mujallarmanagarciya

mujallarmanagarciya Mujalla ce da ke bayar da labarai domin samun faɗakarwa da halin da ƙasa ke ciki.

15/10/2023
Ni Da Gwamna Mun Tattauna Wasu Dubaru Da Za Mu Bi Don Kawo Zaman Lafiya a Gabascin Sakkwato----Sanata Lamido
01/10/2023

Ni Da Gwamna Mun Tattauna Wasu Dubaru Da Za Mu Bi Don Kawo Zaman Lafiya a Gabascin Sakkwato----Sanata Lamido

Bayan Kashe Wanda Ake Zargi Ya Zagi Annabi: Gwamnan Sakkwato Ya Fadi Matsayarsa
25/06/2023

Bayan Kashe Wanda Ake Zargi Ya Zagi Annabi: Gwamnan Sakkwato Ya Fadi Matsayarsa

Ahmed Aliyu ya Kara da cewa mutanensa nada matukar soyayya da kauna ga Annabin Rahama ta yadda ba za su yi wasa da taba janibinsa ba, kan haka ya bukaci alumma dasu mutunta manzon Allah SAW.

Soyayyar Rakiya Da Breaker Ni Ganau Ba Jiyau Ba, Domin Har Zuwa Gidansu Take Tana Taya Mahaifyarsa Aikace-Aikace Don Kam...
02/04/2023

Soyayyar Rakiya Da Breaker Ni Ganau Ba Jiyau Ba, Domin Har Zuwa Gidansu Take Tana Taya Mahaifyarsa Aikace-Aikace Don Kamun Kafa

Daga Mu'az Sulaiman Sa'eed

Da fari dai ban so na saka baki na akan maganar nan ba kwata-kwata, saboda a wajena, ba kowane batu ne ya ke buƙatar tankawa ba. To amma abubuwa biyu sun ja hankali na ƙwarai da gaske. Abu na farko shi ne tausayin da Rakiya ta bani, ta kuma bawa mutane da yawa bayan kallon hirar su da na yi da Hadiza Gabon. Sai abu na biyu yadda na ga wasu na alaƙanta cewa wannan masoyin ba wani ba ne illa Hamisu Breaker.

Wannan gaɓar ta biyu ta yi daidai da tunanina bayan kammala kallon hirar da muka yi tare tawa masoyiyar da bamu wahalar da juna ba😃. Ina gama kalla, nace mata, Allah ya sa ba BREAKER ta ke nufi kuwa. Ummu Hanan tace anya kuwa?

Mu dawo maganar mu. A ƙarƙashin wannan gaɓa ta biyu ina da abubuwan faɗa dozin guda kamar haka:

1. Ban yi wannan rubutun domin aibata wani ko bawa wani kariya a cikin su biyun ba. Illa dai kawai na ɗan san wani abu dangane da alaƙar su biyun.

2. Hamisu maƙobcin mu ne a unguwar Dorayi, domin gida ɗaya ne tsakanin mu da gidansu, don haka tamkar ƙani ya ke a wajena tun bai kai shekara biyar a duniya ba. Bayan kasancewarsa maƙobcin kuma tamkar ƙani, Hamisu ɗalibi na ne na tsawon shekaru kafin yai nisa a harkar waƙa, domin kuwa har ya fara waka yana koyar karatu a wajena.

3. Ban san abin da ya fara haɗa Hamisu da Rakiya ba, amma na tabbatar cewa Rakiya ta yiwa ko kuma tana yi wa Hamisu so maras misaltawa, domin kuwa ta kan zo ta wuni a gidansu tare da mahaifiyar sa, su yi hira, ta taya ta aiki, kuma ta raka ƙanwarsa Khadija duk inda aka aketa (kanti, siyo kayan miya da sauransu), duk da kasancewar matsayinta na tauraruwar fim (ko nace celebrity).

4. Ba sau ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba, duk lokacin da na shiga gidan su Hamisu na sameta (Rakiya) ko s**a fito da Khadija ko da shi Hamisu, in har Hamisu zai gaisheni to sai ta rusuna take gaishe ni. Saboda duk wanda ta fahimci yana da wata ƙima ko influence akan Hamisu tana girmama shi.

5. Ba ni kaɗai ba, duk waɗanda suke rukunin gidanjenmu sun saba da ganinta domin a wancan lokacin ɗaiɗai ne ranekun da bata gidan su Breaker (ko da baya gari).

6. Tambayar a nan shi ne, shin Hamisu Breaker ya taɓa soyayya da Rakiya?

7. Ba zan iya amsa tambayar kai tsaye ba, amma tun a wancen lokacin, abin da mafi yawan mu muka fahimta shi ne Rakiya ke neman soyayyar Hamisu Breaker. Kuma ina da dalili.

8. Na taɓa tattaunawa da shi a kan alaƙarsa da Rakiya, musamman akan zuwan da ke gidansu na rashin dacewar hakan. A lokacin ya bani amsar cewa tana sonsa ne, shi kuma gaskiya bai aminta ba. Ta kan zo gidan har ta tafi basu haɗu ba, domin ita tana zuwa wajen mahaifiyarsa ne da niyyar kamun ƙafa. Don haka ba yadda zai iya hana ta zuwa, saboda ya faɗa mata bata ji ba. Mun yi makamanciyar wannan maganar da mahaifiyar Hamisu watarana, kuma amsar da na samu bata ci karo da abin da Hamisu ya faɗa min ba.

9. Kamar yadda na ji (daga wasu abokansa) cewar akwai waƙoƙin da s**ai tare da Hamisu wanda ita ta ɗau nauyin su, ta biya shi, ta kuma roƙe shi su yi video ɗin waƙar tare.

10. A lokacin da duk waɗannan abubuwan suke faruwa, Hamisu bai yi shura an san shi a ko ina kamar yanzu ba. Don haka in dai ya tabbata shi ne wanda Rakiya ta ba da labari, to tabbas ba ɗaukaka ce ta raba su ba, tun farko ta gino soyayyar ta ne da tubalin toka, ko kuma son maso wani.

11. Na iya tunawa a cikin hirarta akwai inda tace "Ya yi min duk wani abu da ya kamata na rabu da shi, na ma manta da shi a rayuwa ta, amma ban rabu da shi ba". Idan har ya tabbata Breaker ne take nufi, to tabbas ni kai na naga dagiyar ta a irin yadda tun yana kulata, har ya zama yana sha mata ƙanshi, da mu'amalar da za ta rabu da shi ɗin amma bata dena ba.

12. A taƙaice, ba ina ganin laifin Rakiya ba ne, domin sha'anin so ya fi ga haka. Haka kuma ba ina kare Hamisu ba ne, amma ni ganau ne cewa tun ba a san Hamisu Breaker sosai ba, ya nuna rashin karɓar soyayyar Rakiya, don haka rabuwar su ba ta da alaƙa da matsayin da ya samu a rayuwa.

Ina ƙara tausaya mata matuƙar gaske, ina kuma yi wa dukkan masoya fatan Allah ya haɗa su da masoyansu na gaskiya.

ADDU'AR YAYE DAMUWA.Annabi SAW Ne Ya koyardamu Addu'ar.Ana Karanta ta ne a koda yaushe, tareda Niyya me kyau.Annabi SAW ...
22/10/2022

ADDU'AR YAYE DAMUWA.

Annabi SAW Ne Ya koyardamu Addu'ar.

Ana Karanta ta ne a koda yaushe, tareda Niyya me kyau.

Annabi SAW yace dukkan wata damuwar ka da Quncin Rayuwa, inde Babu zaluntar wani ko wata aciki, to haqiqa Allah ze amsamaka.

ga Yacce ADDU'AR take:-
LA'ILAHA ILLALLAH UL AZEMUL HALIMU.
LA'ILAHA ILLALLAH RABBUL ARSHIL AZEEM.
LA'ILAHA ILLALLAH U RABBUSSAMAWATI WA RABBUL ARDI, RABBUL ARSHIL KAREEM.

لا اله الا الله العظيم الحليم
لا اله الا الله رب العرش العظيم
لا اله الا الله رب السماوات و رب الأرض رب العرش الكريم
MA'ANA:
Babu wani abun bauta da gaskiya sai Allah, ya Allah Kai me Girma ne, me hakuri(da bayi, Kuma ka hureta ga bayi)

Babu abun bauta da gaskiya sai Allah, ya Allah Ubangijin Al-arshi me Girma.

Babu abun bauta da gaskiya sai Allah, ya Allah Ubangijin sammai da Qassai, Kuma kaine Ubangijin Al-arshin Nan me Girma, (Allah) Kai me Karamcine.

SHARHI ATAIQAICE.
Dukkan wadannan kalmomin da suke Addu'ar yabo ne da Girmama Allah Ubangijin Halittun sama da Qasa, da Kuma miqa wuya ga Allah tareda sallamawa ga hukuncin shi.

Kuma kalmomi ne na rokon Allah da kamun Qafa a gareshi a domin ya yayewa bawa damuwa ko bakin ciki ko Bala ai, da Kuncin Rayuwa.
WALLAHU A'ALAM

Ya Allah ka yaye mana namu, ka tausayamana duniya da lahira, .

+2348168311092
Tambayoyi akan darasi

...Zaton Alkhairi, Jarumta Ne. Kamar Yadda Munana Zato Yake Zama Ragontaka.Domin Sau Da Yawa a Wurin Da Jarumi Yake Tsam...
22/10/2022

...Zaton Alkhairi, Jarumta Ne. Kamar Yadda Munana Zato Yake Zama Ragontaka.

Domin Sau Da Yawa a Wurin Da Jarumi Yake Tsammanin Faruwar Abu Mai Kyau Da Zai Taimaki Ci Gaban Rayuwarsa.

Rago Kuma Cika Yake Da Tsoron Faruwar Mummuna Wanda Zai Tsinke Zaren Tasa Rayuwar.

Shi Ya Sa Sarkin Rome Julius Yake Cewa;

"Matsoraci Yana Mutuwa Sau Dubu Kafin Lokacin Mutuwarsa, Amma Jarumi Ba Ya 'Dandanar 'Dacin Mutuwa Sai Sau 'Daya."

Ka Tabbata Akan Kyakkyawan Zato a Cikin Duk Harkokin Da Ka Tsoma 'Kafafunka.

Domin Idan Halinka Ya Kasance Kyautata Zato, To Tamkar Kana Yi Wa Kanka Bishara Ne Cewa 'Karshen Rayuwarka Zai Zama Kyakkyawa.

ALLAH Ya Cika Rayuwarmu Da Kyakkyawan Zato, Don Albarkar SHUGABA(S.A.W)🙏💔🙏🙏

YANZU-YANZU: Hukumar Kula Da Kafafen Watsa Labarai Ta Ƙasa NBC Ta Haramtawa Dukkan Gidajen Rediyo Sanya Waƙar Ado Gwanja...
07/09/2022

YANZU-YANZU: Hukumar Kula Da Kafafen Watsa Labarai Ta Ƙasa NBC Ta Haramtawa Dukkan Gidajen Rediyo Sanya Waƙar Ado Gwanja Ta Warr.

Me za ku ce?

31/08/2022
31/08/2022
30/08/2022

A hirar shi da muryar amurka, magajin gidan da abin ya faru, mallam umaru kauran yabo ya bayyana cewa, da dare maidakin ta yi wani dambu na masara da kowa ya ci duk da wandanda ba gidan su ke ba, kuma ba a sami wata matsala ba.

30/08/2022
30/08/2022

Adresse

Ogunia

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque mujallarmanagarciya publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Contacter L'entreprise

Envoyer un message à mujallarmanagarciya:

Partager