17/07/2025
Tinubu: Buhari Ya Rayu da Gaskiya, Ya Mutu Cikin Girma, Najeriya Za Ta Ci Gajiyar Alƙairansa
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya jagoranci wani zama na musamman na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa domin girmama tsohon Shugaban Ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari, GCFR, wanda ya rasu a kwanan nan, yana mai bayyana shi a matsayin mutum mai gaskiya, dattijo na kwarai, kuma gwarzon da Najeriya ba za ta manta da shi ba.
A cikin jawabin sa, Shugaba Tinubu ya bayyana Buhari a matsayin jagora da ya kasance misali na kwarai a rayuwar siyasa da shugabanci, wanda bai yarda da almubazzaranci ko yabon kai ba, kuma bai taɓa rungumar mulki domin jin daɗin kansa ba.
“Shi ne na farko a cikin mayaƙa lokacin yaƙi, na farko a cikin ‘yan ƙasa a lokacin zaman lafiya, kuma na farko a cikin zukatan al’umma ba tare da son zuciya ba. Rayuwarsa ta kasance wa’azi ga masu ɗabi’a marasa kyau, kuma mafaka ga masu ɗabi’a ta gari,” in ji Tinubu.
Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa ko a lokacin mulkinsa da bayan kammala wa’adinsa, Buhari bai taɓa nuna son mulki ko shisshigi ba, inda ya jaddada cewa marigayin ya koma Daura cikin nutsuwa, ba don akwai wani rinjaye akan sa daga gwamnati ba.
Ya kara da cewa: “Rayuwarsa ta fi nuna kishin ƙasa a aikace fiye da surutai. A fagen mulki, ya kasance mai biyayya ga ƙasa. Bayan mulkinsa, ya koma rayuwar gida cikin sauƙi, ya bar ci gaba da mulki ga waɗanda s**a gada.”
“Rayuwar Buhari ta shafe fiye da shekaru 50 a hidimar ƙasa, daga kasancewar sa gwamna, zuwa shugaban mulki na soja, zuwa shugaban ƙasa na mulkin dimokuraɗiyya, zuwa jagoran amana a hukumar PTF.” Inji Tinubu.
A karshen jawabin nasa, Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyya ga Hajiya Aisha Buhari da iyalansa gaba ɗaya, tare da gwamnatin Jihar Katsina da al’ummar Najeriya, yana addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya ba shi Aljannatu Firdaus.
Shugaban Ƙasa ya kuma yaba da yadda Kwamitin Jana’iza, ƙarƙashin jagorancin George Akume da Gwamna Dikko Radda, s**a shirya jana’izar Shugaba Buhari.