20/07/2025
MAGANI A GONAR YARO.!
:
:
ZAN TABBATAR MAKA DA LALLAI MANZON
ALLAH (SAW) SHINE FARKON "MU'ASSASIN"
DARIKA"
Zan Riskar Dakai, Amsan Tamboyin Ka Cikin
Kur'ani Da Hadisi Kamar Yadda Ka Buqata,
Idan Har Ka Bini A Tsanake.
:
:
GA CHALLANGE, GAMI DA TAMBAYAR DA WANI
BAWAN ALLAH, YAYI MIN COMMENT DA SU
KAMAR HAKA.
Shafi'u Sani
Dukwanda yamutu abatijjane ba
amusulmiba tabbas yayi hasara, Allah yace
(WALATAMUTUNNA ILLAH WAANTUM
MUSLIMUN) kuma wai don Allah, wacce
dariqa annabi da sahabbansa s**ayine?
Shin tijjaniyya s**ayi? ko kadiriyya ko
ahmadiyya ko shazaliyya ko
naqashebandiyya ko arusiyya ko burhaniyya
s**ayi? shin mawai, cikin wayannan dariqu
waccece annabi yazabama alummarsa yace
sushiga? DON ALLAH MALAN KAAMSAMIN
TAMBAYOYINNAN KURANI DA HADIS. Like ·
ALHAMDULILLAH.
* Amsar Tambayar Ka Bisa Qalubalen Ka Na
Farko Karkashin Wannan Aya 102 A Ali
Imrana.
ﻭَﻟَﺎ ﺗَﻤُﻮﺗُﻦَّ ﺇِﻟَّﺎ ﻭَﺃَﻧْﺘُﻢْ ﻣُﺴْﻠِﻤُﻮﻥَ
* Ai Kasani, Ba Yadda Mutum Zai Zamo,
Batijjane, Har Sai Ya Kasance Cikekken
Musulmi, Mai Cikekkiyar Sallamawa ALLAH
(Swt),
Sannan Ba Ta Yadda Mutum Zai Kasance Mai
Sallamawa ALLAH Har Sai Ya Kasance Mai
Riko Da Bibyar Sharuddan Muqaman Addinin
ALLAH Guda 3.
A Muqamul Islam, Tijjanawa, Sun Kadaita
ALLAH Bisa Haqiqar Kadaitawa (Tauhidi),
Sannan Duk Abinda Yazo Na Ibadu Cikinta,
Kamar Sallah, Azumi Zakka, Aikin Hajji To
Sunayi Shin Aikin Wanne Addini Ne Wannan?
Sannan Kuma, A Mukamul Imani, Tijjanawa
Sunyi Imani Da Sharuddan Ta Guda Shida
Shin Aikin Wanne Addini Ne Wannan?.
* Muqamul Ihasan Kuwa, Wannan Dama
Sansanin 'Yan Gatace, Anan Yan Darika S**ai
Sansani, Kuma Anan S**a Tare.
* IDAN BA TIJJANE YA MUTU A WANNAN
TAFARKI, SHIN BAI KASANCE MUSULMI BA.?
Amsar Tambaya Ta Biyu.
Kafin Kayi Wannan Tambaya Akan Me Yasa
ANNABI (SAW) Da Sahabban Sa, Basuyi Daya
Daga Darikun Da Ka Zayyano Ba, To Ya
Kyautu, Kasoma Tambayar Kanka Cewa.
* Shin Me Yasa ANNABI (SAW) Da Sahabban
Sa, Basubi Mazhabobi Ba, Kamar Malikiyya,
Shafi'iyya, Hambaliyya, Hanafiyyy