kakakin rundunar Houthis ya fitar, sun ce harin na cikin wani shiri na hadin gwiwa da kawayensu domin kai farmaki kan wasu muhimman wurare a Isra’ila.

Kungiyar ta kuma yi gargadi cewa a shirye take ta kara tsananta hare-hare idan Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a yankin Gabas ta Tsakiya
ATP Hausa

'Birtaniya ba za ta shiga yaƙi da Iran ba duk da matsin lambar Trump'Ƙarin bayani  Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ...
01/04/2026

'Birtaniya ba za ta shiga yaƙi da Iran ba duk da matsin lambar Trump'

Ƙarin bayani

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya ce ƙasarsa ba za ta shiga yaƙi da ƙasar Iran ba, duk da matsin lambar da yake fuskanta daga shugaban Amurka, Donald Trump.

Da yake magana a wani taron manema labarai a yau, Starmer ya bayyana cewa akwai matsin lamba mai yawa a kansa domin ya sauya matsayinsa kan shiga yaƙin, amma ya jaddada cewa ba zai canza wannan matsaya ba.

Ya ƙara da cewa a matsayinsa na Firaminista, zai ci gaba da yanke shawara ne bisa muradun ƙasar Birtaniya.

Lokacin da aka tambaye shi ko yana ƙara kusantar Turai sakamakon dangantakar da ta yi tsami da Trump, Starmer ya ce ba zai zaɓi tsakanin Amurka da Turai ba.

Ya ce, “Yana da muhimmanci a gare mu mu ci gaba da samun kyakkyawar alaƙa da Amurka da kuma Turai baki ɗaya.”

A nasa ɓangaren, Trump ya shaida wa jaridar The Telegraph cewa yana duba yiwuwar ficewar Amurka daga ƙungiyar NATO da muhimmanci.

Trump ya sha s**ar NATO da kuma Birtaniya kan rashin shiga yaƙin da Amurka ke yi da Iran

20/03/2026
03/03/2026

Jirage biyu marasa matuƙa na ƙasar Iran sun kai hari a Ofishin Jakadancin Amurka da ke birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya da sanyin safiyar Talata, 3 ga watan Maris, inda s**a haddasa gobara. Hukumomin Amurka sun umarci 'yan ƙasarsu da ke biranen Riyadh, Jeddah da Dhahran su nemi wurin ɓuya a inda suke.

28/02/2026

Ministan Tsaron Isra'ila Israel Katz ranar Asabar ya ce ƙasarsa ta kai "hare-haren kandagarki" a Iran, saboda abin da ya kira barazanar da take yi ga tsaron ƙasarsu.

25/02/2026

Barka da safiya
























21/02/2026

Sannu da tashin a suba

Adresse

Rabe Issa Stores
Belbédji

Site Web

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Rabe Issa stores publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Partager