Muryar Nijar TV

Muryar Nijar TV Muryar Nijar TV ,kafa ta farko akan intanet a Nijar dake yaɗa labarai a cikin harsunan ƙasar (Hausa, zabarmanci...) NIAMEY-NIGER+22799483017
(1)

La première webtv d'information general au Niger ,en langues Local(Hausa,Zarma...)

31/12/2025

Bulletin des activités des FDS du 22 au 28 décembre 2025

Nijar da ƙawayen na ta ,sun ɗauki wannan matakin ne bayan da ƙasar Amurika ta saka Nijar cikin jerin ƙasashen da ta hara...
31/12/2025

Nijar da ƙawayen na ta ,sun ɗauki wannan matakin ne bayan da ƙasar Amurika ta saka Nijar cikin jerin ƙasashen da ta haramta wa takardar biza.
Waɗannan matakan ana ganin tamkar sun ƙara dako da tsamin dangantakar diplomasiya tsakanin AES da Amurika.

Mu ƙaru da juna. Wane irin ta'asiri ku ka sani ke da sarauta ko sarakunan gargajiya a Nijar?
30/12/2025

Mu ƙaru da juna.
Wane irin ta'asiri ku ka sani ke da sarauta ko sarakunan gargajiya a Nijar?

Yan majalisar riƙon ƙwarya a Nijar sun shawarci gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta mayyar da ranakun hutun ma'aikata a ƙasa...
30/12/2025

Yan majalisar riƙon ƙwarya a Nijar sun shawarci gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta mayyar da ranakun hutun ma'aikata a ƙasar a ranar juma'a da Lahadi ,yayin da asabar za ta kasance ranar aiki.

An fara wani babban taron musanyan yawu tsakanin matasa da dattawan ƙasar Nijar a birnin Yamai.Taron na kwanaki biyu da ...
30/12/2025

An fara wani babban taron musanyan yawu tsakanin matasa da dattawan ƙasar Nijar a birnin Yamai.

Taron na kwanaki biyu da aka fara a yau talata 30/12/25 ya mayyar da hankali akan wasu mahimman batutuwan gina ƙasa .Matasan ƙasar da mahukunta,tsofaffin shugabannin ƙasa, sarakunan gargajiya, da malaman addini ne s**a taru a zauren taron dan tattauna

Mahimman batutuwan da s**a haɗa da kishin ƙasa,haɗin kan al'umma, jagoranci, zamantakewa, da kuma tattalin arziki ne taron zai tattauna akai

Manufar wannan taron ita ce sanin inda aka fita da kuma inda za'a je domin samun kyakkyawan tunanin gina ƙasa a cikin haɗin kai.

Tun a ranar 15 ga watan septemban 2025 ne aka garƙame Ibrahim Yacouba a gidan yarin Oullam,bayan da hukumomin Shari'a a ...
30/12/2025

Tun a ranar 15 ga watan septemban 2025 ne aka garƙame Ibrahim Yacouba a gidan yarin Oullam,bayan da hukumomin Shari'a a Yamai s**a ce ana zargin shi da hannu a wata badaƙalar laifin kisan kai domin yin tsafi da aka k**a wani Boka da aikatawa.

Alƙalin da ke kula da wannan shari'ar,ya wanke sananen ɗan siyasar a Nijar na jam'iyyar kishin ƙasa ,Ibrahim Yacouba.

Amma wasu makusantan na Yacouba sun sheda mana cewa ,yanzu haka matakin da babban mai shigar da ƙara na gwamnati(procureur) zai ɗauka kawai suke jira,suna masu sa ran a sake shi a cikin gaggawa .

Tun dai farkon wannan al'amarin, wasu ƙungiyoyi da gidajen jaridu sun sha nanata cewa waɗanda ake zargin da wannan laifin,ba su ambaci suna Ibrahim Yacouba ba a cikin wannan badaƙalar.

Fitaccen ɗan siyasar a Nijar,kuma magoyi bayan hamɓararen shugaban ƙasa Mohmed  Bazoum, Alhassan Intinicar, ya faɗi haka...
30/12/2025

Fitaccen ɗan siyasar a Nijar,kuma magoyi bayan hamɓararen shugaban ƙasa Mohmed Bazoum, Alhassan Intinicar, ya faɗi hakan ne cikin wani rubutun da ya wallafa a shafukan sada zumunta, inda
yake iƙirarin cewa tun ba a yau ba yake bai wa Nijar gudunmuwa ta fannoni daban-daban ,ciki har da fannin tsaro.

Intinicar ya ce ko a yanzu a shirye yake ya shiga aikin ɗamara dan baiwa ƙasarsa ta Nijar gudunmuwa a fannin tsaro.

Wannan furucin na sa na zuwa ne bayan da mahukuntan ƙasar Nijar s**a ƙirƙiri wata dokar da za ta tilasta wa ko wane ɗan ƙasa bai wa ƙasar kariya ,duk zuwa yanzu ba'a fayyace abinda wannan ƙudurin ke nufi ba a kai tsaye.

Shin kun shirya shiga aikin soji dan ba wa ƙasarku kariya?

Shugaba TIANI da takwaransa na ƙasar Turkiyya ERDOGAN sun tattauna ta wayar tarho  a yau Litinin.  Fadar shugaban Nijar ...
29/12/2025

Shugaba TIANI da takwaransa na ƙasar Turkiyya ERDOGAN sun tattauna ta wayar tarho a yau Litinin. Fadar shugaban Nijar ta ce ɓangarorin biyu sun tattauna wasu muhimman batutuwa ne akan kyakkyawar hulɗa,abubuwan ƙaruwa da cigaban ƙasashen biyu

Yan sandan farin kaya sun tsare Sarkin SOKORBÈ a ofishinsu bayan da ma'aikatar cikin gidan Nijar ta dakatar da shi daga ...
29/12/2025

Yan sandan farin kaya sun tsare Sarkin SOKORBÈ a ofishinsu bayan da ma'aikatar cikin gidan Nijar ta dakatar da shi daga muƙamin sa, saboda wasu kalaman da ya yi na zargin an tafka rashin adalci a kokowar da ta haɗa Issaka Issaka na Dosso da Noura Hassan na Tahoua

Ya na daga cikin fitattun yan kokowar da s**a yi suna sosai a Nijar .Idan kun gane shi,ku rubuta mana sunan shi
29/12/2025

Ya na daga cikin fitattun yan kokowar da s**a yi suna sosai a Nijar .
Idan kun gane shi,ku rubuta mana sunan shi

Cikin wani faifan murya da aka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta ne ,aka ji Sarkin na Sokorbé mai martaba MOUSSA MADO...
28/12/2025

Cikin wani faifan murya da aka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta ne ,aka ji Sarkin na Sokorbé mai martaba MOUSSA MADOUGOU DAKAOU,na furta wasu kalamai da mahakuntan ƙasar s**a ce, na baraza ga zaman lafiya da haɗin kan al'umma.

A cikin kalaman na sa ,sarkin, ya yi zargin cewa ne ,an tafaka rashin adalci akan batun kokowar da NOURA HASSAN na Tahoua, ya kayar da ISSAKA ISSAKA na Dosso.

Ƙoƙarin mahukunta na ganin waɗannan kalaman ba su tada ƙura a tsakanin yan ƙasar ba ne ya sa ,gwamnatin ƙasar ta fuskar ma'aikatar cikin gida ta ɗauki matakin dakatar da sarkin daga muƙaminsa ,kafin gama ɗaukar matakan da s**a k**ata.

Dalilai diyawa ne ofishin ministan cikin gidan ya dogara da su wajen ɗaukar wannan matakin, musamman ma irin ta'asirin da ke da SARKI a cikin al'umma, kuma a ce ya yi irin wannan furucin.

Noura Hassan ya kada Zakirou Zakari a wasan ƙarshe na kokowar gargajiya ta bana.
28/12/2025

Noura Hassan ya kada Zakirou Zakari a wasan ƙarshe na kokowar gargajiya ta bana.

Adresse

Niamey

Téléphone

+22793022642

Site Web

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Muryar Nijar TV publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Contacter L'entreprise

Envoyer un message à Muryar Nijar TV:

Partager