07/08/2025
MATASHIYA/NASIHA:
Idan ka zamanto Mutumin kirki,mai kyakkyawar manufa a rayuwa, sai Allah ya hadaka da mutanen kirki masu kyawawan manufofi irin naka, domin samun cikar burinka.
Koda ka samu matsala da wani daga cikin Jama'arka, kar ka fidda tsammanin alkhairi daga gareshi. Watakil idan kayi masa uzuri ka kyautata zato gareshi, ka yafe masa, sai alkhairi ya biyo bayan hakan.
Mutanen kirki anan duniya, sune ma'abotan alkhairi a lahira. Kuma mutum ba ya zama mutumin kirki har sai tunaninsa da ayyukansa duk sun zama na kirki.
Kayi kokari ka chanza rayuwar wani daga mummuna zuwa kyakkyawa ta hanyar nasiha, shawarwari, ko taimako, ko agaji, ko kuma ta dalilin afuwarka.
Duk abinda muke furtawa da aikatawa na alheri zamu samu sakamakon sa a wa wajen Allah ranar alƙiyama
Allah ya bamu dacewa aduniya da lahira, amin
Sheikh Aliyu said gamawa hafizahullah